Tambaya
Waɗanne abubuwa ne masu burgewa da aka gano cikin binciken kimiya na kayan tarihi na Littafi Mai Tsarki?
Amsa
Binciken tarihi na Littafi Mai Tsarki kimiya ce ta bincike da kuma maido da al’adun da suka wuce da za a iya tabbatar da su, ko a ƙalla a bada sabon haske akan, labarin Littafi Mai Tsarki. Binciken tarihi na Littafi Mai Tsarki ya ƙunshi bincike kan gine-gine, harshe, rubuce-rubuce, fasaha, kayan aiki, tukwane da kuma sauran abubuwa masu yawa da suka daɗe suka ɗauki dogon lokaci, na kusan sheka ɗari biyu, waɗanda suke nazari kan binciken tarihi na Littafi Mai Tsarki suna ta aiki a Gabas ta tsakiya wajen yunƙurinsu na maido da abin da ya gabata. Akwai dubban abubuwan da masu binciken tarihi suka gano da suka faɗaɗa binciken sosai, amma wasu sunfi wasu mahimmanci. Wasu daga cikin abubuwan da suka gano sune su Litattafan Tekun Gishiri, Rubutun Tel Dan , akwatin ƙasusuwa na Kayafa, gicciyayyen mutum, Layun Ketef Hinnom, Kasko mai ɗauke da rubutu game da gidan Allah, da kuma Rubutun Bilatus. Bari mu duba kowanne ɗayansu a taƙaice domn mu ga dalilin da yasa suke da mahimmanci.
Litattafan Tekun Gishiri: Ɗaya daga cikin mafi mahimmancin abubuwan da aka gano a fagen binciken tarihi na Littafi Mai Tsarki shi ne gano Litattafan Tekun Gishiri a 1947 a yankin Qumran Arewa ta Yammacin shore na Tekun Gishiri. Awai kimanin takardu 900 da kuma katse-katse da suka ƙunshi abin da aka gano. Litattafan sun kasance kafin A.D. 100 kuma sun haɗa da cikakken kwafi na littafin Ishaya. Mahimmancin abin da aka gano shi ne shekarun takardun da kuma abin ban mamaki na rashin bambance-bambancen da suka kasance mafi aminci irinsu Rubutun Masoretic, Codex Vaticanus da kuma Codex Sinaiticus. Mafi yawancin takardun (kusan kaso 99) kuskure ne na alamomin cikin rubutu ko kuma kurakuren rubutu. Abin mamaki shi ne, ba wasu takardu da suka canza ma’anar saƙon, basu da wani bambanci na tauhidi. Wannan ya bamu tabbacin cewa rubutun da muke da shi a Littafi Mai Tsarki a yau ɗaya yake da wanda Ikilisiya ta farko take da shi shekaru dubu biyu da suka wuce. Ba wasu matanai da za su iya kasancewa haka.
Rubutun Tel Dan: Wannan allon dutse na rubutu yana ɗauke da rubutu wanda shi ne na farko da yayi bayani akan daular Dauda wadda ba cikin Littafi Mai Tsarki take ba. Hazayel sarkin Aram ne ya kafa ta, wanda a yanzu Suriya ce. Rubutun ya bayyana nasarorin sojoji da suka yi dai-dai da labarin Littafi Mai Tsarki a 2 Tarihi 22. Anyi wannan rubutu tun ƙarni na 9 B.C., wannan ya bamu ranar da ta yi daidai da daular Dauda da kuma kasancewarta. Wannan shi ne kaɗai ƙarin bayanin da aka samu wanda ba a Littafi Mai Tsarki yake ba game da gidan Dauda ya zuwa yau.
Akwatin ƙasusuwa na Kayafa: Akwatin ƙasusuwa wani dutse ne ko akwati ne da ake binne ƙasusuwan matacce (akwatin gawa na da). Akwatin kasusuwa na kayafa na ɗauke da rubutu “Yeosef bar Qafa” an yi shi a lokaci haikali na biyu. Yeosef (Yusufu) ɗan Kayafa ne. wannan na nuna cewa akwai babban firist a lokacin Yesu kuma sunansa Kayafa. Kayafa shi ne firist din da ya jagoranci yiwa Yesu shaidar zur (Matiyu 26:57-67).
Gicciyayyen Mutum: Wannan shi ne cikakkaen kwarangwal na mutumin da aka gicciye a ƙarni na farko. Ƙasusuwan ƙafa na ɗauke da ƙusoshin gicciyewa. Akwai waɗanda suka yi gardamar cewa gicciyewar Kiristi yaudara ce saboda wannan ba shi bane babban hukunci a lokacin Kiristi. Waɗannan abubuwa da suka rage sun tabbatar da cewa ana gicciyewa kuma gicciyewar Yesu anyi ta yadda aka bayyana a Littafi Mai Tsarki.
