settings icon
share icon
Tambaya

Mene ne Littafi Mai Tsarki ke faɗi game da Kirista da cire zakka?

Amsa


Cire zakka ya zama wata batu ne da yawanci Kiristoci na gwagwarmaya da ita. A cikin ikilisiyoyi da dama ana girmama cire zakka fiye da kima. A lokaci guda kuma, Kiristoci da dama suna ƙin bada kai ga gargaɗin Littafi Mai Tsarki game da bada baye-baye ga Ubangiji. Cire zakka/bayarwa an nufe su da zama abin murna, abin albarka. Assha, wannan ba safai batun yake cikin ikilisiya a yau ba.

Cire zakka ya zama tunanin Tsohon Alƙawari ne. Zakka ta zama ƙa’idar doka wanda dukkan Isra’ilawa zasu bada 10% na komene da sun sami albashi da suka nome ga Alfarwa ta Sujada/Haikali (Littafi Firistoci 27:30; Littafin Lissafi 18:26; Maimaitawar Shari’a 14:24; 2Tarihi 31:5). Waɗansu na da ganewa zakkar Tsohon Alƙawari a matsayin tsara haraji domin tanadin bukatun Firistoci da Lawiyawa na tsarin hadayu. Babu inda Sabon Alƙawari ta umarta, ko ma ta bada goyon baya cewa Kiristoci su bada kai ga tsarin cire zakka bisa doka. Bulus yayi magana cewa masu bangaskiya su ajiye rabon abin shiga nasu garin a tallafi ikilisiya (1Korantiyawa 16:1-2).

Babu inda Sabon Alƙawari ta ayyana takamaimai a ajiye a gefe wani kaso bisa ɗari na kuɗin shiga, amma kawai ta ce ya zama “gwargwadon samunsa” (1Korantiyawa 16:2). Ikilisiyar Kirista sun ɗauka daga asali adadi 10% daga zakkar Tsohon Alƙawari kuma suka shafa ta a matsayin “mafi ƙanƙanta da aka bada shawara” don Kiristoci cikin bayarwar su. Ko da yake Sabon Alƙawari bata kwatanta jimla takamaimai ba ko kashi nawa daga cikin ɗari da za a bayar, tayi magana game da muhimmanci da fa’idodin bayarwa. Ya kamata su bayar yadda zasu iya, “gwargwadon samunsa.” Wasu lokatai wannan na nufin a bayar fiye da zakka, wasu lokatai zai iya zama a bayar ƙasa da zakka. Duk ya zama bisa ga iyawar Kirista da kuma bukatun ikilisiyar Allah kan ko ya cire zakka da/ko nawa ne shi ko ita kamata a bayar (Yakubu 1:5). Sai kowa ya bayar yadda yayi niyya, ba tare da ɓacin rai ko tilastawa ba,domin Allah na son mai bayarwa da daɗin rai” (2Korantiyawa 9:7).

EnglishKoma zuwa shafin gida na Hausa

Mene ne Littafi Mai Tsarki ke faɗi game da Kirista da cire zakka?
© Copyright Got Questions Ministries