Tambaya
Me Littafi Mai Tsarki ya ce game da sake haihuwar mutum bayan ya mutu (reincarnation)?
Amsa
Maganar sake haihuwa bayan mutuwa ba ta da wani tushe a Littafi Mai Tsarki, wanda ya gaya mana a fili cewa zamu mutu sau daya bayan nan sai shari’a (Ibraniyawa 9:27). Littafi Mai Tsarki bai fadi wasu mutane da suka sake samun dama ta biyu ta yin rayuwa ba ko su dawo a matsayin wasu mutane ko dabbobi. Yesu ya ce da barawon akan gicciye, "Yau ma za ka kasance tare da ni a Firdausi" (Luka 23:43),ba "Za ka sake samun dama ka yi rayuwa a duniya ba." Matiyu 25:46 ta gaya mana cewa za su shiga rai madawwami sannan marasa ba da gaskiya kuma madawwamiyar azaba. Sake haihuwa bayan mutuwa sanannen abu ne da wasu suka yi imani na dubban shekaru, amma Kirista basu taba amincewa da shi ba ko masu addinin Yahudanci saboda ya na sabani da Littafi Mai Tsarki.
Nassi daya da wasu suke ganin shi a matsayin sake haihuwa bayan mutuwa shi ne Matiyu 17:10-12 wadda ta hada Yahaya Maibaftisma da Iliya. Duk da haka, wannan nassin bai ce Yahaya Maibaftisma Iliya ne ya sake dawowa ba amma ana nufin zai cika anabcin zuwan Iliya idan mutane suka gaskata da maganarsa suka yarda da Yesu a matsayin Mai Ceto (Matiyu 17:12). Sai mutane musamman suka tambayi Yahaya Maibaftisma ko shi ne Iliya, kuma ya ce, “A’a, ba Ni ba ne” (Yahaya 1:21).
Yin imani da sake haihuwa bayan mutuwa tsohon abun bauta ne wanda yawacin addinan gargajiya na Indiya suka gaskata da shi, irin su Hindu, Sikhism, da Jainism. Yawan cin marasa addini suma sun gaskata da sake haihuwa bayan mutum ya mutu, tare da masu aiki da ruhohi. Ga Kirista, duk da haka, ba wata shakka: sake haihuwa bayan mutuwa ba shi a Littafi Mai Tsarki kuma dole a ki shi a matsayin karya.
English
Me Littafi Mai Tsarki ya ce game da sake haihuwar mutum bayan ya mutu (reincarnation)?