settings icon
share icon
Tambaya

Ko akwai Allah? Akwai wata shaida na kasancewar Allah?

Amsa


Akwai Allah? Na same shi da sha’awa cewa an bada kulawa mai yawa ga wannan cacar baki. Neman ra’ayi na kwana nan na faɗi cewa fiye da da kashi 90% bisa ɗari na mutane cikin duniya yau sun gaskata akwai Allah ko waɗansu iko mai tsauri. Duk da haka, ko ta yaya an aza alhakin kan waɗancan da sun gaskata akwai Allah da ko yaya su tabbatar cewa Shi da gaske yana nan. Gare ni, ina tunani da ya zama ta wata hanya dabam.

Duk da haka, ba za a iya tabbatar ko rashin tabbatar da kasancewar Allah ba. Littafi Mai Tsarki kuwa tana faɗi cewa dole ne mu amsa ta bangaskiya gaskiyar cewa akwai Allah, “ In ba game da bangaskiya ba kuwa, bashi yiwuwa a faranta masa rai. Domin duk wanda zai kusaci Allah, lalle ya gaskata, akwai shi, yana kuma sakamako ga masu neman sa.” (Ibraniyawa 11:6). Idan Allah na sha’awar haka, zai iya a sauƙaƙe ya bayyana kuma tabbatar wa dukan duniya cewa shi yana nan. Amma idan yayi haka ɗin, ba za a sami bukata na bangaskiya ba. “ Sai bangaskiya ba. “ Sai Yesu ya ce, ‘wato saboda ka gan ni ka bada gaskiya? Albarka ta tabbata ga waɗanda basu gani ba, amma kuma suka bada gaskiya “ (Yahaya 20:29).

Wannan bata nufin, ko da yake, cewa babu tabbacin kasancewar Allah ba. Littafi Mai Tsarki ta furta, “ Dubi yadda sararin sama ka bayyana ɗaukakar Allah! Dubi yadda suke bayyana a fili ayyukan sa da yayi! Kowace rana tana shelar daukakar sa ga ranar da ke biye. Kowane dare yana nanata ɗaukakar sa ga daren da ke biye. Ba magana ko kalma da aka hurta. Ba wani amon da aka ji. Duk da haka muryar su ta game duniya duka, saƙon su ya kai koina a duniya. Allah ya kafa wa rana alfarwa a sararin sama” (Zabura 19:1-4). Duban taurarin sama, fahintar doron duniya da ikokin sama, duban al’ajaban halitta, ganin kyan faɗuwar rana- duk waɗannan suna nuna ga Allah mahalicci. Idan da waɗannan basu isa ba, akwai kuma tabbacin Allah a cikin zukatan mu. Mai Hadishi 3:11 tana gaya mana, “--- Shine kuma yasa mana buri mu san abin da ke nan gaba, ...” Akwai wata abu zurfafa can can cikin halittar mu mai yarda cewa akwai wani abu bayan wannan rai, da kuma wani bayan wannan duniya. Zamu iya musunci wannan sani a fahince, amma kasancewar Allah a cikin mu kuma ta wurin mu har yanzu tana nan. Duk da wannan dai, Littafi Mai Tsarki tana gargaɗe mu cewa waɗansu har ila yau zasu yi musun sanin Allah, “ Wawaye sukan ce ma kan su, ‘Ba Allah’ “ (Zabura 14:1). Tun da fiye da kashi 98% bisa ɗari na mutane duk tarihi, cikin duk al’adu, cikin duk wayewar kai, a manyan ɓangarori na duniya, sun gaskata da kasancewar wani irin Allah- dole akwai wani abu (ko wani) mai sanadin wannan bangaskiya.

Bugu da ƙari akan gardamar Littafi Mai Tsarki na kasancewar Allah, akwai jayayya ta azanci. Farko, akwai gardamar yanayin kasancewa. Siffa mafi farin jini na gardamar yanayin kasancewa daga asali tana amfani da tunani game da Allah don tabbatar da kasancewar Allah. Tana farawa da ma’anar Allah kamar “Wannan da babu abu mafi gaggrumar da za a yi tunani.” Sa’anan nan ne za a yi jayayya cewa a kasance yafi rashin kasancewa, don haka ne babban abin tunani ya kasance. Idan babu Allah ba sa’anan ba Allah ne mafi abin tunawa ba – amma wannan zai yi gwagwarmaya da ma’anar Allah ainun.

