Tambaya
Ko budurcin Maryamu dukkan rayuwarta bisa ga Littafi Mai Tsarki ne?
Amsa
Abu ne da Ikilisiyar Katolika suka yarda da shi cewa Uwar Yesu Maryamu ta kasance da budurci tsawon rayuwar ta. ko wannan Magana bisa ga Littafi Mai Tsarki ne? Kafin mu duba wasu nassoshi, yana da mahimmanci ku fahimci dalilin da yasa Ikilisiyar Katolika ta gaskata da wannan Magana ta budurcin Maryamu dukkan Rayuwar ta. Ikilisiyar Katolika tana duban Maryamu a matsayin "Uwar Allah" da kuma "Sarauniyar Sama”. Katolika sun gaskata cewa Maryamu na da wani babban matsayi a Sama, da ke da kusanci da Yesu da kuma Allah Uba. Ba inda aka fadi wannan a Littafi Mai Tsarki. Bugu da kari, koda a ce ma ta mallaki wani babban matsayi, kasancewar ta taba yin jima’I ba zai hana ta samun wannan Matsayin ba. domin jima’I a cikin aure ba zunubi ba ne. Ba ta inda Maryamu za ta aibata kanta ta wurin yin jima’I tare da mijinta Yusufu. Dukan wannan Magana ta budurcin Maryamu dukkan rayuwar ta ba koyarwar Littafi Mai Tsarki ba ce, Maryamu a matsayin Sarauniyar Sama, wannan fahimta ce wadda ba ta Littafi Mai Tsarki ba game da jima’I .
To, me Littafi Mai Tsarki ya ce game da budurcin Maryamu dukkan rayuwar ta? in muka yi amfani da New American Bible, wanda fassarar Katolika ce, zamu ga cewa maganar budurcin Maryamu dukkan rayuwar ta ba a koyar da shi a Littafi Mai Tsarki ba. Matiyu 1:25 NAB ya gaya mana, "Amma bai san ta ba, har sai da ta haifi Danta, ya kuma sa masa suna Yesu." Shi, Yusufu, bai yi judanya ta jima’I da ita ba, Maryamu, HAR SAI bayan ta haifi danta, Yesu. Ma’anar wannan nassi a bayyane take sosai. Yusufu da Maryamu ba su ta ba yin jima’I ba har sai bayan da aka haifi Yesu. Matiyu 13:55-56 NAB ya bayyana, "Ashe wannan ba dan masassakin nan ba ne? Uwa tasa ba sunan ta Maryamu ba? ‘yan uwansa kuwa ba su ne Yakubu, da Yusufu, da Saminu da Yahuza ba? ‘yan uwansa mata ba duk tare da mu suke ba?" abin da Katolika suke cewa, shi ne, asalin kalmar ta Helinanci ta “yan uwa” a ayar za su iya zama dangi maza da mata, ba lallai yan uwansa na uwa daya uba daya ba. duk da haka, asalin ma’anar abin da ake so a fadi a bayyane ta ke, suna tunanin Yesu dan Yusufu ne, dan Maryamu, kuma dan uwan Yakubu, da Yusufu, da Saminu, da kuma Yahuza da yan uwan da ba a lissafta ba. Uban, da Uwa, da yan uwa . Abin mamaki ne ma’anar maganar ta fassara “yan uwa maza” da “yan uwa mata” a matsayin “dangi” da kuma Ambato Uwar da uba na Yesu.
Matiyu 12:46 NAB ya gaya mana, "Yana cikin Magana da taro, sai ga uwa tasa da yan uwansa suna tsaye a waje, suna nema su yi magana da shi." Mu kuma duba Markus 3:31-34; Luka 8:19-21; Yahaya 2:12; da kuma Ayyukan manzanni 1:14. Duka sun fadi uwar Yesu da yan uwansa. Idan da danginsa ne, ko ya’yan Yusufu daga aurensa na baya, me yasa a kowane lokaci ake maganarsu tare da Maryamu? Maganar budurcin Maryamu dukkan rayuwar ta ba za a iya fito da ita daga Littafi Mai Tsarki ba, tursasa ta aka yi cikin Littafi Mai Tsarki, sabanin abin da Littafi Mai Tsarki ya ce.
English
Ko budurcin Maryamu dukkan rayuwarta bisa ga Littafi Mai Tsarki ne?