settings icon
share icon
Tambaya

Ko ceto ta bangaskiya kaɗai ne, ko ta bangaskiya haɗe da ayyuka?

Amsa


Wannan watakila ita ce tambaya mafi muhimmanci cikin dukkan tauhidin kirista. Wannan tambaya ita ce sanadiyar Jaddada- tsaguwa tsakanin Ikilisiyar Ikilisiyar Yan Tawaye da Ikilisiyar Katolika. Wannan tambaya ita ce mabudin bambanci tsakanin Kiristanci na Littafi Mai Tsarki da kuma yawancin “Kirista” kungiyoyin bori. Ceto ta bangaskiya kaɗai ne, ko ta bangaskiya haɗe da ayyuka? An cece ni kawai ta gaskatawa da Yesu, ko sai na gaskata da Yesu kuma in yi waɗansu abubuwa?

An mai da tambayar bangaskiya kaɗai ko bangaskiya haɗe da ayyuka da wuya ta waɗansu nassoshin Littafi Mai Tsarki marasa sulhuntuwa. Kwatanta Romawa 3:28, 5:1 da Yakubu 2:24. Waɗansu na ganin bambancin tsakanin Bulus (ceto daga bangaskiya kadai) da kuma Yakubu (ceto ta bangaskiya hade da ayyuka). A gaskiya, Bulus da Yakubu ba sa rashin jituwa ko kaɗan. Maganar rashin jituwa kaɗai da mutane na da’awa ita ce kan dangantaka tsakanin bangsakiya da ayyuka. Bulus a rukunance yana faɗi cewa baratswa ta wurin bangaskiya kaɗai (Afisawa 2:8-9) yayin da Yakubu ana gani na faɗi cewa baratswa ta bangaskiya haɗe da ayyuka. Wannan al’amari mai wuya ga alama zata sami amsa ta wurin gwajin abin da ke daidai Yakubu ke magana a kai. Yakubu yana bayyana kuskuren koyarwa cewa mutum kan iya sami bangaskiya ban da haifar da kowanne ayyuka masu kyau (Yakubu 2:17-18). Yakubu yana ƙarfafa magana cewa bangaskiyar gaske cikin Kiristi kan haifar da sakewar rayuwa da ayyuka masu kyau (Yakubu 2:20-26). Yakubu baya faɗi cewa baratswa ta bangaskiya ne haɗe da ayyuka ba, amma kuma cewa mutumin da da gaske ne an baratas ta bangaskiya zai sami kywawan ayyuka a rayuwarsa. Idan mutum na da’awar shi mai bangaskiya ne, amma baya ayyuka masu kyau cikin rayuwarsa – to shi bila haddin baya da bangaskiya ta gaske cikin Kiristi ba (Yahaya 2:14,17,20,26).

Bulus na faɗin abu ɗaya ne cikin rubuce-rubucensa. Ƴaƴa masu kyau da masu bada gaskiya zasu samu a cikin rayuwar su ga jerin su cikin Galatiyawa 5:22-23. Nan take bayan an faɗa mana cewa an cece mu ta bangaskiya, ba ayyuka ba (Afisawa 2:8,9), Bulus ya sanar mana cewa an halicce mu muyi kyawawan ayyuka (Afisawa 2:10). Bulus ya zaci rayuwar da an sake kamar daidai kamar yadda Yakubu yake, “ Saboda haka, duk wanda ke na Almasihu, sabuwar halitta ne, tsohon al’amari duk ya shuɗe, ga shi, kome ya zama sabo” (2Korantiyawa 5:17)! Yakubu da Bulus ba sa rashin jituwa a kan koyarwar su kan ceto ba. Sun ɗoshi fanni ɗaya ne daga fuskoki dabam dabam. Bulus a sauƙaƙe yana ƙarfafa cewa barataswa ta bangaskiya ne kaɗai yayin da Yakubu ya sa ƙarfi akan magana cewa bangaskiya cikin Kiristi yakan haifar da ayyuka masu kyau.

EnglishKoma zuwa shafin gida na Hausa

Ko ceto ta bangaskiya kaɗai ne, ko ta bangaskiya haɗe da ayyuka?
© Copyright Got Questions Ministries