settings icon
share icon
Tambaya

Mene ne Littafi Mai Tsarki tana fadi game da shan barasa/giya? Ya zama zunubi ne ga Kirista ya sha barasa/giya?

Amsa


Littafi na ƙunshe da gargaɗai da yawa game da shan barasa (Littafin Firistoci 10:9; Littafin Lissafi 6:3; Maimaitawar Shari’a 29:6; Littafin Mahukunta 13:4,7,14; 1Samuila 1:15; Misalai 20:1; 31:4,6; Ishaya 5:11,22;24:9;28:7;29:9;56:12; Mika 2:11; Luka 1:15). Duk da haka, Littafi bata hana lalle kada Kirista ya sha biya, giya ko kowane abin sha mai sa maye. A gaskiya, wasu nassoshi na zancen barasa cikin tabbatattun sharuɗɗa. Mai Hadishi 9:7 na umarta “ka sha ruwan inabinka da fara’a.” Zabura 104:14-15 na furci cewa Allah ya bada ruwan inabi “da zai sa shi farin ciki.” Amos 9:14 na zancen shan ruwan inabi daga gonar inabinsa a matsayin alamar albarkar Allah. Ishaya 55:11 tana ƙarfafa “I, zo mu sayi ruwan inabi da madara...”

Abin da Allah ya dokaci Kiristoci game da shan barasa shine su guje buguwa (Afisawa 5:18). Littafi Mai Tsarki ta hukunta buguwa da abubuwa makamantanta (Misalaii 23:29-35). An dokaci Kiristoci kuma kada su yarda jikunansu ya sami “mallaka” da ko mene (1Korantiyawa 6:12; 2Bitrus 2:19). Shan barasa fiye da kima babu shakka jaraba ne. Littafi kuma ta hana Kirista daga yin kome da mai yiwuwa yasa wasu Kiristoci yin laifi ko mai yiwuwa ya ƙarfafa su yin zunubi gaba da lamirinsu (1Korantiyawa 8:9-13). Bisa ga hasken waɗannan ƙa’idoji, zai zama da wuya matuƙa ga wani Kirista ya ce yana shan barasa don ɗaukakar Allah (1Korantiyawa 10:31).

Yesu ya maida ruwa zuwa ruwan inabi. Ya zama kamar cewa Yesu ya sha ruwan inabi a wani sa’i (Yahaya 2:1-11; Matiyu 26:29). A zamanin Saboon Alƙawari, ruwan sha bata da tsabta ainun. Banda dabarun tsabtace ruwa na zamanin yau, ruwa kullum na cike ne da ƙwayoyin cuta, cututtuka da kowace irin abin gurɓatawa. Haka ɗin gaskiya ne cikin masu yawan ƙasashe masu tasowa a yau. A sakamakon haka, mutane kullum na shan ruwan inabi (ko ruwan tonis) saboda yafi zama da rashin gurɓacewa. Cikin 1Timoti 5:23, Bulus yana gabatar wa Timoti da tsai da shan ruwa (wanda mai yiwuwa ita ce ke sa masa matsalolin cikinsa) kuma a madadi ya sha ruwan inabi. A wannan lokaci, ruwan inabi na yin kumfa (ƙunshe da abin sa maye) amma ba lalle na adadin yadda take a yau ba. Bai zama daidai a faɗi cewa ya zama ruwan tonis ba, amma kuma ba daidai a faɗi cewa ya zama daidai kamar da barasa da an cika amfani da shi yau. Da kuma, Littafi bata hana Kiristoci lalle daga shan giya, ruwan inabi, ko wani abin sha mai ƙunshe da barasa ba. Barasa bai zama, a ciki da na kanta, a shafe da zunubi ba. Ya zama, buguwa da jaraba ga barasa da Kirista dole ne ya janye kansa gaba ɗaya (Afisawa 5:18; 1Korantiyawa 6:12).

Barasa, an sha da jimla kima, ba mai cutarmu ko jaraba bane. A gaskiya, waɗansu likitoci na bada shawara a sha adadi kaɗan na jar inabi don amfani kiwon lafiyarta, musamman ga zuciya. A sha barasa da adadi na kima ya zama batun ƴancin Kirista. Buguwa da jaraba zunubi ne su. Duk da haka, bisa ganin Littafi Mai Tsarki game da barasa da abin da zai jawo, bisa ga sauƙin faɗuwa cikin jarabar shan barasa fiye da kima, da kuma bisa yiwuwar sa wani yin laifi da/ko tuntuɓen wadansu – kullum yafi kyau ga Kirista yaki gaba ɗaya daga shan barasa.

EnglishKoma zuwa shafin gida na Hausa

Mene ne Littafi Mai Tsarki tana fadi game da shan barasa/giya? Ya zama zunubi ne ga Kirista ya sha barasa/giya?
© Copyright Got Questions Ministries