Tambaya
Me ake nufi da sujada ga Maryamu (Mariolatry)?
Amsa
Mariolatry na nufin “wuce gona da iri na girmamawa ko yi wa Maryamu uwar Yesu sujada.”kalmar tana nufin “sujada ga Maryamu”. Sauran ikilisiyoyi suna kalubalantar Katolika kan “yi wa Maryamu sujada” amma Katolika sun karyata haka, sun nace da cewa suna girmama Maryamu ne amma ba sa yi mata sujada. Koyarwar Katolika da aka yarda da ita ita ce Allah ne kadai ya cancanci “dauakaka”, abin da ake kira sujada ga Allah kadai (latria); duk da haka, tsarkaka sun cancanci ta su karamar daukaka da ake kira “girmamawa” ko girmama tsarkaka (dulia). Tsarin Katolika ya cigaba da cewa Allah ya daukaka budurwa Maryamu fiye da sauran tsarkaka, domin haka za ta karbi girmamawa mafi yawa (dulia), da ake kira girmamawar da tafi ta tarkaka amma ba ta kai ta Allah ba (hyperdulia). Amma, Katolika sun sa lura da suka ce, ba ta kai ta Allah ba hyperdulia tana kasa da ta Allah latria. Katolika sun ce, tun da ba su ba Maryamu daukakar da Allah kadai ne za a ba ba, yin sujada ga Maryamu (Mariolatry) ba laifi ba ne. Tsofaffin Ikilisiyi na gabashin duniya ma suna girmama Maryamu a matsayin mafi tsarki cikin tsarkaka, suna kiranta “Budurwa mai Tsarki Maryamu”, suna raira mata wakoki, suna yin addu’a gare ta, suna sumbatar hoton siffarta.
A masayin nau’I na bautar gumaka, sujada ga Maryamu zunubi ne. Littafi Mai Tsarki ya lissafta bautar gumaka da sauran zunubai irin su, sihiri, da kishi, da tsafi, da fasikanci, da kuma gaba, wadannan ayyukan halin mutumtaka ne (Galatiyawa 5:20). Bautar gumaka kowane abu ne wanda ya maye gurbin Allah daya na gaskiya, ko kuma abin da aka ba daraja daya da Allah. An hana bautar gumaka a Tsohon Alkawari (Fitawa 20:3–4). An gargadi Isira’ilawa cewa “Gama Ubangiji Allahnku wuta ne mai cinyewa, shi kuma mai kishi ne” (Maimaitawar Shari’a 4:24).
Mariolatry ya bayyana uwar Yesu a matsayin abar dogara, da girmama wa, da kuma a bar bautawa. Akwai gargadi da yawa a cikin Littafi Mai Tsarki akan sujada ga wani ban da Allah. Maryamu mace ce kamar kowacce. Ba ta da ikon hada mu da Allah, ta warkar da mu, ko ta ji addu’oinmu. Ko Katolika da sauran tsofaffin Ikilisiyoyi sun karfafa sujada ga Maryamu? Sun karya ta cewa suna yi; duk da haka, bambancin tsanin “daukaka” da “babban bangirma” yana da wuyar gane wa. Daukaka Maryamu da sunaye irin su Matsakaiciya, mai ceto, sanadin Cetonmu, Mai Tsarki Uwar Allah, Budurwa Mara aibi, da kuma Sarauniyar Sama ba zai taimaka ba amma zai kara karfafa sujada ga Maryamu (Mariolatry). Raira wakoki ga maryamu, yin addu’a zuwa tare ta, sumbatar hoton ta, yawo da hotunanta kan tituna, da kuma russunawa siffar ta yana nuna yawan girmamawa da ya kama da bautar gumaka kuma za a iya kiran shi sujada ga Maryamu.
English
Me ake nufi da sujada ga Maryamu (Mariolatry)?