Layun Ketef Hinnom: A shekarar 1979, an sami ƙananan litattafai biyu na azurfa waɗanda ake ratayawa a matsayin layu a cikin kabari a Ketef Hinnom, yana kallon kwarin Hinnom, inda aka saka tun wajen ƙarni na 7th B.C. Aikin warware naɗaɗɗun litattafan tare da samar da hanyar da za ta hana su wargajewa ya ɗauki shekaru uku. Duk da suke taƙaitattu, layukan suna ɗauke da rubutu mai matsayin rubutu mafi daɗewa daga cikin Littafi Mai Tsarki na Ibraniyanci. Bayan an warware litattafan, masu binciken kimiya na kayan tarihi na Littafi Mai Tsarki sun taras da rubuce rubuce biyu masu mahimmanci. Ɗaya daga ciki albarkar ce ta firist na haikali daga littafin Kidaya: “Ubangiji ya sa muku albarka ya kiyaye ku. Ubangiji ya sa fuskarsa ta haskaka ku, ya yi muku alheri. Ubangiji ya dube ku da idon rahama, ya ba ku salama” (Littafin Kidaya 6:24-26). Ɗayan kuma shi ne tetragrammaton YHWH, sunan Ubangiji, wanda daga shi muka samo na turanci Jehovah. Layun suna nan kafin Litattafan Tekun Gishiri da shekaru 500 kuma sune misali na sunan Ubangiji mafi daɗewa a rubuce.
Kasko mai ɗauke da rubutu game da gidan Allah: Kasko mai ɗauke da rubutu game da gidan Allah abu ne da masu ilimin kimiya kan kayan tarihi suka gano. An sami kasko mai ɗauke da rubutu game da gidan Allah a Arad, birnin mutanen Kan’ana a Nagef. An sami ɓalle-ɓallen Kasko fiye da 100 kuma an same su a farkon ƙarni na 6th B.C. Mahimmin abin shi ne suna Magana ne kan haikalin Urushalima da kuma sunayen mutanen da aka rubuta a cikin Littafi Mai Tsarki. Wannan ba taimakar a gane lokacin da haikali yake kawai ya yi ba. amma ya tabbatar da kasancewar wasu jerin mutane a Littafi Mai Tsarki.
Rubutun Bilatus: Wannan allon dutse an samo shi ne a Kaisariya a Bahar Rum. An samo allon a wani babban gini na wasan kwaikwayo a Kaisariya kuma yana ɗauke da rubutu mai ambatar sunan Buntus Bilatus mai mulkin Yahudiya, da kuma kayan wasa, wanda wani gini ne da aka yi don girmamawa ga sarki Tibariyas daga Bilatus. Akwai rubuce rubuce da dama domin a gurɓata labarin Littafi Mai Tsarki akan kasancewar Bilatus; wannan allon ya bayyana cewa daga “Buntus Bilatus ne, shugaban ƙasar Yahudiya” Ya kuma tabbatar da cewa ya yi rayuwa a lokacin Yesu, kamar yadda Littafi Mai tsarki ya faɗa.
Waɗannan abubuwa da aka gano suna kyau a sashin ilimi kuma suna ƙara tabbatar da sahihancin Littafi Mai Tsarki. Amma ga masu bi. Waɗannan abubuwa da aka gano kada su ƙara mana komai ga fahimtarmu kan mahimmanci ko matsayi na Littafi Mai Tsarki. Littafi Mai Tsarki rubutun kalmomin Allah ne, wanda ba kuskure ko aibi a ciki kuma Allah ne yake ba wa mutane marubuta kuma yana da amfani domin ƙarfafawa da kuma koyar da masu bi hanyoyin Allah: “Kowane nassi hurarre na Allah ne, mai amfani ne kuma wajen koyarwa, da tsawatarwa, da gyara hali, da kuma tarbiyyar aikin adalci, domin bawan Allah ya zama cikakke, shiryayye sosai domin kowane kyakkywan aiki” (2 Timoti 3:16-17). Littafi Mai Tsarki baya buƙatar shaida ta tabbatarwa domin bayyana gaskiyarsa, amma jin daɗi ne sanin cewa ba wani binciken kimiya na kayan tarihi da ya ƙaryata ko kalma ɗaya ta maganar Littafi Mai Tsarki, kuma bincike-bincike da dama sun yi shaida ga tarihinsa da kuma daidaitarsa a kimiyance..
English
Waɗanne abubuwa ne masu burgewa da aka gano cikin binciken kimiya na kayan tarihi na Littafi Mai Tsarki?