settings icon
share icon
Tambaya

Me zai sa in gaskata da tashin Kristi daga matattu?

Amsa


Abu ne tabbatacce cewa an kashe Yesu Kiristi a kan idon jama’a a Yahudiya a ƙarni na 1st A.D., ƙarƙashin Buntus Bilatus, ta hanyar gicciyewa, bisa ga umarnin majalissar Yahudawa. Tarihin waɗanda ba Kristoci ba na Flavius Josephus, da Cornelius Tacitus, da Lucian of Samosata, da kuma Maimonides har ma da majalissar Yahudawa sun tabbatar da labarin Kristoci na farko waɗanda shaidu ne na gani da ido na wannan mahimmin tarihi na mutuwar Yesu Kristi.

Game da tashinsa daga matattu kuma, akwai jerin shaidu masu yawa waɗanda suka goyi bayan wannan magana. Marigayi fitaccen mai hazaka kuma shugaba na tabbatar da kyakkyawan shugabanci na ƙasa da ƙasa Sir Lionel Luckhoo (na Guinnesss Book of World Records ta wurin babban ƙoƙarinsa na wanke mutane daga hukuncin kisa sau 245 a jere) ya zama misali na ƙara ƙaunar Krista da kuma ƙara masu ƙarfi a cikin al’amarin tashi daga matattu lokacin da ya rubuta cewa, “Na kwashe fiye da shekaru 42 a matsayin Lauya mai yaƙi da kisan kai, na bayyana a ɓangarori da dama na duniya kuma har yanzu cikin yin haka nake. Na sami damar yin nasarori da yawa a kan shari’a kuma ina faɗi da babbar murya cewa shaidar tashin Yesu Kristi daga matattu abin mamaki ne wanda ya zama dole a amince ta wurin hujjoji domin ba wani abu na shakka a ciki. ”

Martanin da al’ummar duniya suka bayar game da wannan shaida bisa hasashe ya zama abin rashin jin daɗi bisa ga miƙa kansu ga yadda aka fasara yanayin yadda abubuwa suke kasancewa haka kawai. Ga waɗanda basu fahimci wannan ba, shi yanayi na bayyana abubuwa ƙoƙarin mutum ne na yin bayanin komai bisa ga yadda suke faruwa kuma ko da yaushe haka yake faruwa. Idan abinda ake tunani na tarihi ya saɓa bayanin halita (misali., mu’ujizar tashin matattu), su masana na duniya suna duban wannan abun da shakka mai tsanani, komai shaidar da yake da ita, komai yadda abun yake a bayya ne.

A ganin mu, irin wannan yarda da al’ada ba tare da la’akari da hujjoji ko shaida ta saɓanin haka ba zai kasance da daɗi ga wanda bai da sonkai ba, don haka sai an yi bincike a kan shaidar. Mun amince da Dr. Wernher von Braun da kuma wasu saura da yawa waɗanda suka gaskata da cewa tursasa abin da Masana suka faɗa akan shaida yana hana mahimmancin abu. Ko kuma a kalmomin Dr. von Braun, “cewa tilastawa a amince da abu ɗaya da aka yarda da shi…zai sa kimiya kanta ta zama ba ta da mahimanci.”

Tun da an ce haka, bari mu duba jerin shaida ta tashin Kristi daga matattu.

Shaida ta farko ta tashin Kristi daga matattu

Da farko dai, mun bayyana tabbatacciyar shaida ta masu gani da ido. Masu kare addinin Kristanci na farko sun lissafta ɗaruruwan shaidu na gani da ido, waɗansu sun rubuta tasu ɗanɗanarwar. Da yawan shaidun nan na gani da ido sun jure shan doguwar azabtarwa da mutuwa a maimakon su ƙi bayyana shaidarsu. Wannan ya tabbatar da cewa gaskiya suke faɗi, sun kawar da yaudara daga ɓangarensu. Bisa ga abin da aka rubuta a tarihi (Littafin Ayyukan manzanni 4:1-17; wasikun Pliny zuwa ga Trajan X, 97, da sauransu) da yawan Kristoci za su iya yanke wahalar da suke sha ta wurin musunta bangaskiyarsu kawai. Maimakon haka, sai ya zama sun zaɓi su jure wahala su kuma yaɗa tashin Kristi daga matattu.

