Tambaya
Ko za a iya bada shaidar ambaliyar ruwan da aka ambata a cikin Farawa? Ko akwai wata shaida a Littafi Mai Tsarki akan rigyawa ta duniya?
Amsa
Ambaliyar ruwan da aka rubuta a cikin Farawa 6 ba za a iya ba da cikakken tabbaci akan ta ba, amma akwai wadatattar shaida da ta goyi bayan cewa ambaliyar ta taɓa kasancewa. Littafi Mai Tsarki ya gabatar da ambaliyar a matsayin wani ɓangaren tarihin farko naduniya, amma duk da haka akwai masu shakka da za su ƙi yarda da wannan shaidar.
Ɗaya daga cikin shaidar ambaliyar ta kwanakin Nuhu ita ce yawan labaran da aka samu game da ambaliyar ruwa bisa duniya da aka samu a ɓangarori daban-daban masu yawa. Masu ilimin yan Adam sun rubuto jerin ɗaruruwan labarai na tsofaffin ambaliya daga duka duniya. Dag tsohuwar Babila, yan ƙasar Amurka, yan asalin Australiya, Aztecs, Romawa, Helinawa, Chaina, Mayans, Inuits, da sauransu da yawa da suka rubutu labari akan rigyawa. Kuma, labaransu sun yi kama da labarin da aka bada a Farawa, harda wani alla da ya yi fushi da kuma mutanen da suka tsira a cikin kwale-kwale.
Ɓangare na biyu akan shaida game da ambaliya a Farawa 6 alama ce ta fili da aka samu a bisa duniya. A misali, kashi 75 cikin 100 na doron duniya suna ɗauke da dutse mai taushi—dutsen da ruwa ya ɗauko, wanda yake dargajewa cikin ruwa, ya kwaso shi ya kuma tara shi a wani wurin daban. Ana samun halittu a yawancin irin wannan ƙasa mai taushi. Sanannen abu ne a sami irin waɗannan halittu da yawa a bayan daki cikin tsummokara, da tarkace, da rubabbun gawawwakin halittu wadanda ke kawo dabbobi masu yawa da ake lalatarwa ta hanyar nuna karfi mai banmamaki.
A Bangare na uku akan shaida ta ambaliyar kwanakin Nuhu shi ne babban nisan da ke tsakanin duwatsu dabam dabam. Misali, kimiya sun gano quartzites wanda aka gano mile 300 daga asalin tushensu a Oregon, al’amarin da ya daina faruwa a yau. Wannan bazuwar ma’adanan ƙasa zai iya zama sakamakon abin da aka faɗi a Zabura 104:6–8—Ruwayen da suke a akan duwatsu da kuma gangarowarsu a guje cikin kwarurruka.
Ɓangare na huɗu akan jerin shaida ta ambaliyar ita ce ganin halittun ruwa da yawa matattu akan kowanne dutse mai tsayi a duniya, har da Himalayas. Me ya kawo wannan al’amari? Ambaliyar ruwan gama duniya bisa da ya lullube duwatsu mafiya tsayi ta ya ya za ka bayyana shi. Farawa 7:18–19 ta bayyana cewa “Ruwa ya bunƙasa ya ƙaru ƙwarai bisa duniya, jirgin kuwa ya yi ta yawo bisa fuskar ruwaye. Ruwa kuwa ya bunkasa ainun a bisa duniya, har ya rufe kawunan dukan duwatsu masu tsayi da yake ƙarƙashin sammai duka.” Masana kimiya har yanzu ba su samar da isasshiyar shaida ta matattun halittun masu yawa ba.
Littafi Mai Tsarki ma kansa yana nan a matsayin ƙarin taimako. Sau da yawa, an tabbatar da tarihin Littafi Mai Tsarki ta hanyoyi da yawa. Idan Littafi Mai Tsarki daidai ne a ɓangarori da yawa na tarihi, me zai sa ayi gardama akan sahidarsa na ambaliya ta gama-duniya ya? Yana ɗaukar shaida daga labarai da yawa na ambaliyar ruwa ta gama-duniya, halittu da yawa, da kuma sauran halittu na ruwa masu kara, Labarin da Littafi Mai Tsarki ya bada isasshen haske akan abin da ya faru a lokacin Nuhu.
English
Ko za a iya bada shaidar ambaliyar ruwan da aka ambata a cikin Farawa? Ko akwai wata shaida a Littafi Mai Tsarki akan rigyawa ta duniya?