settings icon
share icon
Tambaya

Yaya zan iya rinjayar zunubi cikin rayuwa ta na Kirista?

Amsa


Littafi Mai Tsarki tana magana game da waɗannan abubuwa da muke da su mu ci nasara da zunubanmu.

(1) Ruhu Mai Tsarki- Kyauta guda da Allah ya bamu (Ikilisiyarsa) da zama da nasara cikin rayuwar Kirista shine Ruhu Mai Tsarki. Allah ya bambanta ayyukan jiki da ɗiya na Ruhu cikin Galatiyawa 5:26-25. Acikin wurin ana kira garemu muyi tafiya cikin Ruhu. “Dukan masu bada gaskiya sun riga sun mallaki Ruhu Mai Tsarki, amma wannan wurin tana gaya mana cewa muna bukatar muyi tafiya cikin Ruhu, muna bada kai ga mulkinsa. Wannan na nufin a zaɓa a sa “ takalmin fata” ga ƙutawar Ruhu Mai Tsarki cikin rayukanmu maimakon a biye wa jiki.

Bambancin da Ruhu Mai Tsarki kan iya yi a rayuwar mai bada gaskiya an nuna shi a rayuwar Bitrus, wanda kafin ya cika da Ruhu Mai Tsarki ya musunci Yesu sau uku, kuma wannan daga baya ya ce zai bi Kiristi har ga mutuwa. Bayan an cika shi, yayi magana a fili kuma da ƙarfi ga Yahudawa a ranar Fentikos na mai Ceto.

Wani yakan yi tafiya cikin Ruhu da yana ƙoƙari kada ya “sa murfi” kan ƙutawar Ruhu ( “bicewar Ruhu” yadda an faɗa cikin (1Tasalonikawa 5:19) da nema maimako a cika da Ruhu (Afisawa 5:18-21). Yaya mutum kan cika da Ruhu Mai Tsarki? Da farko dai, ya zama na zaɓin Allah ne yadda ma take ko a cikin Tsohon Alƙawari. Ya zaɓi mutane ɗai ɗai da aukuwa takamaimai cikin Tsohon Alƙawari ya ciccika mutane ɗai ɗai da ya zaɓa su kammala aikin da Ya so suyi (Farawa 41:38; Fitowa 31:3; Littafin Lissafii 24:2; 1Samuila 10;10; da sauransu). Ina bada gaskiya cewa akwai shaida cikin Afisawa 5:18-21 da Kolosiyawa 3:16 cewa Allah kan zaɓa ya cika waɗanda suna ciccika kansu da maganr Allah yadda ana gani gaskiyar sakamakon kowace cikawa cikin waɗancan yayi kuma. Hakanan, wannan ya kawo mu ga abu na gaba.

(2) Maganar Allah, Littafi Mai Tsarki- 2Timoti 3:16-17 tana faɗi cewa Allah ya bamu maganarsa a shirya mu don kowace kyakyawan aiki. Tana koyar mana yadda zamu yi rayuwa da abin da zamu gaskata, tana bayyana mana lokacin da mun zaɓi saɓanin hanyoyi, takan angaza mana mu koma tafarki na daidai, kuma takan taimake mu mu tsaya kan tafarki. Yadda Ibraniyawa 4;12 ke faɗi, ita rayayyiya ce da ƙarfi kuma takan iya huda ga zukatan mu ta tumbuke dukkan zurfafan damuwar da bisa ganin mutum ba a iya rinjaye ta ba. Mai Zabura yayi faɗi game da ikon ta na sauya rayuwa cikin Zabura 119:9,11,105 da waɗansu ayoyi. Joshuwa an gaya mana cewa mabuɗin nasararsa cikin samun nasara bisa maƙiyansa (kwatancin yaƙin mu na ruhaniya) shine kar ya manta da wannan dabarar amma a maimako yayi tunani a kan ta yini da dare don ya iya kiyaye ta. Hakanan yayi, ko lokacin da abin da Allah ya umarce shi bai zama da azanci ta soja ba, kuma wannan ita ce mabudi ga nasararsa cikin yaƙe-yaƙensa don ‘Ƙasar Alƙawari.

Wannan abu shine wanda kullum muke ɗauka da salon rashin muhimmanci. Muna nuna dan aiki ga ita ta riƙe Littattafan mu Masu Tsarki zuwa Coci ko karanta addu’o’in yini, amma mun kasa mu haddace ta,yi tunani a kai, a nemi shafa cikin rayukan mu, iƙirari da zunuban da ta bayyana, ana yabon Allah don kyautai da ta bayyana Shine ya bamu su. Muna a kullum ko dai da rashin marmarin ci ko kuwa da zarin ci sa’anda an zo ga Littafi Mai Tsarki ko dai mu ci daidai yadda zamu rayu a ruhaniyanceta ci daga Kalma daidai loton da mun je Coci (amma ba a taba taunawa isasshe a zama da lafiya, Kirista masu yin girma) ko dai mu zo kullum mu ci amma ba a taɓa yin tunani na lokacin da zai isa a sami ni’ima daga gareta.