Haka ya zama, yayin da azabtarwar mai tsanani ce, ba ta inganta abin da ka gaskata kamar yadda za ta inganta wanda ya gaskata (ta wurin nuna gaskiyarsa ta hanya mai tsada). Abin da ya sa Krista na farko waɗanda aka kashe suka yi fice shi ne sun san cewa abin da suke faɗi gaskiya ne ko karya ne. Ko dai sun ga Yesu lokacin da yake raye da kuma bayan mutuwarsa ko basu gani ba. wannan babban abu ne. Idan da duk ƙarya ne, me yasa wasu za su tabbatar da haka a cikin yanayin da suke ciki? Me zai sa suna sane su manne wa irin wannan ƙaryar mara riba a cikin tsanani, da kurkuku, da azabtarwa, da kuma mutuwa?

Yayin da masu jihadi na 11, ga watan Satumba 2001, sun yarda da abin da suka gaskata (kamar yadda shaida ta ba da ta wurin yarda su mutu akan haka), ba su iya sani ba kuma ba za su iya sanin ko gaskiya bane. Amma sun sa bangaskiyarsu ga al’adun da kakannin-kakanninsu suka bar masu. Idan ka duba da kyau, Kristoci da aka kashe ta wajen azabtarwa su ne na farko. Ko dai sun ga abin da suke cewa sun gani ko ba su gani ba.

A cikin misalai na masu bayyanawa ta gani da ido akwai Manzanni. Dukan su sun faɗa cikin wani canji wanda ba shi boyuwa bayan bayyanar da Kristi ya yi garesu da ya tashi daga matattu. Bayan an gicciye shi, dukansu suka ɓoye cikin tsoro domin rayukansu. Bayan tashinsa sai suka bi tituna, gaba gaɗi suka bayyana tashinsa duk da matsanacin tsanani. Me ya sa suka canza nan da nan? Ba kuɗi aka ba su ba. Manzannin sun sadaukar da duk abin da suke da shi domin su shaida tashinsa, har da rayuwarsu.

Shaida ta Biyu ta tashin Kiristi daga matattu

Jerin shaida ta biyu ta maida hakali akan juyowar wasu manya-manyan abokan hamayya, waɗanda aka fi sani sune Bulus da Yakubu. Bulus ya kasance mai tsanantawa Ikilisiya ta farko. Bayan abin da ya bayyana a matsayin saduwa da Kristi wanda ya tashi daga matattu, Bulus ya sami canzawa ta gaggawa mai ban mamaki daga babban mai tsanantawa Ikilisiya zuwa ɗaya daga cikin mafi kwarewa da jajircewa wajen kare ta. kamar Kristoci da yawa na farko, Bulus ya sha wahalar talauci, tsanani, duka, zaman kurkuku, da kisa domin miƙa kai da jajircewarsa ga tashin Yesu daga matattu.

Yakubu ma ya yi hamayya, koda yake ba kamar yadda Bulus ya yi ba. Ta dalilin saduwarsa da Kristi bayan tashi daga matattu ya zama nagartaccen mai bi, shugaba na Ikilisiyar Urushalima. Har yanzu muna da abin da masana suka yarda ta zama ɗaya daga cikin wasiƙunsa zuwa ga Ikilisiya ta farko. Kamar Bulus, Yakubu a cikin miƙa kai ya sha wahala ya kuma mutu saboda shaidarsa, wannan ya tabbatar da gaskiyar abinda ya gaskata (duba Littafin Ayyukan manzanni da kuma Josephus’ mai binciken tarihi na Yahudawa XX, ix, 1).

