settings icon
share icon
Tambaya

Fassarar mafarkin kirista? Shin mafarkanmu daga Allah ne?

Amsa


GotQuestions.org ba hidimar fassarar mafarkin kirista bane. Ba mu fassara mafarki. Munyi imanin cewa mafarkin mutum da ma'anar waɗannan mafarkai suna tsakanin mutum da Allah shi kaɗai. A dā, Allah yana magana da mutane wani lokaci a mafarki. Misali su ne Yusufu, ɗan Yakubu (Farawa 37:5-10); Yusufu, mijin Maryamu (Matiyu 2:12-22); Sulemanu (1 Sarakuna 3:5-15); da wasu da yawa (Daniyel 2:1; 7:1; Matiyu 27:19). Akwai kuma wani annabcin annabi Yowel (Yowel 2:28), wanda manzo Bitrus ya nakalto a cikin Ayyukan Manzanni 2:17, wanda ya ambaci Allah ta amfani da mafarkai. Don haka Allah na iya yin magana ta hanyar mafarki, idan ya ga dama.

Koyaya, dole ne mu tuna cewa Littafi Mai-Tsarki cikakke ne, tun da ya bayyana duk abin da muke buƙatar sani daga yanzu har zuwa lahira. Wannan ba ana cewa Allah baya yin mu'ujizai ko ma yayi Magana ta mafarkai a yau ba, amma duk abin da Allah yace, ko ta mafarki, ko hangen nesa, ko kuma "ƙaramar murya," zai yarda da abinda ya rigaya ya bayyana a cikin Kalma. Mafarki ba zai iya ƙwace ikon nassi ba.

Idan kana da mafarki kuma ka ji cewa wataƙila Allah ne ya ba ka, ka yi addu'a sosai ka bincika Maganar Allah kuma ka tabbata cewa mafarkin naka ya yi daidai da Nassi. Idan haka ne, ka yi addua cikin tunani game da abin da Allah yake so ka yi bisa mafarkinka (Yakubu 1:5) A cikin Littafi, duk lokacin da wani ya sami mafarki daga Allah, Allah koyaushe ya bayyana ma'anar mafarkin a bayyane, ko kai tsaye ga mutumin, ta hanyar mala'ika, ko ta hanyar wani manzo (Farawa 40:5-11; Daniyel 2:45; 4:19). Lokacin da Allah yayi mana magana, yana tabbatar da fahimtar sakonsa a fili.

EnglishKoma zuwa shafin gida na Hausa

Fassarar mafarkin kirista? Shin mafarkanmu daga Allah ne?
© Copyright Got Questions Ministries