Tambaya
Ko Yesu ƙagaggen labari ne kawai? Ko Yesu kwafin allolin al’ummai ne na sauran addinan dā?
Amsa
Akwai mutane da yawa da suke cewa labaran Yesu kamar yadda aka rubuta a Sabon Alkawari ƙagaggun labarai ne kawai da aka aro daga tatsunniyoyin al’ummai, kamar su labarin Osiris, Dionysus, Adonis, Attis, da Mithras. Abin da ake cewa shi ne waɗannan labarai ne iri ɗaya da labarin Yesu Kiristi a sabon alkawari. Kamar yadda Dan Brown ya ce a Da Vinci Code, “Babu wani abinda yake na sahihi a Kiristanci.”
Domin a binciko gaskiya game da cewa marubutan bisharu sun yo aro daga masu ƙirƙira ƙagaggun labarai, yana da mahimmanci (1) ka bincika tarihi game da bayanin (2) ka duba abubuwan da allolin ƙaryar suka yi idan ka kwatanta da na Kiristi, (3) ka fallasa dukan wata ƙarya da aka yi (4) ka kuma duba dalilin da yasa aka yarda da bisharun Sabon Alkawari a matsayin hoto na abubuwan da suke na gaskiya da kuma tarihin Yesu Kiristi.
Bayanin cewa Yesu ƙagaggen labari ne ko kuma rurutawa ce ya sami tushe daga masana tauhidi na Jamus a ƙarni na 90. sun faɗi cewa Yesu ba wani abu bane ban da hoton sanannun allolin nan masu mutuwa da tashi a wurare daban daban---Tammuz a Mesopotamia, Adonis a Siriya, Attis a Asiya Minor, da kuma Horus a Masar. Abin dubawa shi ne babu wani littafi mai ɗauke da waɗannan labaran da ake ɗauka da mahimmanci a sashin ilimi a yau. An bincika bayanin da ya sake tasowa na cewa Yesu kamar Tammuz ne da ya sake dawowa, a misali, masana na zamani sun kuma gano cewa labarin bashi da wani tushe. Duka ba daɗewa da wannan zance ya sake tasowa, musamman saboda kasancewar yanar gizo da kuma yawan yaɗa labarai marasa tushe.
Wannan ya kai mu ga fage na gaba na bincike—ko da gaske ƙagaggun labaran alloli na dā sun bada hoton Yesu Kiristi? A misali, bidiyon Zeitgeist ya yi waɗannan bayanai game da allan Masarawa Horus:
• an haife shi a watan Desamba 25 daga wata budurwa Isis Mary:
• Tauraruwa daga gabas ta bayyana kasancewarsa
• Sarakuna uku sun zo domin su girmama jaririn “ mai ceto”
• ya zama yaro mai hikima ta koyarwa a shekara 12
• A shekara ta 30 aka yi masa “ baftisma” ya fara “ aikinsa”
• Horus yana da “ almajirai” goma sha biyu
• An bashe da Horus
• An gicciye shi
• An binne shi na kwana uku
• Bayan kwana uku ya tashi
Duk da haka, bayan an bincika asalin rubutun da aka yi game da Horus, wannan shi ne abin da muka gano:
• Isis ce ta haifi Horus; ba wani wuri a tarihi da aka kira ta da “ Mary” bugu da kari, “ Mary” suna ne na Turanci da ake amfani da shi na asalin sunanta. Miriam, Amma bama ayi amfani da “ Mary” a cikin asalin bugu na farko na Littafi Mai Tsarki ba.
• Isis ba budurwa ba ce; ita gwauruwar Osiris ce kuma ta tauri cikin Horus daga Osiris.
• an haifi Horus a watan Khoiak (oct/Nuw), ba Desamba 25 ba. Bugu da kari ma, ba inda aka fadi asalin ranar haihuwar Kiristi a Littafi Mai Tsarki.
• Ba wani wuri da aka rubuta sarakuna uku sun ziyarce shi ranar haihuwarsa. Littafi Mai Tsarki bai fadi asalin yawan shehunan da suka zo su ga Kiristi ba.
• Horus ba “ Mai Ceto” bane ta kowace hanya; bai mutu domin kowa ba.
• Ba wani labara na cewa Horus malami ne a shekara 12.
• Ba’ a yi wa Horus “ baftisma” ba. Labari daya da aka bada na Horus da ya shafi ruwa guda daya ne in da aka yanyana Horus, inda Isis take rokon wani allah kada ya buto da shi daga cikin ruwea.
• Horus ba shi da wata “ ma’ aikata.”
• Horus ba shi da almajirai goma sha biyu. Bisa ga labarin Horus, Horus yana da alloli biyu da suke binsa, akwai kuma wasu mabiya 16 da aka bayyana da kuma abokan gabarsa wadanda suke yaki da shi da ba’ a san yawansu ba.
• Ba wani labarin bashewa da abokin Horus ya yi masa.
• Horus bai mutu ta wurin gicciyewa ba. Akwai labaran mutuwar Horus da dama, amma ba wanda ya kunshi gicciyewa.
• Ba wani labara da yace an bizne Horus na kwana uku.