Shaida ta Uku da ta Huɗu ta tashin Kristi daga matattu

Shaida ta uku da ta hudu ta maida hankali ga shaidar da maƙiya suka ba da akan kabarin da ba kowa da kuma gaskiyar cewa bangaskiya ga tashi daga matattu ta samo tushe ne daga Urshalima. An kashe Yesu a kan idon jama’a an kuma binne shi a Urshalima. Da ya zama da wahala bangaskiya ta sami tushe daga Urshalima yayin da jikinsa yake cikin kabari inda majalisar Yahudawa za su iya tono shi, su ajjiye shi a bainar jama’a, daga nan su ƙaryata shi. maimakon haka, majalisar Yahudawa sun zargi almajiransa da sace gangar jikinSa, wajen ƙoƙarin yin bayanin ɓacewarsa (don haka kabarin ba kowa). Ta yaya zamu iya yin bayanin gaskiyar kabarin da ba kowa? A nan ga misalai mafi sauƙi uku:

Na farko, almajiran sun sace gangar jikin, idan da haka ne, da sun san da cewa tashinsa daga matattu ƙarya ne. Da ba su so su sha wahala su kuma mutu saboda haka ba. (dubi shaida ta farko game da bayyana gaskiya ta gani da ido.) Dukan shaidun na gani da ido ai da sun san cewa basu ga Kristi ba saboda haka ƙarya suke. Kewaye da masu maƙarƙashiya mai yawa, tabbas da sai wani ya bada labarin, ko ba don ya kawo ƙarshen wahalar da yake sha ba ai ya kawo ƙarshen wahalar iyalinsa da abokansa. Tsarar Kristoci na farko sun sha azaba matuƙa, musamman bayan tashin hankalin da aka yi a Roma a A.D.64 (wutar da Nero ya umarta domin ya sami damar faɗaɗa masarautarsa, wadda ya ɗorawa Krista wajen ƙoƙarin wanke kansa). Yayin da masanin tarihi na Romawa Cornelius Tacitus ya ba da labarinsa (annals) a mulkin Roma (aka wallafa tsara guda bayan wutar):

“Nero ya ɗora masu laifin ya kuma sa azabtarwa mai tsanani akan jinsin wasu mutane da ake kira Krista da aka ƙi domin suna yin abin da ake ƙyama, Christus, wanda daga gare shi sunan ya samo asali, ya sha hukunci mai tsanani a zamanin Tibariyas, a hannun ɗaya daga cikin masu mulkinmu, Bintus Bilatus, wanda yafi dukan saura mugunta ba a Yahudiya kawai ba, amma har a Roma, in da abubuwa marasa kyau da abun kunya daga kowane ɓangare na duniya suke samo asali suka zama sanannu. Da farko sai aka kama waɗanda suka amsa laifinsu; daga nan, bisa bayanansu, an hukunta mutane da yawa, ba bisa yawan laifi na hallaka birnin ba, bisa ƙin jini na Dan adam. An ƙara da kowace irin ba’a akan mutuwarsu. An rufe su da fatar namomin jeji, karnuka sukai ta kyakkece su suka halaka, ko kuma a buga masu ƙusa kan gicciye, ko kuma a sa su cikin wuta an ƙone su, domin su haskaka cikin dare, lokacin da rana ta fadi.” (Annals, XV, 44)

Nero yana haskaka lambunsa na shagulgula da Kristocin da ake ƙonewa da rai. Tabbas da wani ya musanta gaskiya a cikin wannan babbar azabtarwa. Gaskiyar it ace, duk da bamu da labarin wani cikin Krista na fari da ya yi musun sanin bangaskiyarsa domin ya kawo ƙarshen shan wahalarsa, maimakon haka, muna da labarai da yawa da ya bayyana bayan tashinsa daga matattu da kuma ɗaruruwan shaidu na gani da ido da suke a shirye su mutu domin haka.

Idan almajiran basu saci jikin ba, ta yaya zamu yi bayanin kabarin da ba kowa? Wasu sun ce Kristi ya yi ƙarya ne da mutuwarsa daga baya sai ya fice daga kabarin. Wannan ƙarya ce zahiri. Bisa ga shaidu na gani da ido, an bugi Kiristi, an azabtar da Shi, an yayyanke Shi, an kuma ji masa raunika. Ya sha wahala ta cikin jiki, an zubar da jininsa sosai, rashin iskar shaka, da caka masa mashi a zuciyarsa. Ba wani dalili da zai sa a gaskata cewa Yesu Kristi (ko wani mutum) zai iya shanye wannan wahalar, yayi ƙaryar cewa ya mutu, ya zauna a kabari na kwana uku ba tare da ma’aikatan lafiya, abinci ko ruwa ba, ya mirgine babban dutsen da aka rufe kabarinsa, ya tafi ba a gansa ba (ba tare da barin jini ba), ya kuma sa ɗaruruwan shaidu na gani da ido su yarda da cewa ya tashi daga matattu kuma cikin ƙoshin lafiya, ya kuma bace ba tare da an gano shi ba. irin wannan bayani ai abin dariya ne.

