Tambaya
Ko akwai ayyukan ruhohin aljanu a cikin duniya a yau?
Amsa
Fatalwa, da bibiya, da Magana da matattu, da katin tarot, da allon duba na Ouija, da kuma madubin bayyana abin da ke gaba—wace alaka gare su? Suna ba mutane da yawa sha’awa saboda suna nuna kamar suna ba da harske ga duniyar da ba a sani ba wadda tafi karfin kasancewarmu. Ga mutane da yawa kuma, waɗannan abubuwa basu da matsala kuma ba su cutarwa.
Mutane da yawa waɗanda suke duban waɗannan batutuwa ba ta mahangar Littafi Mai Tsarki ba sun gaskata da cewa fatalwa ruhohi ne na matattu waɗanda, ko ma saboda wanne irin dalili basu isa “inda ya kamata su je ba.” Bisa ga waɗanda suka gaskata da batun fatalwa, akwai ire-iren bibiya kala uku: (1) Wobuwa (kamar yin tariyar abin da ya wuce ba tare da yin magana da wani ruhu ba). (2) bibiya daga ruhohin mutum, wanda yanayinsa haduwa ce ta abu mai kyau da mara kyau (amma ba mugu ba). irin waɗannan ruhohi suna so ne kawai su ɗauke hankalin mutum; wasu suna zama kamar yan wasa, amma, a wani ɓangare, basa cutar da mutane. (3) yin magana da ruhohin da ba na mutane ba ko aljanu. Waɗannan abubuwa za su iya bayyana a matsayin ruhohin mutane, amma suna cutarwa kuma suna da haɗari.
Lokacin da kake karatu game da fatalwoyi da kuma bibiya wadda ba daga mahangar Littafi Mai Tsarki ba, ka tuna cewa, wai don marubucin yana kwatanci da Littafi Mai Tsarki ko kuma yana ambaton wani suna da yake a cikin Littafi Mai Tsarki (irinsu Mika’ilu babban shugaba) bai nuna cewa yana hangen abin daga mahangar Littafi Mai Tsarki ba ne. Idan ba a bada izini akan bayanin marubuci ba, ya kamata mai karatu ya tambayi kansa, “Ta yaya shi/ita suka san haka? Wane izini gare shi/ta?” Misali, ta yaya marubuci ya san cewa aljanu suna bayyana a matsayin ruhohin mutane? Waɗanda suke duban waɗannan abubuwa ba daga mahangar Littafi Mai Tsarki ba. suna ɗora fahimtarsu ne bisa ga tunaninsu, da tunanin wasu, ko kuma wata ɗanɗanawa tasu a baya. duk da haka, bisa ga yardarsu cewa aljanu suna yaudara kuma suna iya yin koyi da ruhohin mutane masu kyau, waɗannan abubuwa zasu iya zama yaudara! Idan mutum yana so ya sami kyakkyawar fahimta a kan wannan batu, dole ne ya je wajen wata majiya mai tushe da ta kasance daidai kashi 100 bisa 100 a kowane lokaci—Maganar Allah, Littafi Mai Tsarki. Bari mu duba abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da irin waɗannan abubuwa.
1. Littafi Mai Tsarki bai taɓa Magana kan bibiya ba. mai makon haka, ya yarda cewa idan mutum ya mutu, ruhun wannan mutumin yana tafiya zuwa wuri ɗaya cikin biyu. Idan mutumin ya gaskata da Yesu Kiristi, ruhunsa zai tafi gaban Ubangiji a samaniya (Filibiyawa 1:21-23; 2 Korantiyawa 5:8). Daga baya, za a mai da masa da jikinsa ranar tashin matattu (1 Tasalonikawa 4:13-18). Idan mutum ba mai bin Kiristi ba ne, ana sa ruhunsa a wurin azabtarwa da ke kira jahannama (Luka 16:23-24).
Ko mutumin mai bi ne ko mara bi ne, babu zancen dawowa cikin duniyarmu ya yi Magana da mutane ko ya tattauna da su ba, ko da ma saboda dalilin yi wa mutane gargaɗi don su gujewa hukunci mai zuwa ne (Luka 16:27-31). Akwai wuri biyu kaɗai da mataccen mutum ya yi Magana da mai rai. Na farko shi ne lokacin da Sarki Saul na Isira’ila ya yi ƙoƙarin tuntubar matacce annabi Sama’ila ta hanyar mai duba. Allah ya yarda cewa Sama’ila ya damu kwarai har ya furta hukunci kan Saul domin rashin biyayyar da ya yi ta maimaitawa (1 Sama’ila 28:6-19). Na biyu shi ne lokacin da Musa da Iliya suka yi Magana da Yesu lokacin da aka sake masa kamanni a Matiyu 17:1-8. Ba wani abu da ya danganci “fatalwa” game da bayyanar Musa da Iliya.
