Tambaya
Ko yin sujada ga tsarkaka / Maryamu daga Littafi Mai Tsarki ne?
Amsa
Littafi Mai Tsarki ya tabbatar mana da cewa Allah kadai za mu yi wa sujada. Duk wani wanda yake karbar sujada ban da Allah a cikin Littafi Mai Tsarki allolin karya ne, wanda shaidan ne da aljanunsa. Dukan masu bin Ubangiji sun ki a yi masu sujada. Bitrus da sauran manzannin sun ki a yi masu sujada (Ayyukan manzanni 10:25–26; 14:13–14). Mala’iku tsarkaka sun ki yarda a yi masu sujada (Wahayin Yahaya 19:10; 22:9). Duka duk maganar iri daya ce, “Yi wa Allah Sujada!”
Roman Katolika sun so su “yanke” wadannan bayyanannun ka’idoji na Littafi Mai Tsarki ta wurin cewa basa yi wa Maryamu ko tsarkaka “sujada” amma suna “girmama” Maryamu da tsarkaka ne kawai. Yin amfani da wata kalmar da bam ba zai canza dalilin da yasa aka yi abun ba. manufar “girmamawa” shi ne ka “dubi abu da bangirma da daraja”. Yanzu ina ne a Littafi Mai Tsarki aka ce mana kada mu darat ta kowa sai Allah kadai. Ba wani laifi ga darajanta amintattun kirista wadanda suka riga mu (dubi Ibraniyawa sura 11). Ba wani laifi ga girmama Maryamu a matsayin Uwar Yesu ta jiki. Littafi Mai Tsarki ya bayyana Maryamu a matsayin “wadda ta sami tagomashi” gun Allah (Luka 1:28). A lokaci guda, ba wani umarni a Littafi Mai Tsarki na darajanta wadanda suka koma sama. Sai dai mu bi sahunsu, I, amma sujada, ko girmamawa, a’a!
Sa’ad da aka matsa masu su ce a zahiri suna yin, sujada ga Maryamu, Katolika za su ce suna yiwa Allah sujada ne ta wurinta, ta wurin daukaka halitta ta musamman da Allah ya yi. Maryamu, a zuciyarsu, ita ce halitta mafi kyau da Allah ya yi, kuma ta wurin daukaka ta, suna daukaka mahaliccinta ne. ga Katolika, wannan kwatankwacin yabo ne ga mai zane ta hanyar yabawa sassakarsa ko zanensa. Matsalar ita ce a zahiri Allah ya yi umarni a kan bauta masa ta wurin abubuwan da aka halitta. Ba za mu russuna mu bauta wa kowace siffa a sama ko a kasa ko a karkashin kasa ba (Fitowa 20:4–5). Romawa 1:25 ba lalle ya zama a bayyane ba: “Saboda sun canza gaskiyar Allah da karya, har yi wa halitta ibada, sun kuma bauta mata, sun ki su yi wa mahalicci, shi wanda yabo ya tabbata a gare shi har abada. Amin.” I, Allah ya halicci abubuwa masu kyau masu ban mamaki. I, Maryamu mutumiyar Allah ce wadda ta cancanci girmamawarmu. A’a, bai kamata mu yi wa Allah sujada wadda ba ta “kai tsaye ba” ta wurin yabon abubuwa (ko mutanen) da Ya halitta. Yin haka kasaitacciyar bautar gumak ne.
Babbar hanyar da Katolika ke “girmama” Maryamu da tsarkaka ita ce ta wurin yi masu addu’a. amma yin addu’a ga wani ban da Allah kadai ba koyarwar Littafi Mai Tsarki ba ce. Ko yi wa Maryamu addu’a ko tsarkaka, ko kuma rokon addu’arsu—ba daya a ciki da yake a Littafi Mai Tsarki. Addu’a wani nau’I ne na sujada. Idan muka yi addu’a ga Allah, muna cewa muna neman taimakonsa ne. yin addu’a ga wani ban da Allah kamar yi wa Allah fashin daukakar da shi kadai yake da ita ne.
Wata hanyar kuma da Katolika ke “girmama” Maryamu da tsarkaka ita ce ta wurin yin siffofinssu da hotunansu. Yan Katolika da yawa suna amfani da hotunan Maryamu da na tsarkaka a matsayin “abin da zai ba ka nasara”. Duk wani karatun Littafi Mai Tsarki zai bayyana wannnan a matsayin kasaitacciyar bautar gumaka (Fitowa 20:4–6; 1 Korantiyawa 12:1–2; 1 Yahaya 5:21). Amfani da rozali ma bautar gumaka ne. kunna kyandir a gaban wata siffa ko hoton tsarkaka bautar gumaka ne. Sa hoton Yusuf da begen cewa ka tsare gidanka (da dai sauran abubuwa da basu kirgo na Katolika) bautar gumaka ne.
Yanayin furtawa ba shi bane matsalar. Ko an bayyana aikin a matsayin “Sujada” ko “girmamawa” ko kuma kowane abu, matsalar iri daya ce. Duk lokacin da ka dauki wani abu da yake na Allah kadai ka dorawa wani, bautar gumaka ne. Littafi Mai Tsarki ya umarce mu kada mu dauakaka kowa, ko mu yi addu’a ga wani, ko dogara ga wani, ko “bautar gumaka” sai Allah kadai. Sai dai mu bautawa Allah kadai. Daukaka, da yabo, girma na Allah ne kadai. Allah ne kadai ya cancanci “ya sami daukaka da girma da kuma iko” (Wahayin Yahaya 4:11). Allah ne kadai ya cancanci ya sami sujadarmu, da dauakaka, da kuma yabo (Nehemiya 9:6; Wahayin Yahaya 15:4).
English
Ko yin sujada ga tsarkaka / Maryamu daga Littafi Mai Tsarki ne?