Tana da muhimmanci cewa idan baka sami al’ada na binciken maganar Allah a kowace yini a hanya mai ma’ana ba, da na haddace ta yayin da ka zo ga wuraren da Ruhu Mai Tsarki ya sanya a zuciyarka, cewa yayi ka fara maida ita al’ada. Ina bada shawara kuma ka fara mujallar yini (ko dai a na’ura mai ƙwaƙwalwa idan kana mai bugawa da sauri fiye da rubutun hannu) ko cikin littafin rubutun da aka ɗaura, da sauransu. Ka mai da shi al’ada kar ka bar Kalma sai bayan da ka rubuta abin da ka tsinta daga gareta. Kullum ina rubuta addu’o’i ga Allah ina roƙon Sa ya taimake ni in sauya a wuraren da yayi magana da ni game da su ma. Littfi Mia Tsarki ne kayan aiki da Ruhu ke mora cikin rayukan mu da rayukan waɗansu (Afisawa 6:17), na lalle ne da babban Sashi na makaman da Allah ya bamu muyi faɗace-faɗace na ruhaniya (Afisawa 6:12-18)!

(3) Addu’a- Wannan kuma shine abu na lalle da Allah ya bamu. Kuma shine wata dabarar da Kirista kullum ke ambaton leɓe amma suna ban tausayin amfani da ita. Muna da taruwai na addu’a, lokatan addu’a, da sauransu, amma bama samun amfani da ita yadda Ikilisiyar farko ta nuna misali (Ayyukan Manzanni 3;1; 4:31; 13:1-3, da sauransu). Bulus yana maimaita ambaton yadda yake addu’a wa waɗanda yake hidimta wa. Ko mu bama sa’anda muke mu kaɗai, amfani da wannan babban abu da ke akwai gare mu. Amma Allah ya bamu alƙawarnasa masu al’ajabi game da addu’a (Matiyu 7:7-11; Luka 18:1-8; Yahaya 5:14-15, da sauransu). Da kuma Bulus ya ƙunsa ta cikin nassin sa kan yi ɗamara don yaƙin ruhaniya (Afisawa 6:18)!

Yaya muhimmancin sa take? Sa’anda kuma ka dubi Bitrus, zaka sami kalmomin Kiristi gare shi cikin Gonar Gatsemani kafin musun Bitrus. A wurin, yadda Yesu ke addu’a, Bitrus na barci. Yesu ya tashe shi kuma yace, “Ku zauna a faɗake, kuyi addu’a, kada ku faɗa ga gwaji. Lalle ruhu ya ɗauka, amma jiki rarrauna ne” (Matiyu 26:41). Kai, kamar Bitrus, na son yin abin da ke daidai amma baka sami ƙarfi ba. Muna bukatar mu bi gargaɗin Allah mu ci gaba da nema, ci gaba da ƙwanƙwasawa, ci gaba da roƙa--- kuma Shi zai bamu ƙarfin da muke bukata (Matiyu 7;7 da na biye). Amma kuma muna bukata muyi fiye da kawai maganar leɓe ga wannan dabarar.

Ba na faɗi cewa addu’a dabo ba ce. Bata zama ba. Allah mai ban tsoro ne. Addu’a a sauƙaƙe mu yarda da iyakacin kanmu da ikon Allah marar matuƙa da juya gare shi don ƙarfin nan na yin abin da Shi yana son muyi ( ba abin da MUKE son yi ba)(1Yahaya5;14-15).

(4) Ikilisiya – Abu mai taimako na ƙarshe shine kuma wanda muke faye yin biris da ita. Sa’anda Yesu ya aike almajiran sa waje, ya aike su bibbiyu (Matiyu 10:1). Sa’anda muna karanta game da tafiye-tafiyen bishara cikin Ayyukan Manzanni, ba sa fita waje far ɗaya ba, amma cikin ruƙuni bibbiyu ko fiye. Yesu ya faɗi cewa inda biyu ko uku sun taru cikin sunan Sa, Shi yana nan a tsakanin su (Matiyu 18:20). Ya umarce mu da kar mu fasa tattaruwar mu gu ɗaya yadda waɗansu suka saba yi amma mu mori lokacin don ƙarfafa juna cikin ƙauna da ayyuka masu kyau (Ibraniywawa 10:24-25). Yana gaya mana mu iƙirarin laifofinmu ga juna (Yakubu 5:16). A cikin littattafan hikima na Tsohon Alƙawari, an gaya mana cewa yadda ƙarfe ke watsa ƙarfe, haka nan mutum ke watsa fuskar abokinsa (Misalai 27:17). “Igiya riɓi uku tana da wuyar tsinkawa.” Akwai ƙarfi cikin alƙaluma (Mai Hadishi 4:11-12).

Waɗansu waɗanda na san su sun sami ƴan’uwa cikin Almasihu (ko ƴan’uwa mata cikin Kiristi) waɗanda sukan zo tare ta wayar iska ko ta mutum da mutum kuma suna faɗi yadda suke yi cikin tafiyarsu na Kirista, yadda yana yiwuwa su sami gwagwarmaya, da alhakin shafa Maganar Allah ga dangantakar su, da sauransu.

Waɗansu lokatai canji yakan zo da sauri. Waɗansu lokatai, a waɗansu wurare, ta kan zo ne a hankali. Amma Allah yayi alƙawari mana cewa kamar yadda muke amfani da abubuwa Sa na taimakon mu, Shi ZAI kawo mana sauyi cikin rayuwar mu. A dage da sanin cewa Shi mai aminci ne ga alƙawaran Sa!

English



Koma zuwa shafin gida na Hausa

Yaya zan iya rinjayar zunubi cikin rayuwa ta na Kirista?
© Copyright Got Questions Ministries