Shaida ta Biyar ta tashin Kiristi daga matattu

A ƙarshe, shaida ta biyar tana maida hankali kan banbance shaidu na gani da ido. A cikin dukan manyan labarai na tashi daga matattu, an bayyana mata a matsayin shaidu na gani da ido na farko. Wannan sabon abu ne tun da yake a al’adun Yahudawa da Romawa ba’a girmama mata. Ana duban shaidarsu a matsayin shaida wadda ba cikakka ba kuma abar watsi. Ganin haka, shi yasa akwai yiwuwar duk wani mayaudarin mai mulki a ƙarni na 1 a Yahuza sai ya zaɓi mace ta zama shaidarsa ta farko. Cikin dukan almajiran maza da suka ce sun ga tashin Yesu daga matattu, idan da dukansu ƙarya suke kuma tashi daga matattu yaudara ce, me yasa suka ɗauki abin da masu shaida mafi illa da kuma ruɗarwa suka samo?

Dr. William Lane Craig ya yi bayanai, “idan ka fahimci aikin mata a ƙarni na farko a al’ummar Yahudawa, abin ban mamaki shi ne wannan labari na kabarin da ba kowa zai zo daga baki mata a matsayin mutane na farko da suka ga kabarin da ba kowa. Mata suna cikin jinshi mafi ƙasƙanci a cikin al’umma a ƙarni na farko na Isira’ila. Akwai wata tsohuwar Magana da shugabannin Yahudawa ke faɗi da ke cewa, ‘Gara a ƙone kalmomi na doka da a ba mata su, kuma mai albarka ne wanda ya’yansa maza ne, amma kaiton wanda ya’yansa mata ne.’ ana wofintar da shaidar mata da har ba a barinsu su zama shaida a kotun Yahudawa. Ƙarin haske akan haka, ya zama abin a tuna ne ganin cewa mata ne manyan masu shaidar farko game da kabarin da ba kowa …dukan wani babban labari za a same shi wurin almajiransa maza a matsayin waɗanda suka gano kabarin-Bitrus ko Yahaya, alal misali. Ganin cewa mata sune shaida ta farko ga kabarin da ba kowa dole a bayyana gaskiya ko ana so ko ba a so sune suka fara ganin kabarin da ba kowa! Wannan shi ya nuna cewa marubutan bishara sun rubuta gaskiyar abin da ya faru, ko da abin kunyane. Wannan na nuna bayyana gaskiya akan shaida ta wannan al’adar fiye da ficcen da tayi a tarihinta." (Dr. William Lane Craig, quoted by Lee Strobel, The Case For Christ, Grand Rapids: Zondervan, 1998, p. 293)

A takaice

Waɗannan jerin shaidu: da abin da shaidu na gani da ido suka bayyana (da kuma al’amarin manzanni’ wannan na kira zuwa ga babbar canzawa), juyowa da kuma bayyana gaskiya da manyan abokan hamayya waɗanda a ƙarshe suka sha azaba har suka mutu da suka yi, gaskiyar kabarin da ba kowa, da kuma shaidar abokan gaba kan kabarin da ba kowa, ganin cewa dukan waɗannan abubuwa sun faru a Urshalima inda bagaskiya ta faro kuma ta cigaba, shaidar matan, da kuma mahimmancin wannan shaida bisa tarihi; dukan waɗannan sun ba da shaida ta tarihin tashi daga matattu. Muna ƙarfafa masu karatu su duba waɗannan shaidu. Wane zaɓi suke yi maka? Da shike mun gano su da kanmu, mun tabbatar da abin da Sir Lionel ya bayyana:

“Shaidun tashin Yesu daga matattu sun yi yawan da ya zama dole a yarda da shi domin bai ba da kofa domin shakka ba ko kaɗan.”

English



Koma zuwa shafin gida na Hausa

Me zai sa in gaskata da tashin Kristi daga matattu?
© Copyright Got Questions Ministries