settings icon
share icon
Tambaya

Yaya zan iya sanin nufin Allah don rayuwa ta? Ko mene ne Littafi Mai Tsarki ke cewa game da sanin nufin Allah?

Amsa


Akwai mabuɗai biyu na sanin nufin Allah don wata hali (1) Ka tabbatar abin da kake tambaya ko tunanin aikatawa zai ɗaukaka Allah kuma ya taimake ka yin girma a ruhaniyance. Idan waɗannan abubuwa biyu gaskiya ne kuma Allah har yanzu bai baka abin da kake tambaya ba – sa’anan bila haddin bai zama nufin Allah don ka sami abin da kake tambaya ba. Ko dai, watakila kana bukata kawai ka jira na ɗan lokaci don abin. Sanin nufin Allah a waɗansu lokaci na da wuya. Mutane suna son Allah ya gaya musu abin da zasu yi kurum- inda za a yi aiki, inda za a yi zama, wanda za a aura, da dai sauransu. Romawa 12:2 tan gaya mana, “ Kada ku biye wa zamanin nan, amma ku bar halin ku ya sake ta wurin sabunta hankalin ku ɗungum, don tabbtar da abin da Allah ke so, wato nufin sa kyakyawa, abin karɓa, cikakke kuma.”

Allah ba safai yakan ba mutane wata masaniya takanas da kuma kai tsaye ba. Allah yakan yardar mana muyi waɗansu zaɓi game da waɗancan abubuwa. Shawara kaɗai wanda Allah bai so mu ɗauka ita ce mu yanke shawara na aikata zunubi ko ƙin nufin sa. Allah yana son muyi waɗansu zabi waɗanda sun yarda da nufin sa. Hakanan, yaya zaka san abin da nufin Allah yake domin ka? Idan kana tafiya kurkusa tare da Ubangiji kuma da gaske kana sha’awar nufin sa don rayuwar ka- Allah zai sa marmarin Sa kan zuciyarka. Mabuɗin shine a san nufin Allah, ba naka ba. “Ka nemi farin cikin ka a wurin Ubangiji, zai kuwa biya maka bukatarka” (Zabura 37:4). Idan Littafi Mai Tsarki bata yi magana gaba da ita ba, kuma zai iya da gaske amfane ruhaniyarka – haka littafi Mai Tsarki ta baka “iznin” yanke shawara da kuma ka bi zuciyarka.

EnglishKoma zuwa shafin gida na Hausa

Yaya zan iya sanin nufin Allah don rayuwa ta? Ko mene ne Littafi Mai Tsarki ke cewa game da sanin nufin Allah?
© Copyright Got Questions Ministries