settings icon
share icon
Tambaya

Mene ne ake nufi da ka karɓi Yesu a matsayin mai ceton kanka?

Amsa


Ko ka taɓa karɓi Yesu a matsayin mai ceton kanka? Kafin ka amsa, ka yardar mani in bayyana tambayar. Da a gane da wannan tambaya daidai, dole ne da farko ka gane”Yesu Kiristi,”“Kanka” da”Mai Ceto” da kyau.

Wane ne Yesu Kiristi? Mutane da dama zasu yarda da Yesu Kiristi a matsayin nagarin mutum, babban malami, ko kuwa annabin Allah. Waɗannan abubuwa sune tabbatattun gaskiya mafi duk game da Yesu. Littafi Mai Tsarki ta gaya mana cewa Yesu shine Allah cikin tsoka, Allah ya zama ɗan Adam (dubi Yahaya 1:1, 14). Allah ya zo duniya ya koyar mana, ya warkad da mu, yayi mana gyara, ya gafarce mu- kuma ya mutu dominmu! Yesu Kiristi Allah ne, mahalicci, Ubangiji babba. Ko ka karɓi wannan Yesu?

Mece ce mai ceto kuma me yasa muke bukatar mai ceto? Littafi Mai Tsarki tana ce mana mu duk mun aikata zunubi, mu duk mun aikata miyagun ayyuka (Romawa 3: 10-18). A sakamakon zunubin mu, mun cancanci fushin Allah da hukunci. Hukunci kadai madaidaici don zunuban da aka aikata ga Allah marar matuƙa kuma madawwami shine hukunci marar iyaka ( Romawa 6:23; Wahayin Yahaya 20:11-15). Shine yasa muke bukatar mai ceto!

Yesu Kiristi, yazo duniya kuma ya mutu a madadinmu. Mutuwar Yesu, a matsayin Allah cikin tsoka, ya zama biya marar iyaka ne don zunubanmu (2 Korantiyawa 5:21). Yesu ya mutu da ya biya hukunci don zunubanmu (Romawa 5:8). Yesu ya biya farashi da cewa kada mu sake biya ba. Tashin Yesu daga matattu ya gwada cewa mutuwarsa ta isa ta biya hukunci don zunubanmu. Shine yasa Yesu ne ɗaya kuma mai ceto kaɗai! (Yahaya 14:6; Acts 4:12). Ko Yesu ne da kansa mai cetonka?

Ko Yesu ne mai ceton”kanka”? Mutane da dama suna duban Kiristanci da kamar zuwan ikilisiya, aikata al’ada, rashin yin waɗansu zunubai. Wancan ba Kiristanci ba ne. Kiristanci na gaskiya shine dangatakar mutum kansa tare da Yesu Kiristi. Karɓan Yesu a matsayin mai ceton ka tana nufin ka aza bangaskiyar kanka da amincewa cikin Sa. Babu wanda an cece shi ta bangaskiyar waɗansu ba. Babu wanda an gafarce shi don yin waɗansu ayyuka ba. Hanya kaɗai na samun ceto shine ka karɓi Yesu da kanka a matsayin mai ceto, kana amince da mutuwarsa a matsayin biya ne domin zunubanka, kuma tashinsa daga matattu a matsayin garanti na rai madawwami (Yahaya 3:16). Ko Yesu ne mai cetonka na kanka?

Idan kana son ka karɓi Yesu Kiristi a matsayin mai cetonka, ga samfurin addu’a anan. Ka tuna, faɗar wace nan addu’a ko wata addu’a dabam ba zai cece ka ba. Amincewa ce kaɗai cikin Kiristi wanda zai iya cece ka daga zunubi. Wace nan addu’a, hanya ce mai sauƙi a furta ga Allah bangaskiyarka a cikin Sa kuma ka gode masa don ya tanadar maka da ceto.”Allah, na sani cewa nayi zunubi gareka kuma na cancanci hukunci. Amma Yesu Kiristi ya ɗauki hukuncin da ya cancance ni, don ta wurin bangaskiya a cikinsa in sami gafartawa. Na juyo daga zunubaina kuma na sa amincewa tawa a cikinka don ceto. Na gode maka don alherinka mai ban mamaki da kuma gafara – kyautar rai madawwami! Amin!”

Ko ka yanke shawara domin Kiristi saboda abin da ka karanta anan? Idan haka ne, don Allah danna kan “Na riga na karɓi Kiristi yau” botin na ƙasa.

EnglishKoma zuwa shafin gida na Hausa

Mene ne ake nufi da ka karɓi Yesu a matsayin mai ceton kanka?
© Copyright Got Questions Ministries