Na biyu shine gardamar mai zane. Gardamar mai zane shine cewa tun da duk sama da kasa suna nuna tsari mai burgewa haka, dole ne akwai wani Allah mai tsarin. Alal misali, in da a ce duniya ma tana ƴan ɗarurrukan miloli kurkusa da rana ko yi gaba can daga rana, da ba zata iya tallafi yawan rai da take yi a yanzu. Idan da abubuwa cikin yanayin duniyar mu suna kuwa ƴan munzali bisa ɗari dabam, kowace rayayyen taliki a duniya zai mutu. ƴar abinci mai gina jiki marar ɗan’uwa guda mai siffantuwa ta ‘ƙaddara yana 1 cikin 10243 (wato 10 na biye da wajen 243 O’s). Ɗan tayin rai guda na ƙunshe da miliyoyi gutsattsarin abinci mai gina jiki.

Gardama ta uku ta azanci domin kasancewar Allah ana kiran ta gardamar tsarin duniya. Kowace abin da ya biyo baya akwai sanadi. Sama duk da duniya da kome ne dake cikin ta ya zama abin da ya biyo baya ne. Dole akwai wani abin da ya zama sanadin kome kuma da kasance. Wancan abu “marar- sanadi” shine Allah. Gardama ta huɗu an san ta da gardamar halin kirki. Kowace al’ada a dukkanin tarihi tana da waɗansu siffar doka. Kowane mutum na da azancin abin da ke daidai da abin da ba daidai ba. Kisankai, karya, sata da kuma haram suna abin ki kusan dukan duniya. Daga ina ne wannan azancin abin da ke daidai da abin da ba daidai ba ta taho idan ba daga wurin Allah mai tsarki ba?

Duk da wannan dai, Littafi Mai Tsarki tana gaya mana cewa mutane zasu ƙi sanin Allah na sarari da rashin shakku kuma a maimako su gaskata ƙarya. Romawa 1:25 tana furta, “ Saboda sun sauya gaskiyar Allah da ƙarya, har sun yi wa halitta ibada, sun kuma bauta mata, sun ƙi yi wa mahalicci, shi wanda yabo ya tabbata a gare shi har abada. Amin.” Littafi Mai Tsarki kuma tana shela cewa mutane basu da hujja na rashin gaskatwa da Allah, “ Gama tun daga halittar duniya al’amuran Allah mara sa ganuwa, wato ikonsa madawwami, da allahntakar sa, sun fahintu sarai, ta hanyar abubuwan da aka halitta kuma ake gane su. Saboda haka mutane sun rasa hanzari” ( Romawa 1:20).

Mutane suna da’awa da rashin gaskatawa da Allah ba ta “kimiyya ba ce” ko “ domin babu tabbatarwa.” Dalilin gaskiya ita ce da mutane sun yarda cewa akwai Allah, dole ne kuma su farga cewa suna da alhaki ga Allah kuma na cikin bukatar gafartawa daga wurin Allah (Romawa 3:23; 6:23). Idan akwai Allah, sa’anan muna da alhaki gare shi na ayyukan mu. Idan babu Allah sa’anan zamu iya yin kome da muke so ba tare da samun damuwa game da ko Allah zai yi mana shari’a ba. Na bada gaskiya shine abin da yasa da yawa cikin jama’ar mu sun makale wa koyarwa cewa mutum daga gwaggon biri ne – a bai wa mutane wata wucin gadi na gaskata cikin wani Allah mahalicci. Akwai Allah kuma a ƙarshe kowa ya sani cewa Shi kuma yana nan. Haƙiƙanin dalilin da waɗansu suna ƙoƙarta faɗance su tabbatar da kasancewar sa ita ce da gaske gardama don kasancewar sa.

Ka yardar mani da ɗayan ƙarshen gardama don kasancewar Allah. Yaya na san akwai Alah ? Na san akwai don na kan yi zance da shi kowace yini. Bana jin muryar sa tana maido mani da zance ba, amma na kan ji da hallarar sa, Na kan ji da bishewar sa, Na kan ji da ƙaunar sa, Ina sha’awar alherin sa. Abubuwa sun faru a rayuwata waɗanda ba su da bayyanin yiwuwa dabam ban da Allah. Allah cikin al’ajabi ya cece ni kuma ya canza rayuwata da ba zan iya taimakawa ba amma dai in yarda kuma in yabe kasancewar sa. Babu wata daga waɗannan gardandami ciki ko kuma ta kan su da kan iya rinjaye wani wanda ya ƙi yarda da abin da yana a bayyane sarai. A ƙarshe, kasancewar Allah dole ne a karɓe shi ta bangaskiya (Ibraniiyawa 11:6). Bangaskiya ga Allah ba wai ayi tsalle da ido a rufe cikin duhu bane, ta zama mataki marar haɗari zuwa cikin ɗaki mai cikakken haske inda kashi 90% bisa ɗari na mutane sun riga sun tsaitsaya.

EnglishKoma zuwa shafin gida na Hausa

Ko akwai Allah? Akwai wata shaida na kasancewar Allah?
© Copyright Got Questions Ministries