Tambaya
Mene ne aiki da ruhi?
Amsa
A karnuka kadan da suka gabata, an sami karuwar sha’awar yin Magana da matattu. Akwai talabijin da ya nuna mafarauta na fatalwa suna tsallakewa, wannan ya zama kyakkyawan misali. Cikin labarin na wanda ya je, ya ba da akan wadannan da kuma saura abubuwa, duniya tana da tatsuniyoyi na hulda da duniyar ruhohi, wasu masu karfafa zuciya wasu kuma masu ban tsoro. Wadanda suke cikin irin wadannan ayyuka ba kowane lokaci suke fahimta ko su gane babbar kasada ta ruhaniya da suke dauka ba .
Ruhaniyanci karyar tsarin addini ce wadda abu mafi bayyana shi ne gaskatawa cewa rai yana rayuwa bayan mutuwar jikin da ake iya gani kuma wadannan ruhohi da basu cikin jiki za su iya Magana da mutane masu rai. Kamar Kirista, masu aiki da ruhu sun gaskata da Allah daya—wanda suke cewa “Madawwami”—da kuma cewa kowane rai zai ba Allah lissafin abin da ya aikata ko zabin da ya yi a rayuwa. Ba kamar Kirista ba, masu aiki da ruhohi basu yarda cewa mutuwa ita ce abu na karshe na shari’anta ruhu ba, amma rai yana da ikon koyo, da yin girma, ya kuma kasance bayan mutuwa ya kara samun dama ta kara girman sani da kuma daidaita. Basu gaskata da cewa mutuwar Yesu ta biya hukuncin zunubi ba da kuma cewa ceto yana zuwa ne ta wurin alheri ta wurin bangaskiya cikin Kiristi, maimakon haka rai yana girma bayan mutuwa ta wurin matakai da dama zuwa ga wani mataki na cika a ruhu. Saboda haka, akwai aikin da za ka iya yi don “ceto” bayan mutuwa.
Aiki da ruhu ya sami faddada ne a 1840s da kuma juyowar karni a Amurka ta Arewa da kuma Kudancin Tuarai. A wadannan lokuta na yake-yake da kashe-kashe, mutane suna ta’azantar da kansu ta wurin Magana da kaunatattunsu da suka mutu. Masu binciken tarihi sun bayyana Maris 31, 1948, a matsayin ranar da aka fara Magana da ruhohi, sa’ad da Margaret da Kate Fox, ta Hydesville, New York, ta fara ba da sanarwa mai ban mamaki cewa sunyi Magana da ruhun wadda aka kashe wato peddler a cikin gidansu. Peddler tana Magana da su ta wurin kwankwasa teburi ko bango. Bayan haka, zaman lafiya ya bunkasa a tsakanin manyan masu matsakaicin matsayi da kuma attajiran Amurka. Matsakaita irin su Paschal Beverly Randolph da Cora Scott toured kasar tana ba da koyarwa da bayanai. A wannan lokaci, rubuce rubucen Franz Mesmer, daga wanda aka samo sunan mesmerism, musamman ya rinjayi ra’ayin masu Magana da ruhohi na bayan rayuwa da kuma Magana da Mafi girma.
Akwai da yawa da suka mika kai wajen bautar ruhi, sun hada da Mary Todd Lincoln (matar Abraham Lincoln) da Sir Arthur Conan Doyle, marubucin Sherlock Holmes mysteries. A karshen 1880s, masu bincike suka fara fallasa sanannun hanyoyin sadarwar a matsayin yaudara , a kuma tabbatar an hana tattaruwarsu. Harry Houdini ya zama sananne wajen kokarinsa na tona masu zamba.
Aiki da ruhi ya ja hankalin masu bi da yawa wadanda basu farin ciki da kafa Ikilisiyoyi kuma suke neman a gyara. Hakika, da yawa daga cikin masu rusarwar na farko da kuma masu fafutukar kare hakkin mata sun kasance masu aiki da ruhi. Tattaruwar masu aiki da ruhi ta ba mata dama ta farko ta suyi Magana gaba gadi a cikin al’ummar da maza suke da rinjaye. Radical Quakers, wadanda suka ki amincewa da cigaba da kafa Ikilisiyoyi domin gazawarsu ta yin adawa da bauta, suka yi amfani da aiki da ruhi a matsayin masu gaba da tsarin zuwa bauta. Duk da cewa wannan yunkurin ya kawo sauye-sauye da dama a al’umma, ya sa mutane da dama sunyi kaura zuwa aikin ruhu irin na duniya, suka maida hankali ga dandanawa ta kai da kuma sako mara tabbaci daga waje, suka kuma karfafa rayuwa tare yin rayuwa da Yesu Kiristi.
