settings icon
share icon
Tambaya

Ko dabbobin gida/dabbobi zasu je sama? Ko dabbobin gida/dabbobi suna da kurwa?

Amsa


Littafi Mai Tsarki bai bada wata koyarwa takamaimai kan ko dabbobin gida/dabbobi suna da “kurwa” ko kuwa dabbobin gida /dabbobi zasu yi zama cikin sama ba. Duk da haka, zamu iya ɗauki waɗansu ƙa’idojin Littafi Mai Tsarki na dukka da kuma bada haske akan fannin. Littafi Mai Tsarki ta furta cewa duk da mutum (Farawa 2:7) da dabbobi (Farawa 1:30; 6:17; 7:15,22) suna da numfashin rai. Bambanci na farko tsakanin bani adam da dabbobi shine cewa anyi mutum cikin kamanni da surar Allah (Farawa 1:26-27). Ba a yi dabbobi cikin kamanni da surar Allah ba. Halitta cikin kamanni da surar Allah na nufin cewa bani adam sun zama kamar Allah, gwanin ruhaniya, tunani, motsin rai, da son rai- kuma- suna da ɓangaren mai ci gaba da kasance wa bayan mutuwa. Idan dabbobin gida/dabbobi suna da “kurwa” ko ɓangaren da ba a iya gani ba, dole ne hakanan ya zama na dabam da “cancanta” mai gazawa. Wannan bambancin mai yiwuwa na nufin cewa dabbobin gida/dabbobi “kurwarsu” baya ci gaba da rayuwa bayan mutuwa ba.

Wata hakikanin da za a lura cikin wannan tambaya shine cewa Allah ya halicci dabbobi a matsayin bangaren halittarsa cikin Farawa. Allah ya halicce dabbobi kuma ya ce suna da kyau (Farawa 1:25). Don haka, babu wata dalili da zai sa ba za a iya sami dabbobiia sabuwar duniya ba (Wahayin Yahaya 21:1). Za a sami tabbataccen dabbobi a lokacin mulkin shekara dubu (Ishaya 11:6; 65:25). Ba ya yiwuwa a fadi tabbatacce ko wasu na wadannan dabbobi mai yiwuwa su zama dabbobin gida da muke da su lokacin da muke nan a duniya. Mu dai san cewa Allah mai gaskiya ne kuma cewa sa’anda mun kai sama zamu sami kanmu da cikakken yarda da yanke shawara kan batun, komene ne zata iya zama?

EnglishKoma zuwa shafin gida na Hausa

Ko dabbobin gida/dabbobi zasu je sama? Ko dabbobin gida/dabbobi suna da kurwa?
© Copyright Got Questions Ministries