settings icon
share icon
Tambaya

Shin ya kamata Kiristoci su je wurin likitoci?

Amsa


Akwai wasu Kiristoci da suka gaskata cewa neman likita yana nuna rashin imani da Allah. A cikin maganar Kalmar-Imani, tuntubar likita galibi ana daukar shi rashin imani wanda zai hana Allah ya warkar da kai. A cikin ƙungiyoyi irin su Kimiyyar Kirista, neman taimakon likitoci wani lokaci ana ɗaukar su a matsayin wani shinge ga amfani da kuzarin ruhaniya da Allah ya bamu don warkar da kanmu. Hankalin waɗannan ra'ayoyin rashi ƙaranci. Idan motarka ta lalace, shin za ka kai ta wurin kanikanci ko jira Allah ya yi mu'ujiza ya warkar da motarka? Idan aikin famfo a cikin gidanka ya fashe, shin kana jiran Allah ya toshe wannan malalar ne, ko kuwa ka kira mai aikin famfo? Allah yana da ikon gyara mota ko gyara bututun ruwa kamar yadda yake da ikon warkar da jikinmu. Gaskiyar cewa Allah yana iya kuma aikata al'ajibai na warkarwa baya nufin koyaushe muyi tsammanin mu'ujiza maimakon neman taimakon mutane waɗanda suka mallaki ilimi da fasaha don taimaka mana.

An ambaci likitoci kusan sau goma a cikin Littafi Mai-Tsarki. Aya kawai da za'a cire daga mahallin don koyar da cewa kada mutum ya je wurin likitoci zai zama 2 Tarihi 16:12. "A shekara ta talatin da tara ta mulkin Asa, sai wani ciwo ya kama shi a ƙafa. Ciwon kuwa ya tsananta ƙwarai, duk da haka Asa bai nemi taimakon Ubangiji ba, sai na magori." Maganar ba wai Asa ya nemi likitoci ba, amma cewa "Asa bai nemi taimakon Ubangiji ba." Ko da lokacin ziyartar likita, babban imaninmu shine ya kasance cikin Allah, ba likita ba.

Akwai ayoyi da yawa waɗanda suke magana game da amfani da "jiyya" kamar sanya bandeji (Ishaya 1:6), mai (Yaƙubu 5:14), mai da ruwan inabi (Luka 10:34), ganye (Ezekiyel 47:12), ruwan inabi (1 Timothawus 5:23), da salves, musamman ma "balm na Gileyad" (Irmiya 8:22). Hakanan, Luka, marubucin Ayyukan Manzanni da Linjilar Luka, Bulus ya kira shi “ƙaunataccen likita” (Kolosiyawa 4:14).

Markus 5:25-30 ya ba da labarin wata mata da ke fama da cutar zubar jini, matsalar da likitoci ba za su iya warkar ba duk da cewa ta kasance ga yawancinsu kuma ta kashe kuɗinta duka. Da ta zo wurin Yesu, sai ta yi tunani cewa idan ta taɓa gefen rigarsa, za ta warke; ta taba Hannun sa, ta warke. Yesu, a lokacin da yake amsawa Farisiyawa game da dalilin da yasa yake zama tare da masu zunubi, ya ce masu, "Ai, lafiyayyu ba ruwansu da likita, sai dai marasa lafiya."(Matiyu 9:12). Daga cikin wadannan ayoyin mutum na iya tantance wadannan ka'idodi:

1) Likitocin ba Allah bane kuma bai kamata a kallesu haka ba. Suna iya taimaka wasu lokuta, amma akwai wasu lokuta lokacin da duk abin da zasu cim ma shine cire kuɗi.

2) Neman likitoci da amfani da magungunan "duniya" ba'a hukunta su a cikin Nassi ba. A gaskiya ma, ana ba da kulawar likita da kyau.

3) Neman shiga tsakani na Allah cikin kowace matsala ta zahiri ya kamata a nemi (Yakubu 4:2; 5:13). Bai yi alƙawarin cewa zai amsa yadda za mu so koyaushe ba (Ishaya 55:8-9), amma muna da tabbacin cewa duk abin da yake yi za a yi shi cikin ƙauna kuma ta haka ne don kyakkyawan muradinmu (Zabura 145:8-9).

Don haka, ya kamata Kiristoci su je wurin likitoci? Allah ya haliccemu a matsayin mutane masu hankali kuma ya bamu ikon kirkirar magunguna da koyon gyaran jikin mu. Babu wani abu da ba daidai ba tare da amfani da wannan ilimin da iyawar zuwa warkarwa ta jiki. Ana iya kallon likitoci a matsayin baiwar da Allah yayi mana, hanya ce da Allah ke kawo waraka da warkewa. A lokaci guda, babban imaninmu da dogaronmu shine su kasance ga Allah, ba cikin likitoci ko magunguna ba. Kamar yadda yake tare da duk shawarwari masu wahala, ya kamata mu nemi Allah wanda yayi mana alƙawarin ba mu hikima yayin da muka roƙe ta (Yakubu 1: 5).

English



Koma zuwa shafin gida na Hausa

Shin ya kamata Kiristoci su je wurin likitoci?
© Copyright Got Questions Ministries