settings icon
share icon
Tambaya

Mene ne Littafi Mai Tsarki ke faɗi game da mutuwar aure da sake yin aure?

Amsa


Farko da kome, ko mece ce dai ra’ayin da wani kan riƙe cikin batun kisan aure tana da muhimmanci a tuna da kalmomin Littafi Mai Tsarki daga Malaki 2:16a: “Allah na Isra’ila, na ce ina ƙin kisan aure.” Bisa ga Littafi Mai Tsarki, shirin Allah shine cewa aure ya zama alƙawari na rai “Har nan gaba su zama ba jiki biyu ba ne, daya ne. Abin da Allah fa ya gama, kada mutum ya raba” (Matiyu 19:6). Allah ya farga, ko da yake, cewa tun da aure ya ƙunshi mutum biyu masu zunubi, kisan aure zata auku. A cikin Tsohon Alƙawari, ya zayyana waɗansu dokoki garin a kiyaye hakkokin zawarawa, musamman mataye (Maimaitawar Shari’a 24:1-4). Yesu yayi zance cewa waɗannan dokoki an bayar da su saboda taurin zuciya na mutane ne, ba don sun zama sha’awar Allah ba (Matiyu 19:8).

Gardama ko an yarda a kashe aure da sake yin aure bisa ga Littafi Mai Tsarki tana kewaye ne da farko kan kalmomin Yesu cikin Matiyu 5:32 da 19:9. Shadarar “in ba a kan laifin zina ba” ita ce kaɗai abu cikin littafi cewa da yiwuwa Allah ya bayar da yarda don kisan aure da sake yin aure. Yawancin masu fassara sun gane da wannan “ɓangaren jimla ta banda” kamar na zancen “rashin aminci na aure” a lokacin ‘alƙawari.” A cikin al’adar Yahudawa, namiji da tamace an ɗauke su ma’aurata ne ko ma tun lokacin da suna cikin “alƙawari.” Fasiƙanci a wannan lokacin “alƙawari” ita ce kaɗai dalili mai inganci domin a kashe aure.

Duk da haka, kalmar yaren Hellenawa da aka juya “rashin aminci na aure” ta zama kalma wanda ma’anarta kan iya zama da kowanne siffa na zunubin fasiƙanci. Zata iya nuna lalata, karuwanci, yin zina,da sauransu. Yesu mai yiwuwa na faɗin cewa an yarda da kisan aure idan anyi fasiƙanci. Jima’i ta zama wata ɓangaren ciki na haɗin aure “Haka su biyun nan zasu zama jiki guda” (Farawa 2:24; Matiyu 19:5; Afisawa 5:31). Don haka,a ƙarye wannan haɗin ta yin jima’i a wajen aure zai iya zama yardajjen dalili na kisan aure. Idan haka ne, Yesu yana da batun sake yin aure cikin tunani a wannan wurin. Jimlar “ya kuma auri wata” (Matiyu 19:9) na nuna cewa kisan aure da sake yin aure an yarda da su a yanayin ɓangaren jimla ta in banda, komece ce ta zama fassarar da take.

Yana da muhimmanci a lura cewa sai ɓangare marar laifi kaɗai ne aka yarda su sake yin aure. Ko da yake ba a rubuta cikin nassin ba, yarda a sake yin aure bayan kisan aure ya zama rahama ga wanda aka yi wa zunubin, ba ga wanda yayi zunubin fasiƙanci ba. Za a sami wasu yanayin inda “ɓangaren mai laifi” an yarda su sake yin aure – amma babu tunanin nan da aka koyar cikin wannan nassin.

Waɗansu sun fahinci 1Korantiyawa 7:15 kamar wata “in banda “ mai yarda da sake yin aure idan abokin aure mara bada gaskiya ya saki mai bada gaskiya. Duk da haka, wurin bata ambaci sake yin aure ba, amma kaɗai ta ce mai bada gaskiya baya a ɗaure ya ci gaba da auren idan abokin aure marar bada gsakiya yana son rabuwa. Wasu na da’awa cewa cin mutuncin (abokin aure ko yaro) sun zama dalilai masu ƙarfi don kashe aure ko da ma ba a tsara su hakanan cikin Littafi Mai Tsarki ba. Yayin da wannan zai iya zama haka ɗin ainun, bai taɓa zama da hikima a ɗauka haka kan maganar Allah ba.

Wasu lokatai ɓacewa cikin gardama kan jimlar in banda ta zama gaskiya cewa komene ne ma’anar “rashin aminci cikin aure” ya zama yardajje don kisan aure, ba bukata don kisan aure ba. Ko da yake anyi fasiƙanci ma’aurata zasu iya, ta rahamar Allah, koyi yin gafara kuma su fara sake gina aurensu. Allah ya riga ya gafarta mana fiye da haka. Tabbatacce zamu iya bin gurbinsa kuma har da gafarta zunubin zina (Afisawa 4:320. Duk da haka, a wasu misalai, abokin aure kan ƙi tuba da ci gaba cikin fasiƙanci. A wurin ne inda Matiyu 19:9 zata iya da yiwuwa ya shafa. Da yawa kuma kan so tun da wuri su sake yin aure bayan kisan aure sa’anda Allah mai yiwuwa na sha’awa su zama su kaɗai.Wasu lokatai Allah ya kan kira mutum yayi zaman kaɗaici don hankalinsa kar ta rabu (1Korantiyawa 7:32-35). Sake yin aure bayan kisan aure kan zama zaɓi cikin waɗansu halayan zama, amma wannan bai nuna cewa ita ce kaɗai zaɓi ba.

Da nauyaya cewa yawan kisan aure tsakanin masu ce su Kirista kusan ya haura kamar na duniyar marasa bada gaskiya. Littafi Mai Tsarki ta mai da ita fili a yalwace cewa Allah na ƙin kisan aure (Malakai 2:16) da kuma cewa shiryawa da gafartawa sune kamata su zama alamomi na rayuwar masu bada gaskiya (Luka 11:4; Afisawa 4:32). Duk da haka, Allah ya san da cewa kisan aure zai faru, har ma a cikin ƴaƴansa. Mai bada gaskiyar da aurensa ya mutu/ko kuma ya sake yin aure bai kamata yaji kamar Allah ya ragu masa ba, ko ma idan kisan aurensa da/ko sake yin aurensa ba akan dalilin jimlar in banda na Matiyu 19:9 ba. Allah kullum na amfani har ma da Kirista marasa biyayya masu zunubi ya cikasa abu mai girma.

EnglishKoma zuwa shafin gida na Hausa

Mene ne Littafi Mai Tsarki ke faɗi game da mutuwar aure da sake yin aure?
© Copyright Got Questions Ministries