settings icon
share icon
Tambaya

Ko Littafi Mai Tsarki ya karfafa ko ya haramta yin addu'a zuwa ga mala'iku?

Amsa


Ba ayar da ta bayyana karara cewa, “Kada ku yi addu’a zuwa ga mala’iku,” amma a bayyane yake cewa kada mu yi addu’a zuwa ga mala’iku. A zahiri, addu’a wani nau’I ne na sujada. Kuma, kamar yadda mala’ika ya ki yarda mu yi masa sujada (Wahayin Yahaya 22:8-9), hak kuma za su ki yarda mu yi addu’a zuwa gare su. Yin sujada ko addu’a ga wani ban da Allah bautar gumaka ne.

Akwai ayyuka da yawa da kuma dalilai na tauhidi na abin da ya sa addu’a ga mala’iku ta zama ba laifi. Kiristi kansa bai taba yin addu’a ga wani sai dai Uba. Sa’ad da almajiransa suka ce masa ya koya masu yadda za su yi addu’a, ya ce masu, Saboda haka sai ku yi addu’a kamar haka: “Ya Ubanmu, wanda ke cikin sama…” (Matiyu 6:9; Luka 11:2). Idan da addu’a zuwa ga mala’iku abu ne wanda mu a matsayin almajiransa za mu yi, wannan shi ne wurin da zai gaya mana. To zahiri, ga Allah kadai za mu yi addu’a.

Wannan ma shaida ce a nassi irin su Matiyu 11:25-26, inda gabatar da addu’ar Kiristi ta fara da "Na gode maka ya Uba, Ubangijin sama da kasa...." Yesu ba addu’arsa tana farawa da Uba bane kawai, amma bukatar da ke cikin addu’arsa bukata ce da wanda zai iya biyan ta sai dai mai iko duka, da masanin abu duka, da kuma ikon wanda yake ko’ina.

Addu’a zuwa ga mala’iku ba za ta zama da amfani ba domin suma halittarsu aka yi kuma ba su dauke da irin wannan ikon.

Lamarin da ya hana yin addu’a ga mala’iku za a iya kara tabbatar da shi ta wurin kara duba Yahaya 17:1-26 inda Yesu ya yi addu’a a madadin mabiyansa, yana rokar masu albarku masu yawa daga gun Allah Uba, ya hada da tsarkakewa, da daukakawa, da kuma kariyar tsarkaka. Wadannan albarku guda uku za su iya zuwa ne kadai daga wanda yake rike da su, kuma, mala’iku ba su da irin wannan iko. Mala’iku ba za su iya tsarkake mu ba, ba za su iya daukaka mu ba, ba kuma za su iya tabbatar mana da gadonmu a cikin Kiristi ba (Afisawa 1:13-14).

Na biyu, akwai wani abu da ya faru a cikin Yahaya 14:13 sa’ad da Kiristi da kansa ya gaya wa masu bi cewa duk abin da muka roka da sunansa, zai yi shi domin yana roko ne kai tsaye daga wurin Uba. Yin addu’a ga mala’iku za ta zama kasawa kan addu’a ta jagorancin Littafi Mai Tsarki.

Al’amari na biyu da Kiristi ya fada shi ne ga sunansa kadai za ayi addu’a a cikin Yahaya 16:26. Wannan ayar tana ba da sakon cewa, bayan hawan Yesu zuwa sama, ya tsaya a matsayin matsakaici a wurin Allah ga dukkan masu bi. Ba wasu mala’iku ko wani wanda aka halitta da zai iya tsayawa a matsayin matsakaici tare da Uba. Dan ne kadai da Ruhu Mai Tsarki (Romawa 8:26) za su iya tsayawa tsakani a gaban kursiyin Uba.

Na karshe, 1 Tasalonikawa 5:17 ta gayawa masubi su rika yin addu’a ba fasawa. Wannan zai iya yiwuwa ne kadai idan mai bi yana da hanyar zuwa gun Allah wanda a koyaushe yana nan a shirye ya saurari rokon kowane mutum a kowane lokaci. Mala’iku ba su da wannan iko—su ba su a ko’ina kuma ba komai suka sani ba—don haka ba su cancanci su karbi addu’oin mu ba.

Addu’a ga Uba ta wurin Kiristi ita ce kadai ta zama wajibi da kuma kyakkyawar hanya wadda zamu yi Magana da Uba. Addu’a ga mala’iku ba daga Littafi Mai Tsarki ba ne.

English



Koma zuwa shafin gida na Hausa

Ko Littafi Mai Tsarki ya karfafa ko ya haramta yin addu'a zuwa ga mala'iku?
© Copyright Got Questions Ministries