settings icon
share icon
Tambaya

Wane ne Ruhu Mai Tsarki?

Amsa


Akwai tunani iri iri kan shaidar Ruhu Mai Tsarki. Waɗansu na kallon Ruhu Mai Tsarki kamar ikon asiri ne. Wadansu sun gane da Ruhu mai Tsarki kamar ikon sojan gona wanda Allah ya bai wa mabiyin Kiristi. Mene ne littafiMai Tsarki ta ce game da shaidar Ruhu Mai Tsarki? A sauƙaƙe a ce Littafi Mai Tsarki na faɗi cewa Ruhu Mai Tsarki Allah ne. Littafi Mai Tsarki kuma tana faɗi cewa Ruhu Mai Tsarki mutum ne, taliki mai tunani, motsin rai, da son rai.

Tabbataccen magana cewa Ruhu mai Tsarki Allah ne ana ganin haka a fili cikin nassoshi da dama haɗe da Ayyukan Manzanni 5:3-4. A cikin wannan aya Bitrus yayi taho-mu-gama da Hananiya akan me yasa yayi wa Ruhu mai Tsarki ƙaryakuma ya gaya masa cewa “ba mutum kayi wa karya ba, Allah kayi wa.” Wannan furci ne sarai cewa karya ga Ruhu Mai Tsarki ya zama karya ne ga Allah, zamu iya kuma sani cewa Ruhu Mai Tsarki Allah ne saboda ya mallaki halayen Allah. Alal misali, tabbataccen magana cewa Ruhu Mai Tsarki yana koina ana gani cikin Zabura 139:7-8 “ Ina zan tafi in tsere wa Ruhun ka? Ina zan gudu in tsere maka? Idan na hau cikin samaniya kana can. Ina kwanta a lahira kana can.” Sa’anan cikin 1 Korantiyawa 2:10 muna ganin hali na sanin kome da kome a cikin Ruhu Mai Tsarki. “ Mune Allah ya bayyana wa, ta Ruhu, domin Ruhu shi yake fayyace kome, har ma zurfafan al’amuran Allah. Wane ne a cikin mutane ya san tunanin wani mutum, in ba ruhun shi mutumin ba? Haka kuma ba wanda ya san tunanin Allah, sai dai Ruhun Allah.”

Zamu iya san cewa Ruhu mai Tsarki da gaske mutum ne saboda ya mallaki tunani, motsin rai da kuma son rai. Ruhu Mai Tsarki yana tunani da kuma sani (1 Korantiyawa 2:10). Ruhu mai Tsarki yakan iya ɓacin rai (Afisawa 4:30). Ruhu yakan yi roƙo domin mu (Romawa 8:26-27). Ruhu Mai Tsarki yakan yanke shawara bis ga nufin sa (1 Korantiyawa 12:7-11). Ruhu Mai Tsarki Allah ne, “Mutum” na uku na Triniti. Kamar Allah, Ruhu Mai yakan iya aiki da gaske a matsayin mai Ta’azziya da Mashawarci da Yesu ya alƙawarta zai zama (Yahaya 14:16,26; 15:26).

English



Koma zuwa shafin gida na Hausa

Wane ne Ruhu Mai Tsarki?
© Copyright Got Questions Ministries