settings icon
share icon
Tambaya

Mene ne muhimmancin baftismar Kirista?

Amsa


Baftismar Kirista, bisa ga Littafi Mai Tsarki, ya zama shaidar waje na abin da ya gudana daga cikin ran mai bada gaskiya. Baftismar Kirista tana misalta kamantuwar mai bada gaskiya tare da mutuwar Kiristi, binnewa, da tashi daga matattu. Littafi Mai Tsarki ta furta, “Ashe, ba ku sani ba du ɗakwancin mu da aka yiwa baftisma a cikin Almasihu Yesu, cikin mutuwa tasa aka yi mana baftismar ba? Saboda haka an binne mu dashi ke nan ta baftisma cikin mutuwa tasa, domin kamar yadda aka tada Almasihu daga matattu ta ɗaukakar Uba haka mu ma muyi zaman sabuwar rayuwa” (Romawa 6:3-4). Cikin baftismar Kirista, aiwatar da nutsarwa cikin ruwa tana hoton binnewa ne tare da Kiristi. Fitowa daga cikin ruwa tana gwada tashin Kiristi daga matattu ne.

Cikin baftismar Kirista, kamata yi akwai abin cancanta guda biyu kafin ayi wa mutum baftisma: (1)Wanda ake masa baftisma dole ne ya amince da Yesu Kiristi a matsayin mai Ceto, da kuma (2) Mutumin dole ya gane abin da baftisma ke nufi. Idan mutum ya san Ubangiji Yesu a matsayin mai ceto, ya gane cewa baftismar kirista ya zama mataki na biyayya cikin shela a fili bangaskiyarsa cikin Kiristi, da kuma na sha’awar yin baftisma – sa’anan babu wata dalilin da zai hana mai ban gaskiya daga yin baftisma. Bisa ga Littafi Mai Tsarki, baftismar Kirista a sauƙaƙe mataki na biyayya ne, shaida a fili na bangaskiyar mutumin cikin Kiristi kaɗai don ceto. Baftismar Kiristi na da muhimmanci don ta zama matakin biyayya –a sanar a fili da bangaskiya cikin Kiristi da miƙa wuya gare shi, kuma da kamantuwa tare da mutuwar Kiristi, binnewa, da tashi daga matattu.

EnglishKoma zuwa shafin gida na Hausa

Mene ne muhimmancin baftismar Kirista?
© Copyright Got Questions Ministries