settings icon
share icon
Tambaya

Ina ne Yesu yake na kwana uku tsakanin mutuwarsa da tashinsa daga matattu?

Amsa


1Bitrus 3:18-19 tana cewa, “Domin Almasihu ma ya mutu sau ɗaya tak ba ƙari, domin kawar da zunubanmu, mai adalci saboda marasa adalci, domin ya kai mu ga Allah. An kashe shi a jiki, amma an rayar da shi a ruhu. Da ruhun ne kuma yaje yayi wa ruhohin da ke kurkuku shela.”

Jimlar, “a ruhu” cikin aya 18 tana daidai da gini kamar jimlar “cikin jiki.” Haka ya zamanto mafi kyau a danganta kalmar “ruhu’ da wuri daidai kamar kalmar “jiki.” Jiki da ruhu sun zama jiki da ruhun Kiristi ne. Kalmomin nan “an rayar da shi a (ciki) ruhu,” na nuna gaskiyar cewa Kiristi mai ɗauke da zunubi da mutuwa ta kawo rabuwar ruhunsa na mutuntaka daga Uban (Matiyu 27:46). Bambancin yana tsakanin jiki da ruhu, kamar cikin Matiyu 27:46 da Romawa 1:3-4, da kuma na tsakanin jikin Kiristi da Ruhu Mai Tsarki. Lokacin da kafarar Yesu don zunubi ta cika, ruhunsa ya sake soma zumunci wanda dă ma an ƙarye.

Bitrus na farko 3:18-22 ta bayyana haɗi ta lalle tsakanin wahalar Kiristi (aya 18) da kuma ɗaukakarsa (aya 22). Bitrus ne kaɗai ya bada labari takamaimai game da abin da ya faru tsakanin waɗannan abubuwa biyu. Kalmar ‘wa’azi” cikin aya 19 bai zama kalmar da aka saba cikin Sabon Alƙawari na bayyana wa’azin bishara ba. Tana nuna a a zahiri shelar sako. Yesu ya sha wahala kuma ya mutu kan gicciye, an kashe jikinsa, kuma ruhunsa ya mutu sa’anda aka mai da shi zunubi. Amma an mai da ruhunsa rayayye kuma ya bada ita ga Uban. Bisa ga Bitrus, a wani lokaci tsakanin mutuwarsa da tashin sa daga matattu Yesu yayi shela ta musamman ga “ruhohin dake kurkuku.”

Da farko dai, Bitrus ya bayyana mutane kamar “ruhohi” kuma ba “iskoki” ba (3:20). Cikin Sabon Alƙawari, kalmar “iskoki” an more ta da bayyana mala’iku ko aljannu, ba ƴan adam ba; kuma aya 22 yayi kamar tana bada shaida ga wannan ma’anar. Kuma, babu inda cikin Littafi Mai Tsarki da an gaya mana cewa Yesu ya ziyarci jahannama. Ayyukan Manzanni 2:31 na faɗi cewa ya tafi Hades bisa ga (New American Standard Bible), amma “Hades” ba jahannama ba ce. Kalmar “Hades” na bayyana wurin matattu. Wahayin Yahaya 20:11-15 cikin NASB ko New Internation Version ta bayar da bambanci a fili tsakanin biyu nan. Jahannama shine wurin din din din da wurin ƙarshe na shari’ar ɓatattu. Hades wuri ne na wucin gadi.

Ubangijinmu ya bayar da ruhunsa ga Uban, ya mutu, kuma a wata sa’i tsakanin mutuwarsa da tashinsa daga matattu, ya ziyarce wurin matattu inda ya bada saƙo ga ruhohi (watakila faɗaɗɗun mala’iku; dubi Yahuza 6) waɗanda ko ta yaya ke da allaƙa da da zamani kafin ruwan tsufana na lokacin Nuhu. Aya 20 ta mai da wannan a sarari. Bitrus bai faɗa mana abin da yayi shelarta ga waɗannan ruhohin kurkuku ba, amma ba zai zama wata saƙo na fansa bane, tun da yake ba a iya ceton mala’iku (Ibraniyawa 2:16). Yana mai yiwuwa shela nasara ne kan Shaidan da kuma rundunoninsa (1Bitrus 3:22; Kolosiyawa 2:15). Afisawa 4:8-10 kuma da alama na nuna cewa Kiristi ya tafi “Firdausin” (Luka 16:20;23:43) kuma ya kwashi zuwa sama dukkan waɗancan waɗanda sun bada gaskiya gare shi tun kafin mutuwarsa. Wannan wurin bata bada yawan bayyani game da abin da ake nufi da “bida kamammun fursunonin yaƙi.”

Hakanan, faɗin duk waɗannan, Littafi Mai Tsarki gaba ɗaya babu sarari ainihi abin da Kiristi yayai na waɗannan kwana uku tsakanin mutuwarsa da tashinsa daga matattu. Yana da alama, cewa yana wa’azin nasara kan faɗaɗɗun mala’iku da/ko kuma marasa bada gaskiya. Abin da zamu iya sani tabbatacce shine cewa Yesu ba wai ya bai wa mutane dama ta biyu don ceto ba ne. Littafi Mai Tsarki na faɗa mana cewa zamu fuskanci shari’a bayan mutuwa (Ibraniyawa 9:27), ba dama na biyu bane. Babu ainihin wata tabbatacce amsa ta zahiri ga abin da Yesu yake yi na lokaci tsakanin mutuwarsa da tashinsa daga matattu. Watakila wannan shine ɗaya daga asiran da zamu gane da zarar mun kai ga ɗaukaka.

English



Koma zuwa shafin gida na Hausa

Ina ne Yesu yake na kwana uku tsakanin mutuwarsa da tashinsa daga matattu?
© Copyright Got Questions Ministries