Tambaya
Ko za a iya haihuwar mutum a matsayin dan Ludu?
Amsa
A 1996, An wallafa, wata jarida ta ludu da madugo, ta tambayi masu karatu me suka gaskata cewa zai iya zama da mahimmanci ga fadadar ludu da madigo idan ilimin kimiya suka gano cewa akwai kwayar halitta a cikin luwadi. Wajen kaso 61 na masu karanta jaridar suka ce irin wannan binkice na kimiya zai kara haifar da ludu da madigo ya kuma sa a fara kallon luwadi ta fuska mai kayau. Misali, idan aka haifi mutum a ludu, za a iya haifar mutum da idanu masu launin kasa-kasa (brown), al’umma tagari ba za ta shari’anta shi kan cewa ba haka idanun mutane suke ba ko kuma ba daidai bane. Kamar haka, da masu ruwa da tsaki na ludu za su karfafa abin su ce ai luwadi ma gado ne kuma ba zai canzu ba, kuma masu bincike za su natsu su samo hujjoji na kimiya da zasu goyi bayan wannan Maganar. Amma kash ga masu luwadi, binciken a kan wanna batu ya kasa samo wata shaida da ke nuna akwai kwayar halitta a luwadi.
Rudanin ya fara ne da aikin Simon LeVay, M.D. In 1991, LeVay ya gwada kwakwalwar matattu guda 41 ya kuma san bambancin tsakanin masu luwadi da kuma masu yi da jinsin da ba nasu ba. hypothalamus, wani fanni ne da yake kula da al’amuran jima’I, tafi kankanta ga maza masu luwadi fiye da jima’I tsakanin namiji da mace. . Dr. LeVay ya gaskata da cewa bambance-bambancen suna tabbatar da tushen ilimin halitta kan luwadi, amma sun kasa duba dalilai masu yawa, ban da kwayoyin halitta, cewa kwakwalwar akwai bambanci. Na farko, dukan mutum 19 yan luwadi sun mutu ne saboda KANJAMAU, cuta ce mai karya garkuwar jiki. Zai iya yiwuwa cutar ta rushe hypothalamus. Na biyu, yan kimiya wadanda suke karatu kan yanayin halittar kwakwalwa (brain biochemistry) sun san cewa yadda mutum yake tunani yana shafar yadda kwakwalwarsa ke aiki; musamman, yana shafar garkuwar da ke sa hutun kwakwalwa da kuma yadda wasu bangarori suke girma suke kuma canza wa. Ko bambancin tsarin kwakwalwa ya fara daga bambancin a tunani tsakanin yan luwadi da kuma masu jima’I da dayan jinsin, maimakon tare da kwayoyin halitta? Na uku, ba wata shaida da ta hada girman hypothalamus luwadi, a matsayin amfani ko cutarwa.
A 1993, Dr. Dean Hamer, mai fafutikar kare ludu, ya fadi wani abu mai ban mamaki a cikin bincikensa cewa za a iya samun kwayar halitta a luwadi. Abokan bincikensa suka cigaba da bincike mai yawa akan mahadin kwayoyin halitta, inda iyalan da ke da yan luwadi da dama suka fara yin nazarin kwayoyin halitta domin sanin ko za a iya samun kwayar halitta daban daban a cikin iyalin da kuma idan bambancin ya danganci wadanda suke yin luwadi. Ko da yake samfarin binciken Hamer's bai yi zurfi ba, ya sami alaka mai mahimmanci tsakanin luwadi da alama a kan mahaifar Uwa, (maternal X chromosome, Xq28). Karin bincike da samfari mafi girma ya ba da sakamako mai rudani a wurin alakar Xq28. Yana da mahimmanci a san cewa abin da Hamer’s ya gano ba a tabbatar da shi ba; a zahirin gaskiya ma, sauran kungiyoyi bincike basu amince da aiki Hamer’s ba sun bayyana aikinsa a matsayin wanda bai yi dai-dai ba kuma yaudara ce.
Idan akwai wasu kwayoyin haitta a cikin yan luwadi, ma’amularsu bata tabbatar da cewa akwai wata hanya da kwayoyin halittar za su hadu ba. misali, idan kayi bincike cikin masu wasan motsa jiki zai iya nuna maka cewa da yawa daga cikin taurarin sun hada wasu jerin kwayoyin halitta domin karin kuzari, kwarewa da karfi sun tabbatar da cewa kasancewa cikin kwararru a wasanni abu ne na gado. Duk da haka, ba wani jerin kwayoyin halitta da zai nuna abin da mutum zai zaba da kuma abin da ya shafi abubuwan da ke kewaye da shi. mutane wadanda suke da kwayoyin halitta na wasan motsa jiki kila zai iya zamar masu jiki su kasance cikin wasu manya-manyan wasanni ko a karfafasu su yi wasanni. Duk da harkar wasanni ta kun shi abubuwan sanannu, zama kwararren dan motsa jiki ba abu bane na gado. Yanayin al’adar inda mutum ya girma da kuma zabin da ya yi shi ke sa ya dauki hanyar abin da yake so ya zama.
