settings icon
share icon
Tambaya

Mene ne addu’ar mai zunubi?

Amsa


Addu’ar mai zunubi shine addu’ar da mutum yakan yi ga Allah sa’anda sun fahimci cewa su masu zunubi ne kuma cikin bukatar mai ceto. Faɗar addu’ar mai zunubi ba zai cika kome da kanta ba. Addu’ar mai zunubi tana da ƙarfi kaɗai idan da ainihi ta wakilci abin da mutum ya sani, fahimta, kuma ya bada gaskiya game da zunubansu da kuma bukatar ceto.

Wajen farko na addu’ar mai zunubi shine ganewa cewa mu dukanmu masu zunubi ne. Romawa 3:10 tayi shela,” Kamar yadda yake a rubuce cewa, Babu wani mai adalci, babu, ko ɗaya.” Littafi mai Tsarki ta mai da shi a fili cewa dukanmu mun yi zunubi. Dukan mu masu zunubi ne cikin bukatar jinƙai da gafara daga Allah (Titus 3:5-7). Saboda zunubanmu, mun cancanci hukuncin har abada (Matiyu 25:46). Addu’ar mai zunubi ta zama roƙo ne don alheri maimakon hukunci. Ta zama roƙo ne don rahama maimakon fushi.

Waje na biyu na addu’ar mai zunubi shine sanin abin da Allah yayi ya magance ɓacewar da hali zamamnu na zunubi. Allah ya ɗauki tsoka kuma ya zama ɗan adam cikin mutuntakar Yesu Kiristi (Yahaya 1:1,14). Yesu ya koya mana gaskiya game da Allah kuma yayi rayuwar cikakken adalci da rayuwa marar zunubi (Yahaya 8:46; 2 Korantiyawa 5:21). Sa’anan Yesu ya mutu kan gicciye a madadinmu, ɗauke da hukuncin da ya cancance mu (Romawa 5:8). Yesu ya tashi daga matattu ya gwada nasararsa akan zunubi, mutuwa da jahannama ( Kolosiyawa 2;15; 1 Korantiyawa sura 15). Saboda duk wannan, zamu iya sami gafarar zunubanmu da yi mana alƙawarin madawwamiyar gida cikin sama – idan dai kawai zamu sa bangaskiyarmu cikin Yesu Kiristi. Duk abin da yake muyi shine bada gaskiya cewa shi ya mutu a madadinmu kuma ya tashi daga matattu (Romawa 10:9-10). Zamu iya sami ceto ta alheri kaɗai, ta wurin bangaskiya kaɗai, cikin Yesu kaɗai. Afisawa 2:8 tana shela,” Domin ta wurin alheri ne aka cece ku saboda bangaskiya- wannan kuwa ba ƙoƙarin kanku bane, baiwa ce ta Allah.”

Faɗar addu’ar mai zunubi shine hanya mai sauƙi na furta ga Allah cewa kana dogara kan Yesu Kiristi a matsayin mai ceton ka. Babu waɗansu kalmomin”sihiri’ masu haifar da ceto. Bangaskiya ce kaɗai cikin mutuwar Yesu da tashinsa daga matattu zai cece mu. Idan ka gane cewa kai mai zunubi ne kuma cikin bukatar ceto ta wurin Yesu kiristi, ga addu’ar mai zunubi da zaka yi ga Allah.” Allah, na sani cewa ni mai zunubi ne. Na sani cewa na cancanci abubuwan da zunubi na ke haddasa. Duk da haka, ina amincewa cikin Yesu Kiristi a matsayin mai cetona. Na bada gaskiya cewa mutuwarsa da tashinsa daga matattu sun tanadar mani gafarar zunubi. Na amince cikin Yesu kuma Yesu kaɗai a matsayin Ubangiji nawa da mai ceto. Na gode maka Ubangiji, don ka cece ni kuma ka gafarce ni! Amin!”

Ko ka yanke shawara domin Kiristi saboda abin da ka karanta anan? Idan haka ne, don Allah danna kan “Na riga na karɓi Kiristi yau” botin na ƙasa.

English



Koma zuwa shafin gida na Hausa

Mene ne addu’ar mai zunubi?
© Copyright Got Questions Ministries