settings icon
share icon
Tambaya

Waɗanne ne dokoki huɗu na ruhaniya?

Amsa


Dokoki Huɗu na Ruhaniya sun zama hanya ce na yada albishir na ceto wanda ke samuwa ta wurin bangaskiya cikin Yesu Kiristi. Ta zama hanya ce mai sauƙi a shirya muhimmiyar labari cikin bishara zuwa ma’ana kashi huɗu.

Na farko daga Dokoki Huɗu na Ruhaniya ita ce,”Allah yana ƙaunarka kuma yana da wata shiri mai ban mamaki don ranka” yahaya 3:16 ta gaya mana,” Saboda ƙaunar da Allah yayi wa duniya, har ya bada makaɗaicin Ɗansa, domin duk wanda ya gaskata da shi kada ya halaka, sai dai ya sami rai madawwami.” Yahay 10:10 tana bamu dalilin da yasa Yesu ya zo,”...Ni kuwa na zo ne domin su sami rai, su same shi a yalwace .” Mene ne yake toshe mu daga ƙaunar Allah? Mene ne yake hana mu daga samun rai a yalwace?

Na biyu daga Dokoki Huɗu na Ruhaniya ita ce,”Zunubi ya shafi ɗan adam kuma don haka a rabe yake daga Allah. A sakamakon haka, ba zamu iya sanin shirin Allah mai ban mamaki don rayukanmu ba.” Romawa ta tabbatas da wannan labari,”gama ƴan adam duka sunyi zunubi, sun kasa kuma ga ɗaukakar Allah.” Romawa 6:23 ta bamu abubuwan da zunubi ya haifar,”... sakamakon zunubi mutuwa ne.” Allah ya halicce mu mu yi zumunci tare shi. Amma dai, ɗan adam ya kawo zunubi zuwa cikin duniya, kuma saboda haka ya rabu daga Allah. Mun rushe dangataka tare da shi wanda Allah ya nufe da samu. Mece ce hanyar warwarewa?

Na uku daga Dokoki Huɗu na Ruhaniya ita ce,”Yesu Kiristi ne kaɗai tanadin Allah domin zunubanmu. Ta wurin Yesu Kiristi, zamu iya sami gafarar zunubanmu kuma a mayar da daidaitaccen dangataka da Allah.” Romawa 5:8 tana gaya mana, : Amma kuwa Allah na tabbatar mana da kaunar da yake mana, wato tun muna masu zunubi, Almasihu ya mutu dominmu.” 1 Korantiyawa 15:3-4 tana sanar mana akan abin da muke bukata mu sani kuma mu gaskata garin a sami ceto,”... cewa an binne shi, an tada shi a rana ta uku, kamar yadda littattafai suka faɗa...” Yesu da kansa ya furta cewa Shine kaɗai hanyar ceto cikin Yahaya 14:6,” Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Ba mai zuwa wurin Uba , sai ta wurina.” Yaya zan iya karɓar wannan kyautar ceto mai ban mamaki?

Na hudu daga Dokoki Huɗu na Ruhaniya ita ce,” Dole mu sa bangaskiyarmu cikin Yesu Kiristi a matsayin mai ceto garin a karɓi kyautar ceto kuma a san shirin Allah mai ban mamaki domin rayukanmu.” Yahaya 1:12 ta kwatanta mana wannan,” Amma duk iyakar waɗanda suka karɓe shi, wato masu gaskatawa da sunansa, ya basu ikon zama ƴaƴan Allah.” Ayyukan Mazanni 16: 31 ta faɗe ta ƙarara ainun,”... ka gaskata da Ubangiji Yesu, zaka sami ceto!...” Zamu iya samun ceto ta alheri kaɗai, ta wurin bangaskiya kaɗai, cikin yesu Kiristi kaɗai. (Afisawa 2:8,9)

Idan kana son ka karɓi Yesu Kiristi a matsayin mai cetonka, ga samfurin addu’a anan. Ka tuna, faɗar wace nan addu’a ko wata addu’a dabam ba zai cece ka ba. Amincewa ce kaɗai cikin Kiristi wanda zai iya cece ka daga zunubi. Wace nan addu’a, hanya ce mai sauƙi a furta ga Allah bangaskiyarka a cikin Sa kuma ka gode masa don ya tanadar maka da ceto.”Allah, na sani cewa nayi zunubi gareka kuma na cancanci hukunci. Amma Yesu Kiristi ya ɗauki hukuncin da ya cancance ni, don ta wurin bangaskiya a cikinsa in sami gafartawa. Na juyo daga zunubaina kuma na sa amincewa tawa a cikinka don ceto. Na gode maka don alherinka mai ban mamaki da kuma gafara – kyautar rai madawwami! Amin!”

Ko ka yanke shawara domin Kiristi saboda abin da ka karanta anan? Idan haka ne, don Allah danna kan “Na riga na karɓi Kiristi yau” botin na ƙasa.

EnglishKoma zuwa shafin gida na Hausa

Waɗanne ne dokoki huɗu na ruhaniya?
© Copyright Got Questions Ministries