Akwai masu bincike da yawa da suka dubi yanayin muhalli a matsayin babban abin da ke haddasa marmarin luwadi. Sun gaskata sasai da cewa dandanawar yara mara kyau a muhallin da ba kauna ko gidan da ba taimako suna daga cikin hanyoyin da abun yake farawa. Abu sananne ya kun shi rashin nuna kulawa ko rashin kasancewar Uba da kuma yawan tsaurara wa, yawan tausayawa ko uwa mai cika nuna kulawa. Lokuta da yawa, ana samun rahotannin cin zarafi ta jiki, ko ta jima’I, ko kuma ta motsin zuciya. Rashin samun kyakkyawar bambancewa ta jinsi yana ba da guduwa wajen cigaban luwadi. Wannan yana farawa ne daga shekara biyu zuwa hudu. A wanna lokaci, yara suna barin hannun iyayensu mata domin samun sabo da iyayensu na jinsi daya. Ga maza, dangantaka tsakanin yaro da Ubansa ita ce hanya ta farko ta habaka amincewa da asalin jinsin shi. Yayin da Uba da da suke zaune tare, Uban yana nuna darajarsa da kuma kaunarsa a wurin yaron yana kuma da sa wa yaron tunanin zama namiji. Yaron zai fara yin tunani irin na jinsin shi ta wurin fahimtar kan shi cikin dangankata da Ubansa. A ka zalika, uwa wadda bata kusa, ko mai zagi, ko kuma wadda ba ta tare da ya ko kuma uwa wadda yarta take kallonta a matsayin rarrauna (irin idan Uba yana cin zarafin Uwa) wannan zai iya shafar yar wajen yarda da amincewa ta ta zama mace.
Kasancewa cikin tsara ta jinsi daya abokai ma suna taka rawa wajen fadada fahimtar jinsi. Bayan kasancewa da yin cudanya tare da abokai na jinsi guda, yara sukan shiga balaga su fara mai da hankali kan wani jinsin. Sa’ad da aka bata wannan tsari da aka halicce su da shi, yaron zai koma ya kaunaci ya kuma sha’awaci wadanda suke jinsinsa. Sa’ad da ya’ya masu irin wannan halayya suka fuskanci kiyayya daga iyayen da suke jinsi daya, sukan ware su koma wa dayan jinsin iyayen. Sai su fara sabawa da yanayin rayuwar jinsin da ba nasu ba. duk da haka, a kowane lokaci akwai marmari na haduwa da iyayen da suke jinsi daya, kauna da sha’awa daga jinsi daya. Wadannan yara sun yarda cewa haka aka haifesu, da sha’awa da kaunar da kuma zama tare da iyayen da suke jinsi daya ita tsawon lokacin da za su iya tunawa. Halin luwadi ya fara ne daga sha’awa ta kauna, ba sha’awa ta jima’I ba. wannan yana nuna bukata ta kauna wadda ba ta jima’I ba, bukatar kauna mai sosa zuciya ta zama jima’I na farkon balaga.
Masu bincke da dama sun karkare cewa wayar da kai kan jima’I yana da wuya, al’amura da yawa na batun halitta, zamantakewa da yanayin tunani suka hadu suke taka rawa wajen yanayin jima’in mutum. Bisa ga Julie Harren, Ph.D., hanyar wannan cudanya tsakanin abubuwa za a iya sake bayyana ta da wadannan abubuwa:
--kwayoyin halitta +sake tunani na kwakwalwa +yanayin wurin da aka haife ka = yanayi na zafi.
--Iyaye + Abokai na tsara + Dandanawa = Muhalli.
--Hali + Muhalli = Wayar da kai kan Luwadi.
Abin da babu a cikin wadannan abubuwa sune kasancewar rai, zabin mutum, da kuma jarabtar Iblisl (duba Yakubu 1:14).
Ko da yake zai iya kasancewa da sauki, bisa ga tunani, ga mai luwadi ya yarda da cewa luwadi ba haihuwar mutum ake da shi ba, hujjojin binciken kimiya da a ka tara sun nuna akasin haka. Luwadi ka iya kasancewa kwayar halitta, amma zabin mutum ma na iya sa shi. daukar abu cikin jinni ba matsawa bane. A karshe yanayin yin jima’I ba cikin mahaifa bane. Ga wadanda suke cikin bakin cikin kasancewa cikin rayuwa ta luwadi, wannan bayani na gaskiya yana baku bege da canzawa. Kwarewar ma’aikatan lafiya ta nuna cewa, tare da taimako, wasu ‘yan luwadi na iya canzawa su koyi maida martani da kuma hanyoyin kare kai ga dandanawar mara dadi da suka yi tun da farko.
A 1 Korantiyawa 6:9-10, zunubin ludu da madigo an fado shi a kusa da na sata. Kamar yadda ba wata kwayar halitta da take sa sata, haka ba wata kwayar halitta da take sa Luwadi. Muhalli, ko kuma al’ada, amma zabi zai iya maida mutum barawo, kuma shi yake sa mutum ya zama dan Ludu da madigo.
Kiristi ya mutu domin ‘yan luwadi. Allah yana kaunar mutane masu irin hali na jima’I, kamar yadda yake kaunar dukkan masu zunubi. Littafi Mai Tsarki ya ce, “amma kuwa Allah ya tabbatar da kaunar da yake yi mana, wato tun muna masu zunubi Almasihu ya mutu dominmu.” (Romawa 5:8). Yesu Kiristi "Shi kansa kuwa shi ne hadayar sulhu saboda gafarar zunubanmu, ba kuwa namu kadai ba, har ma na duniya duka." (1 Yahaya 2:2).
Bisharar Kiristi "ita ce ikon Allah mai kai kowane mai ba da gaskiya ga samun ceto" (Romawa 1:16). A wurin Kiristi ne kadai muke da cikakkar hanya ta warkarwa, da maidowa, da gafartawa, da kuma ta’azantarwa. Shi ne hanya wadda za mu dandana tabbatarwa, da kauna mara iyaka, da daraja, da kuma amincewar Ubanmu na sama.
English
Ko za a iya haihuwar mutum a matsayin dan Ludu?