settings icon
share icon
Tambaya

Me Littafi Mai Tsarki ya ce game da budurwa Maryamu?

Amsa


Maryamu uwar Yesu Allah ya bayyana ta a matsayin “zababbiya” (Luka 1:28). jimlar “zababbiya” ta samo asali ne daga kalmar Helinanci, wadda take nufin “alheri mai yawa”. Maryamu ta sami alherin Allah.

Alheri wani “tagomashi ne”, ma’ana wani abu da muka samu duk da bamu cancance shi ba. Maryamu tana bukatar alheri daga Allah kamar yadda sauranmu muke bukata. Ita kanta maryamu ta fahimci haka, kamar yadda ta fadi a Luka 1:47, “. . .Allah mai ceto na, da shi ruhuna yake ta farin ciki. . .”

Maryamu ta gane cewa tana bukatar Mai Ceto. Littafi Mai Tsarki ya ce Maryamu ba wata ba ce amma mutum ce kamar kowa wadda Allah ya za ba ya yi amfani da ita ta hanya mai ban mamaki. I, Maryamu mace ce mai aminci wadda kuma ta sami tagomashi (alheri) gun Allah (Luka 1:27-28). A lokaci guda kuma, Maryamu mutum ce mai zunubi wadda take bukatar Yesu Kiristi a matsayin Mai Ceton ta, kamar kowa (Mai Hadishi 7:20; Romawa 3:23; 6:23; 1 Yahaya 1:8).

Maryamu ba ta dauki ciki na jiki irin wanda mutane suke dauka ba. Littafi Mai Tsarki bai ce haihuwar Maryamu kamar sauran haihuwa ce da aka sani ta mutane ba. Maryamu budurwa ce sa’ad da ta haifi Yesu (Luka 1:34-38), amma maganar kasancewar budurcin Maryamu na din din din ba shi a Littafi Mai Tsarki. Matiyu 1:25, ana Magana ne akan Yusufu, an bayyana cewa, “Amma bai san ta ba, sai bayan da ta haifi Danta, ya kuma sa masa suna Yesu.”

kalmar “sai bayan da” tana bayyana cewa Yusufu da Maryamu ba su taba yin ma’amula ta jima’I ba sai bayan da aka haifi Yesu. Yusufu da Maryamu sun haifi ya’ya da yawa tare bayan haihuwar Yesu. Yesu yana da yan’uwa guda uku: Yakubu, da Yusufu , da Saminu, da kuma Yahuza (Matiyu 13:55). Yesu yana da yan uwa mata, duk da ba a ambaci sunansu ba (Matiyu 13:55-56). Allah ya albarkaci Maryamu ta wurin bata ya’ya da yawa, wanda a al’adarsu bayyananniyar alama ce ta albarkar Allah a kan mace.

Wani lokaci da Yesu yake Magana, wata mace a cikin taro jama’a ta daga murya ta ce, “Albarka ta tabbata ga wadda ta haife ka, wadda ka sha mamanta” (Luka 11:27). Ba wata babbar dama da ta fi wannan da Yesu zai bayyana cewa Maryamu ta cancan ci yabo da daukaka. Me ya ce? “maimakon haka, I, amma albarka ta fi tabbata ga wadanda suke jin maganar Allah, suke kuma kiyaye ta.” (Luka 11:28). Ga Yesu, biyayya ga Allah ta fi mahimmanci ne sa da zama matar da ta haifi Mai Ceto.

Yanzu a ina ne a Littafi Mai Tsarki Yesu, ko wani, ya ba da yabo, girma, ko daukaka ga Maryamu. Alisabatu yar uwar Maryamu ta ya bi Maryamu a Luka 1:42-44, amma yabon ta akan albarkar haihuwar Mai Ceto ne amma ba saboda wata daukaka ta Maryamu ba.

Maryamu tana nan a wurin gicciye sa’ad da Yesu ya mutu (Yahaya 19:25). Maryamu tana tare da manzanni a ranar fentikos (Ayyukan manzanni 1:14). Duk da haka, ba a kara ambatar Maryamu ba bayan Ayyukan manzanni sura 1. Manzannin basu ba Maryamu wani babban aiki ba. Mutuwar Maryamu ba labarin ta a cikin Littafi Mai Tsarki. Ba wani abu da aka ce game da hayewarta zuwa sama ko babban aikinta a can. A matsayin uwar Yesu a duniya, za a iya girmama Maryamu, amma bata cancanci sujada ko daukakarmu ba.

Ba inda Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa Maryamu za ta ji addu’oinmu ko za ta iya tsayawa tsakanin mu da Allah. Yesu shi kadai ne mai kai kukanmu da kuma matsakaicinmu a sama (1 Timoti 2:5). Idan aka yi mata sujada, da daukaka, ko addu’a, Maryamu za ta fadi abin da mala’iku suka fadi: “Yi sujada ga Allah!” (duba Wahayin Yahaya 19:10; 22:9.) Ita kanta Maryamu ta zama misali a gare mu, da ta mika sujadarta, da daukaka, da kuma yabo ga Allah kadai: “Zuciya ta na daukaka Shi, Ubangiji, Allah Mai Cetona, da shi ruhuna yake farin ciki, domin fa shi ya dubi kaskancin baiwa tasa. Ga shi jama’a ta dukan zamanai, za su ce mini mai albarka ce ke nan gaba. Domin fa shi da yake Mai iko, manyan al’amura ya yi mini sunansa labudda Mai tsarki ne” (Luka 1:46-49).

English



Koma zuwa shafin gida na Hausa

Me Littafi Mai Tsarki ya ce game da budurwa Maryamu?
© Copyright Got Questions Ministries