settings icon
share icon
Tambaya

Shin ambaliyar Nuhu ta game duniya ce ko kuwa ta gari?

Amsa


Littattafan littafi mai tsarki game da ambaliyar sun bayyana a sarari cewa ta shafi duniya ne. Farawa 7:11 ta faɗi haka “dukan maɓuɓɓugai na manyan zurfafa suka fashe, tagogin sammai suka buɗe.” Farawa 1:6-7 da 2:6 sun gaya mana cewa yanayin ambaliyar ya banbanta da abinda muke fuskanta a yau. Dangane da waɗannan da wasu kwatancin na Littafi Mai-Tsarki, yana da kyau a yi hasashen cewa a wani lokaci rufin ruwa ya rufe duniya. Wannan shimfidar kan iya zama alfarwa mai tururi, ko kuma ta kasance tana da zobba kamar na zoben kankara na Saturn. Wannan, a haɗe da wani ruɓaɓɓen ruwa a ƙarƙashin ƙasa, wanda aka saki akan ƙasar (Farawa 2:6) zai haifar da ambaliyar duniya.

Ayoyi mafi bayyane wadanda suka nuna girman ambaliyar sune Farawa 7:19-23. Game da ruwaye, “Ruwa kuwa ya bunƙasa ainun a bisa duniya, har ya rufe kawunan dukan duwatsu masu tsayi da yake ƙarƙashin sammai duka. Ruwa ya bunƙasa bisa duwatsu ya yi musu zara da ƙafa ashirin da biyar. Duk taliki wanda yake motsi bisa duniya ya mutu, da tsuntsaye, da dabbobin gida, da na jeji, da dukan masu rarrafe waɗanda suke rarrafe bisa duniya, da kowane mutum, da kowane abin da yake bisa sandararriyar ƙasa wanda yake da numfashin rai cikin kafafen hancinsa ya mutu. Ubangiji ya shafe kowane mai rai wanda yake bisa ƙasa, da mutum, da dabba, da masu rarrafe, da tsuntsayen sararin sama, an shafe su daga duniya. Nuhu kaɗai aka bari, da waɗanda suke tare da shi cikin jirgi.”

A cikin nassi na sama, ba kawai ana samun kalmar "duka" ana amfani da ita akai-akai ba, amma kuma zamu sami "duk manyan duwatsu da ke ƙarƙashin sammai duka an rufe su," "ruwan ya tashi ya rufe duwatsu zuwa zurfin sama da ashirin ƙafa "da" kowane abu mai rai wanda yake motsi a cikin ƙasa ya halaka." Waɗannan kwatancin suna bayyana a sarari cewa ambaliyar ruwa ta mamaye duniya. Har ila yau, idan ambaliyar ta kasance ta gida, me ya sa Allah ya umurci Nuhu ya gina jirgi maimakon ya gaya wa Nuhu ya ƙaura kuma ya sa dabbobin su ƙaura? Kuma me ya sa ya umarci Nuhu ya gina jirgi mai girma wanda zai iya ɗauke da kowane irin dabbobin ƙasa da ake samu a duniya? Idan ambaliyar ba ta duniya ba, da ba za a bukaci jirgi ba.

Peter also describes the universality of the flood in 2 Peter 3:6-7, where he states, “By these waters also the world of that time was deluged and destroyed. By the same word the present heavens and earth are reserved for fire, being kept for the day of judgment and destruction of ungodly men.” In these verses Peter compares the “universal” coming judgment to the flood of Noah's time and states that the world that existed then was flooded with water. Further, many biblical writers accepted the historicity of the worldwide flood (Isaiah 54:9; 1 Peter 3:20; 2 Peter 2:5; Hebrews 11:7). Lastly, the Lord Jesus Christ believed in the universal flood and took it as the type of the coming destruction of the world when He returns (Matthew 24:37-39; Luke 17:26-27). Bitrus ya kuma bayyana yadda ambaliyar ta game duniya baki daya a cikin 2 Bitrus 3:6-7, inda ya ce, “Ta haka ne kuma, duniyar wancan zamani, ruwa ya sha kanta, ta hallaka. Ta maganar Allah ne kuma sama da ƙasa da suke a nan a yanzu, aka tanada su ga wuta, ana ajiye su, har ya zuwa ranar nan da za a yi wa marasa bin Allah shari'a, a hallaka su.” A cikin wadannan ayoyin Bitrus ya Kwatanta hukuncin “duniya” mai zuwa game da rigyawar zamanin Nuhu kuma ya faɗi cewa duniyar da ta wanzu a lokacin tana cike da ruwa. Bugu da ari, marubutan Littafi Mai-Tsarki da yawa sun yarda da tarihin ambaliyar duniya (Ishaya 54:9; 1 Bitrus 3:20; 2 Bitrus 2:5; Ibraniyawa 11:7). A ƙarshe, Ubangiji Yesu Kristi yayi imani da ambaliyar duniya kuma ya ɗauke ta a matsayin nau'in halakar da ke zuwa ta duniya lokacin da zai dawo (Matiyu 24:37-39; Luka 17:26-27).

Akwai hujjoji da yawa wadanda ba na Littafi Mai Tsarki ba wadanda suke nuni ga masifar duniya kamar ambaliyar duniya. Waɗannan manyan kaburburan da aka samo a kowace nahiya da ɗimbin tarin gawayi waɗanda zasu buƙaci rufewar ciyayi da yawa da sauri. Ana samun burbushin halittu a saman duwatsu a duniya. Al'adu a duk ɓangarorin duniya suna da wani nau'i na labarin tatsuniya. Duk waɗannan gaskiyar da wasu da yawa shaidu ne na ambaliyar duniya.

EnglishKoma zuwa shafin gida na Hausa

Shin ambaliyar Nuhu ta game duniya ce ko kuwa ta gari?
© Copyright Got Questions Ministries