settings icon
share icon
Tambaya

Yaya zan daidaita da Allah?

Amsa


Garin a”daidaita” da Allah, dole ne da farko mu gane da abin da”ba daidai ba.” Amsar ita ce zunubi,”...Ba wanda ke aikata abin da ke daidai. Babu ko ɗaya” (Zabura 14:3). Mun yi tawaye ga umarnan Allah; mun zama” kamar tumakin da suka ɓata.” (Ishaya 53:6).

Mugun labari shine cewa hukuncin zunubi shine mutuwa.” Wanda yayi zunubi shi zai mutu” (Ezekiyel 18:4). Labari mai dadi shine cewa Allah mai ƙauna ya bi mu garin ya kawo mana ceto. Yesu ya furta manufarsa shine”shine neman abin da ya ɓata, ya cece shi kuma” (Luka 19:10), kuma ya faɗi manufarsa ta cika sa’anda ya mutu akan gicciye da kalmomi”an gama!” ( Yahaya 19:30).

Samun daidaitaccen dangataka da Allah yana fara da yarda da zunubanka. Na biye faɗin laifi da tawali’u ga Allah (Ishaya 57:15) kuma da ƙuduri a rabu da zunubi.” Da baki yake shaidawa ya sami ceto” (Romawa 10:10).

Wannan tubar dole ne bangaskiya ta bi bayanta. Takamaimai dai, bangaskiya ga mutuwar Yesu hadaya da kuma tashi daga matattu mai ban mamaki sun isar dashi ya zama mai cetonka.”Wato in kai da bakinka ka bayyana yarda, cewa Yesu Ubangiji ne, ka kuma gaskata a zuciyarka Allah ya tashe shi daga matattu, za ka sami ceto” (Romawa 10:9). Da yawan waɗansu nassoshi suna zancen bangaskiya ta zama abin tilas, kamar su Yahaya 20:27; Ayyukan Manzanni 16:31; Galatiyawa 2:16; 3:11, 26 kuma Afisawa 2:8.

Ayi zaman daidaita da Allah ya zama al’amari ne ka amshi abin da Allah yayi a madadinka. Ya aiko da mai ceto, ya tanadi hadaya domin kau da zunubanka (Yahaya 1:29), kuma ya miƙa maka alƙawari:”Kowa yayi addu’a da sunan Ubangiji zai sami ceto” (Ayyukan Manzanni 2:21).

Kyakkyawar kwatance na tuba da gafartawa shine misalin na ɓataccen ɗa (Luka 15:11-32). ƙaramin ɗan ya lalatar da kyautar babansa cikin zunubi mai kunyatarwa (aya 13). Sa’anda ya yarda da abin da yayi ba daidai ba, ya yanke shawara ya koma gida (aya 18).Ya zaci ba za’a ƙara ɗaukarsa ɗa ba (aya 19), amma yayi kuskure . Baban ya ƙaunace ɗan tawayen da ya komo kamar yadda ya saba (aya 20). Dukka an gafarta, kuma biki ya biyo baya (aya 24).

Allah nagari ne da zai kiyaye alƙawaransa, har ma da alƙawari ya gafarta.”Ubangiji yana kusa da waɗanda suka ƙarai, Yakan ceci waɗanda suka fid da zuciya (Zabura 34:18).

Idan kana son ka karɓi Yesu Kiristi a matsayin mai cetonka, ga samfurin addu’a anan. Ka tuna, faɗar wace nan addu’a ko wata addu’a dabam ba zai cece ka ba. Amincewa ce kaɗai cikin Kiristi wanda zai iya cece ka daga zunubi. Wace nan addu’a, hanya ce mai sauƙi a furta ga Allah bangaskiyarka a cikin Sa kuma ka gode masa don ya tanadar maka da ceto.”Allah, na sani cewa nayi zunubi gareka kuma na cancanci hukunci. Amma Yesu Kiristi ya ɗauki hukuncin da ya cancance ni, don ta wurin bangaskiya a cikinsa in sami gafartawa. Na juyo daga zunubaina kuma na sa amincewa tawa a cikinka don ceto. Na gode maka don alherinka mai ban mamaki da kuma gafara – kyautar rai madawwami! Amin!”

Ko ka yanke shawara domin Kiristi saboda abin da ka karanta anan? Idan haka ne, don Allah danna kan “Na riga na karɓi Kiristi yau” botin na ƙasa.

English



Koma zuwa shafin gida na Hausa

Yaya zan daidaita da Allah?
© Copyright Got Questions Ministries