Tambaya
Ko yin amfani da hotuna da siffofi a addinance bautar gumaka ne? Me ake nufi da siffa?
Amsa
Zahirin magan ita ce, hotuna da siffofi na addini zanen hotuna ne na wadansu mahimman mutane a addini, ta wurin amfani da alamomi. A addinin kiristanci, hotuna da siffofi sun nuna wadansu mutane kamarsu Kiristi, da Maryamu, ko kuma tsarkaka. Siffa hoto ne, da yawanci ake yi a jikin katako a yi masa kala, da za a girmama a matsayin wani abu mai tsarki. Siffa za ta iya zama zane-zane, ko wani hoto. Duk da cewa mutanen da suke amfani da siffofi a sujadarsu za su ce ba bautar gumaka suke ba, amma zai yi wuya a gane yadda “girmama” wani abu a matsayin “ mai tsarki” ya sha bamban da bautar gumaka.
Duk da Katolika suna girmama hotuna na addini, an fi samun hotuna da siffofi a kasashen yammaci ko kuma tsohuwar Ikilisiya, wadda take koyar da cewa amfani da siffofi da hotuna lokacin addu’a yana taimakon mai yin sujadar ya san Allah, ya kuma kasance tare da tsarkaka, ya kuma yi girma cikin ya’yan Ruhu. Sa’ad da tsohon Kirista ya shiga cikin Ikilisiyarsa, yakan kunna kandir, ya yi alamar gicciye, sa’annan ya sumbaci hotunan Kiristi, Theotokos (Maryamu), da kuma tsarkaka. Cikin Ikilisiyar za a sa hotuna na sauran “tsarkaka” kamar yadda suke kira.
Kirista na da suna da hotuna a gida, kuma wurin da ake ajiye hotunan shi ne wurin da iyalin suke yin addu’oi. Hotuna ana dubansu a matsayin misali na jikin Kiristi, wanda ya bar ruhunsa duniya. Wadanda suka mika kai sun kuma gaskata cewa hotunan kamar wata kofa ce zuwa sama, kuma ibadarsu za ta tafi kai tsaye zuwa sama, inda mutumin da aka yi hotonsa zai karba. Wadansu ma suna cewa siffofi da hotuna suna aikata al’ajabi.
John Calvin da sauran yan kowace dariku ba sa amfani da siffofi da hotuna; sun bukaci cire siffofi da hotuna daga Ikilisiya da gida je. Bisa ga masu sake tsarawa (Reformers), girmama siffofi da hotuna da sauran zane-zane na addini bautar gumaka ce, kuma suna da gaskiya. Duk wata sunbata, ko russunawa, ko yin addu’a ga siffa da hoto bautar gumaka ne. membobi na tsohuwar Ikilisiya sun nace cewa su ba bauta wa wannan kala da ita ce suke yi ba, amma sun ce suna ba da girma, da daukaka, da kuma mika kai ga tsarkaka ne da kuma siffa da hotunan Maryamu. Suna addu’a zuwa ga maza da mata; suna karbar ikon na ruhu wanda siffofin ba su da shi.
Wannan ba shi cikin Littafi Mai Tsarki.
Ba wani abu mara kyau ga kirkira ko jin dadin hotuna na addini, ko kallon wani abu da yake cikin Littafi Mai Tsarki kana sha’awa wannan ba zai zama bautar gumaka ba. kasancewar kana da hoton Yesu ko na mala’iku a gidan ka ba lallai ya zama bautar gumaka ba, idan za ka dunga ganinsu a matsayin zane-zane ne kawai, ko kuma ka dinga ganinsu a matsayin misalai na tarihin addini. Amma amfani da su domin yin sujadarka ko kallonsu a matsayin “kofa ta zuwa sama” zahiri wannan bautar gumaka ce.
Littafi Mai Tsarki ya hana bautar gumaka (Littafin Firistoci 26:1; Maimaitawar Shari‘a 5:9). Allah ne kadai za a russunawa a yi masa sujada. Siffofi ba matsakaita ba ne a wurin kursiyin alheri, ba kuma tsarkakan da suke wakilta ba ne. Mutanen da suke a samaniya ba su da ikon jin rokonmu ko amsa mana rokonmu.
Yesu Kiristi ne kadai da kuma Ruhu Mai Tsarki za su iya roka mana a wurin Uba (Romawa 8:26–27, 34).
Mu yi nesa da duk wani abu da zai iya kaimu ga bautar gumaka.
English
Ko yin amfani da hotuna da siffofi a addinance bautar gumaka ne? Me ake nufi da siffa?