Su ne Bulus ya bayyana a matsayin tsarin imani na addini da suka musalci gaskiyar bishara, kaffarar zunubi ta wurin mutuwar Yesu Kiristi a kan gicciye, a matsayin, “suna dauke da siffofin ibada amma sun musalci ikon ta” (2 Timoti 3:1–5). Duk da, da yawa cikin masu aiki da ruhi suna zuwa sudajar Lahadi, suna raira wakoki, suna kuma yiwa Allah daya sujada, aiki da ruhi da kuma Kirsitanci ba abu guda bane. Baya ga gaskatawarsu ga juyin halitta na rayuka ta hanyar samun girma bayan mutuwa, masu amfani da ruhi suna neman hulda da su ne ta wurin séances, Ouija boards, da matsakaita. Masu aiki da ruhhohi da yawa suna cewa suna da nasu jagorancin, daga wanda suke samun dukkan sakonni su kuka sa su a rayuwarsu. Ga masu aiki da ruhi, Littafi Mai Tsarki ba shi bane asalin tushen gaskiya da kuma sani game da bayan rayuwa da Allah.
Littafi Mai Tsarki na dauke da tsattsaurar fadakarwa akan aiki da ruhi (Littafin Firistoci 19:31; 20:6; Maimaitawar Shari’a 18:9–13). Sarkin Isira’ila na farko, Sarki Soul, ya karya umarnin Allah na kada ya kasance cikin aiki da ruhi kuma ya rasa mulkinsa saboda haka (1 Sama’ila 15:23; 1 Tarihi 10:14). Sa’ad da manzanni suka hadu da mutane masu aiki da ruhi da suke da wani iko daga ruhohi, sukan fitar da wadannan ruhohi a matsayin aljanu (Ayyukan manzanni 16:16–18). Nassoshi da dama sun ba da manyan dalilai na cewa kada Kiristoci su nemi hulda da ruhi, suka ce ruhohi da ake Magana da su aljanu ne kuma za su iya ba da sako wanda ba na dogaro ba ko kuma na rudarwa (1 Yahaya 4:1).
Akwai yiwuwar cewa yawancin masu Magana da matattu ta wurin aiki da ruhi yaudara ce. Sauran masu magana da kaunatattunsu da suka mutu ta wurin amfani da Ouija boards, matsakaita, da kuma séances Magana ce da aljanu wadanda suke ba da bayani na karya. Wata karya da mutane suka fi samu ta wurin magana da alloli ita ce ba jahannama ba kuma shari’a ta karshe da ga Allah. Amma Ibraniyawa 9:27 ta bayyana cewa, “Tun da yake an kaddara wa mutum ya mutu sau daya ne, bayan haka kuma sai shari’a.” Mutuwa ba ta da makawa, haka kuma shari’a. zunubi shi ya kawo shari’a, kuma kowa yana da shi (Romawa 3:23). Hanya daya tak da mutum zai gujewa hukunci shi ne mu karbi alheri daga Allah ta wurin bayyana zunuban mu, da yarda da cewa Yesu ya mutu domin zunuban, da kuma amincewa ya mika rayuwarsa ga Kiristi kafin mutuwarsa (Yhaya 3:16; Romaawa 3:24). Littafi Mai Tsarki ya bayyana karara cewa duk wanda ya mutu ba tare da Kiristi ba zai sha azaba ta har abada a jahannama (Matiyu 25:41). Gaskatawa da koyarwar karya da ake samu daga “jagorantar ruhi” zai karkatar da mutane da dama daga koyarwar Littafio Mai Tsarki, wanda shi ne shirin Shaidan (1 Bitrus 5:8; 1 Timoti 4:1).
Wadanda suka shiga aiki da ruhi suna yin ayyukan da za ka ga kamar ba su da wata illa amma a zahiri suna bude kofa don saduwa da aljanu, firgici harma da zarge-zarge. Da yawan masu aiki da ruhi an raunanar da su an kuma gurbata tunaninsu, ko ba a fili ba, ta wurin saduwa da aljanu da yake farawa da séances, Ouija boards, Magana da matattu, Reiki healing, da kuma magana da matsakaita. Ga dukkan wadanda suke neman gaskiya, Yesu ya yi magana da babbar murya a Yahaya 14:6, “Ni ne hanya ni ne gaskiya ni ne kuma rai. Ba mai zuwa wurin Uba sai ta wuri Na.”
English
Mene ne aiki da ruhi?