settings icon
share icon
Tambaya

Ta yaya zan sami tabbacin cetona?

Amsa


Yawancin masu bin Yesu Kiristi suna neman tabbacin ceto a wuraren da ba daidai ba. Muna neman neman Ceto a cikin abubuwan da Allah yake yi a rayuwarmu, a cikin haɓakarmu ta ruhaniya, cikin kyawawan ayyuka da biyayya ga Maganar Allah da ke bayyane a cikin tafiyarmu ta Kirista. Duk da yake waɗannan abubuwan na iya zama shaidar ceto, amma ba su bane abinda yakamata mu kafa tushen ceton mu ba. Maimakon haka ya kamata mu sami tabbacin ceton mu a cikin gaskiyar Kalmar Allah. Ya kamata mu kasance da tabbaci cewa za mu sami ceto bisa ga alkawuran da Allah ya bayyana, ba don ƙwarewarmu ba.

Ta yaya zaka sami tabbacin ceto? Yi la'akari da 1 Yahaya 5:11-13: “Wannan kuma ita ce shaidar, cewa Allah yā ba mu rai madawwami, wannan rai kuwa yana cikin Ɗansa. Duk wanda yake da Ɗan, yana da rai. Wanda ba shi da Ɗan Allah kuwa, ba shi da rai. Na rubuto muku wannan ne, ku da kuka gaskata da sunan Ɗan Allah, domin ku tabbata kuna da rai madawwami.” Wanene yake da dan? Waɗannan ne waɗanda suka ba da gaskiya gare shi (Yahaya 1:12). Idan kana da Yesu, kana da rai. Ba rayuwar ɗan lokaci ba, amma har abada. Wanene yake da dan? Waɗannan ne waɗanda suka ba da gaskiya gare shi (Yahaya 1:12). Idan kana da Yesu, kana da rai. Ba rayuwar ɗan lokaci ba, amma har abada.

Allah yana so mu sami tabbacin ceto. Kada muyi rayuwar kiristanci muyi al'ajabi da damuwa kowace rana shin muna da ceto da gaske ko a'a. Wannan shine dalilin da yasa littafi mai tsarki ya bayyana shirin ceto sarai. Yi imani da Yesu Kiristi (Yahaya 3:16; Ayukan Manzanni 16:31). “Wato, in kai da bakinka ka bayyana yarda, cewa ‘Yesu Ubangiji ne,’ ka kuma gaskata a zuciyarka Allah ya tashe shi daga matattu, za ka sami ceto.” (Romawa 10:9). Shin kun tuba daga zunubanku? Shin kun gaskanta cewa Yesu ya mutu ne domin ya biya bashin zunubanku kuma ya tashi daga matattu (Romawa 5:8; 2 Korantiyawa 5:21)? Shin ka yarda dashi shi kadai domin ceto? Idan amsarka ga waɗannan tambayoyin ita ce "eh," ka sami ceto! Tabbatarwa yana nufin yanci daga shakka. Ta wurin ɗaukan Maganar Allah a zuciya, ba za ka sami shakka game da gaskiyar cetonka na har abada ba.

Yesu da kansa ya tabbatar wa waɗanda suka ba da gaskiya gare shi: “Ina ba su rai madawwami, ba kuwa za su halaka ba har abada, ba kuma mai ƙwace su daga hannuna. Ubana, wanda ya ba ni su, ya fi duka girma, ba kuwa mai iya ƙwace su daga ikon Uban” (Yahaya 10:28-29). Rai madawwami ne kawai- har abada. Babu wani, har da kai kanka, da za su iya kwace kyautar ceton da Allah ya ba ka daga gare ka.

Yi farin ciki da abin da Kalmar Allah ke faɗa maka: maimakon yin shakka, za mu iya rayuwa da gaba gaɗi! Zamu iya samun tabbaci daga Kalmar Kristi cewa ceton mu ba zai kasance cikin tambaya ba. Tabbacinmu na ceto ya dogara da cikakke kuma cikakkiyar ceton da Allah ya tanadar mana ta wurin Yesu Kiristi.

EnglishKoma zuwa shafin gida na Hausa

Ta yaya zan sami tabbacin cetona?
© Copyright Got Questions Ministries