2. Littafi Mai Tsarki ya yi ta Magana kan mala’iku da suke yawo ba a ganinisu (Daniyel 10:1-21). Wasu lokuta, wadannan mala’iku sun yi Magana da mutane masu rai. Muganyen ruhohi ko aljanu, zasu iya shigar mutane, su zauna a cikinsu su mallake su (duba Markus 5:1-20, alal misali). Bisharu huɗu da kuma littafin Ayyukan manzanni sun rubuta misalai da yawa na waɗanda aljanu suka mallake da kuma bayyanar mala’iku nagari domin taimakon mai bi. Mala’iku, nagartattu da mugaye, za su iya sa abin ban mamaki ya auku (Ayuba 1–2; Wahayin Yahaya 7:1; 8:5; 15:1;16).
3. Nassi ya nuna mana cewa aljanu sun san wasu abubuwan da mutane ba su sani ba (Ayyukan manzanni 16:16-18; Luka 4:41). Da yake waɗannan mugayen malaiku suna nan da daɗewa, za su san abubuwan da mutane da suke da taƙaitattar rayuwa ba za su sani ba. Tun da yake Sheɗan yana da damar zuwa gaban Allah a yanzu, (Ayuba 1-2), ya yiwu za a iya barin aljanu su san wasu abubuwa game da gaba, amma wannan hasashe ne kawai.
4. Littafi Mai Tsarki ya ce Shaiɗan shi ne uban ƙarairayi da kuma mayaudari (Yahaya 8:44; 2 Tasalonikawa 2:9) ya bayyana kansa a matsayin “mala’ikan haske.” Waɗanda suka bi shi, mutane ko wani abu, za su aikata abu iri ɗaya da shi (2 Korantiyawa 11:13-15).
5. Shaiɗan da aljanu suna da iko sosai (idan aka kwatanta su da mutane). Ko Mika’ilu babban shugaba yana dogara ne kaɗai da ikon Allah a lokacin da yake fama da shaiɗan (Yahuza 1:9). Amma ikon Shaiɗan ba komai ba ne idan a ka kwatanta shi da ikon Allah (Ayyukan manzanni 19:11-12; Markus 5:1-20), kuma Allah yana yin amfani da muguwar aniya ta shaiɗan domin ya cika kyakkyawar manufarsa (1 Korantiyawa 5:5; 2 Korantiyawa 12:7).
6. Allah ya umarce mu kada mu haɗa kanmu da duk wani abu da ya shafi sihiri, da bautar Iblis, ko kuma duniyar mugayen ruhohi. Wannan ya ƙunshi yin amfani da duba, da Magana da matattu, da allan duba na Ouija, da bayyana abin da ke gaba, da katin tarot, da kuma hulɗa da ruhohi, da dai sauransu. Allah yana duban waɗannan abubuwa a matsayin abin ƙyama (Maimaitawar Shari’a 18:9-12; Ishaya 8:19-20; Galatiyawa 5:20; Wahayin Yahaya 21:8), kuma waɗanda suka sa kansu cikin irin waɗannan abubuwa suna kira wa kansu bala’i ne (Ayyukan manzanni 19:13-16).
7. Masu bi na Afisa sun nuna misali wajen ƙone kayayyakin sihiri (litattafai, kayan kide-kide, kayan ado, kayan wasanni, da sauransu.). Sun furta aikata waɗannan abubuwa a matsayin zunubi suka kuma ƙone kayayyakin waɗannan ayyuka a fili (Ayyukan manzanni 19:17-19).
8. Samun yanci daga ikon Shaiɗan yana samuwa ne ta wurin Ceton Allah. Ceto ya zo ne ta wurin gaskatawa da bisharar Yesu Kiristi (Ayyukan manzanni 19:18; 26:16-18). Yunkurin daina hulɗa da aljanu ba tare da Ceto ba banza ne. Yesu ya yi gargaɗi kan zuciyar da ta kauce daga fuskar Ruhu Mai Tsarki: wannan zuciyar kamar shararren wuri ne da ba komai da ke shirye domin aljanu da yawa su zauna (Luka 11:24-26). Amma idan mutum ya zo wurin Kiristi domin gafarar zunubai, Ruhu Mai Tsarki zai zauna tare da shi har a ranar fansa (Afisawa 4:30).
Wasu ayyukan da ba daidai bane za a iya danganta su da aikin yaudara. Zai fi dacewa a fahimci bayanai game da fatalwoyi da kuma bibiya a matsayin aikin aljanu. Wasu lokutan aljanu ba sa yin kokarin boye yanayinsu, wasu lokutan kuma za su iya yin amfani da yaudara, su bayyana a matsayin ruhohin mutum. Wannan yaudara tana kara haifar da karairayi da kuma rudani.
Allah ya ce wawanci ne ka nemi shawarar matattu a madadin masu rai. Mai makon haka Ya, ce, ga doka ga kuma shaida!” (Ishaya 8:19-20). Maganar Allah ita ce tushen hikimarmu. Masu bin Yesu Kiristi kada su kasance cikin sihiri. Duniyar ruhohi zahiri ce, amma Kirista baya buƙatar ya ji tsoron ta (1 Yahaya 4:4).
English
Ko akwai ayyukan ruhohin aljanu a cikin duniya a yau?