Tambaya
Mene ne aiki da ruhohi?
Amsa
Aiki da ruhohi, kamar yadda wanda ya kafa ta, Allan Kardec ya bayyana, “wata hanya ce da aka kaddamar don dangantaka tsakanin halittun da ba a gani da kuma mutane.” Kardec malami ne na Faransanci wanda asalin sunansa shi ne Hippolyte Leon Denizard Rivail. Kardec wanda ya tsara Aiki da ruhohi na hakidar Kardecist, kudurin shi ne a yi bincike kan ruhohi—asalinsu, da yanayinsu, da kuma dangantakarsu da duniyar da muke ciki. Aiki da ruhohi ya zama sanannen abin da yanzu an gabatar da shi a kasashe 35. Kardec ya kuma rubuta The Spirits’ Book wajen kokarinsa na banbance yadda aiki da ruhi ya sha bamban da Aiki da ruhohi.
Babban abin da aiki da ruhohi ya kunsa shi ne ruhohin da basu mutu ba suna tafiya daga wannan jiki zuwa wancan na tsawon rayuwa da yawa don su inganta kansu a dabi’a da kuma ilimi. Wannan hakidar ta kamanta da sake haihuwar mutum cikin jiki (reincarnation), akwai bambanci da haka, bisa ga aiki da ruhohi, ruhohi ba za su dawo a matsayin dabbobi ba ko kowane nau’in rayuwa mafi kankanta. Canzawar ruhun kowane lokaci ta yin gaba ce, kuma kowane lokaci ruhohi suna zaune a jikunan mutane. Masu aiki da ruhohi sun gaskata cewa wannan yana bayyana bambance-bambancen yanayi na hankali a cikin ‘yan Adam.
Masu aiki da ruhohi sunce ruhohi marasa jiki suna iya yin alheri ko mugunta ga masu rai kuma ‘yan Adam suna iya tattaunawa da ruhohi ta wurin tsafi da masu duba. Aiki da ruhohi ya sami karbuwa a karni na 19th, tare da zamani, kuma yai dai-dai da ilimi a hanyoyi da dama, musamman a imaninsu na cewa mutum zai iya cigaba da girma ta wurin tunani. Marubuci Sir Arthur Conan Doyle da matarsa shahararrun masu aiki da ruhohi ne.
Aiki da ruhohi ba addini bane amma ilimi ne da kuma “ hanyar rayuwa,” bisa ga masu aiki da ruhohi. Ba masu jawabi, ko kuma tattaruwar kungiya da ta kunshi tattaunawa game da ruhohi, yanda za su dinga ko ba za su dinga tafiya a cikin duniya ba sakamakon wadannan tafiye tafiye, da sauransu. Masu aiki da ruhohi suna daratta binciken kimiya fiye da ibada ko bin dokiki, ko da yake suna yin rayuwa mai kyau ta hankali da neman ilimi.
A zahiri Littafi Mai Tsarki ya hana aiki da ruhohi. Kada mutanen Allah su yi nemi shawarar bokaye. Tsafi da kuma mabiya duka kazantattun abubuwa ne da Allah ya hana (Littafin Firistoci 19:31; 20:6; Galatiyawa 5:20; 2 Tarihi 33:6). Duk da masu aiki da ruhohi suna dora abubuwasu karkashin inuwar “kimiya” ba shi da wani bambanci. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa duniyar ruhu bata da iyaka a gare mu, domin kariyarmu.
Ruhun da masu aiki da ruhohi suke amfani da shi ba na mutane bane; Littafi Mai Tsarki ya ce ruhohin mutane suna fuskantar shari’a bayan mutuwa (Ibraniyawa 9:27), kuma ba wani abu a Littafi Mai Tsarki da ya nuna cewa ruhohi suna dawo wa cikin duniyar masu rai domin wani dalili ko kuma ta wata siffa.
Mun san Shaidan mayaudari ne (Yahaya 8:44). Abin da Littafi Mai Tsarki ya karkare shi ne, duk wata Magana da bokaye za su yi da “rayukan matattu” Magana ce da aljanu a boye (Wahayin Yahaya 12:9). Aiki da ruhohi bai tafi dai-dai da Littafi Mai Tsarki ba kuma a ruhaniyace yana da hadari. “Ku natsu, ku zauna a fadake. Magabcinku Iblis yana zazzagawa kamar zaki mai ruri, yana neman wanda zai lankwame” (1 Bitrus 5:8).
English
Mene ne aiki da ruhohi?