• Horus bai tashi daga matattu ba. ba kuma wani labara da yace Horus ya fito daga kabari da jikin da ya shiga da shi. Wasu labaran sun ce Isis ya dawo da Horus/Osiris da rai ya kuma cigaba da zama ubangijin karkashin duniya wato jahannama.
Idan muka kwatanta bango da bango, Yesu da Horus in da suka kamanta da juna kadan ne idan ma akwai.
An kuma kamanta Yesu da Mithras daga wadanda suke cewa bayanin Yesu kagaggen labara ne. Dukan waɗannan kwatanci na Horus sun samu ne ga allahn rana (e.g., budurwa ta haife shi, gicciyewa, tashi bayan kwana uku, da sauransu).
Amma menene labarin Mithras ya ce?
• An haife shi daga cikin dutse mai ƙarfi, ba daga wata mace ba.
• Da farko ya yi yaƙi da rana daga nan kuma sai turkakken sa, wanda aka ce shi ne halitta ta farko. allahn rana ya kashe san, wanda daga baya ya zama tushen rayuwa ta yan Adam.
• An yi bikin haihuwar Mithras’s a Desamba 25 ba, a lokacin hunturu.
•Ba inda aka ambaci cewa shi babban malami ne.
• Ba inda aka ambaci cewa Mithras yana da almajirai goma sha biyu. Dabarar cewa Mithras yana da almajirai 12 ya yiwu ta zo ne daga wani babban hoto da Mithras yake kewaye da alamomi na zodiac sha biyu. Ba inda aka ambaci cewa Mithras yana da almajirai goma sha biyu.
• Mithras bai tashi da jiki ba. Bayan da Mithras ya gama aikinsa a duniya, an ɗauke shi zuwa Firdausi cikin karusa, da rai da lafiyarsa. Marubucin Kristanci na farkoTertullian ya yi rubutu akan kungiyar asiri ta Mithras yana bayyana alamun tashi daga matattunsa, amma wannan ya faru ne da daɗewa bayan zuwa Sabon Alkawari, don haka idan ma akwai wani kwaikwayo to addinin Mithras ne yake kwafa daga Kristanci.
za' a iya bada misalai da yawa kan Krishna, Attis, Dionysus, da kuma sauran labaran alloli, amma duk sakamakon iri daya ne. A ƙarshe, abubuwan tarihi da Yesu ya yi a Littafi Mai Tsarki sun fita da ban. duk wani ikirarin makamancin labarin Yesu da ƙagaggun labarai na al'ummai duk farfaganda ce kawai. bugu da ƙari, tatsunniyoyi game da Horus, Mithras, da dai sauran addinan da suka zo kafin Kristanci, akwai kadan daga cikin tarihin abubuwan da waɗannan addinai suka yi imani kafin zuwan kiristanci. Da yawa daga cikin rubuce-rubuce na farko na addinai sun fara tun daga ƙarni na uku dana hudu A.D. Yin tunanin cewa wannan gaskatawar da waɗannan addinai suke da ita kafin zuwan Kiristanci (wadda ba ta a rubuce) ta yi kama da abin da Kirista suka gaskata jahilci ne. zai fi ba da ma’ana ka danganta duk wata kamanceceniya tsakanin wadannan addinai da Kiristanci da cewa addinan sun kwaikwayi koyarwar Kiristanci game da Yesu.
Wannan shi ya kai mu sashi na gaba da zamu duba: yaudarar da masu cewa Kristanci ya aro daga addinan asirai da arna suka yi. Zamu yi la’akari da yaudara biyu musamman: yaudarar ƙarya da ke haddasa kalamai na ƙarya.
Idan wani abu ya riga wani kasancewa, wasu sun yanke cewa abu na farko shi ya haifar da na biyu. Wannan ita ce yaudarar da ƙarya ta haifar. Zakara na iya yin cara kafin fitowar rana kowace safiya, amma wannan bai nuna cewa zakaran shi ya sa rana ta fito ba. Ko da labarin allolin da suke nan kafin Kristanci ya yi kama da na Kiristi (kuma bai ma yi ba), bai nuna cewa hakan ya sa marubutan Bisharu su ƙirƙiri Yesun ƙarya ba. Yin irin wannan ikirari ya yi daidai da faɗin cewa jerin shirye-shiryen bidiyo (TV) na star trek ya haifar da shirin jirgin sama na NASA.
Yaudara ta kalamai na ƙarya tana kasancewa ne lokacin da aka sake ma’anar kalma domin ta ba da hujja. Misali, fim din Zeitgeist ya ce Horus “ya fara hidimarsa, amma kalmar hidima an canza ta. Horus ba shi da wata “hidima” ta musamman – ba wani abu da ya yi kama da aikin Kiristi. Waɗanda suke danganta Yesu da Mithras suna magana ne game da “baftisma” domin shigar da sababbin mutane addinin Mithras, amma mene ne asali abin? Firistocin Mithras za su sa sababbin shiga a cikin rami, su rataye bajimi bisa ramin, su yanka cikin bajimin, domin jini ya lullube sababbin shiga. Irin wannan abu bai yi kama da baftismar Kirista ba a ko kaɗan. Nutsar da mutum cikin ruwa (yana nuna mutuwar Kiristi) tasowa daga cikin ruwan kuma (yana nuna tashin Kiristi daga matattu). Amma masu cewa Yesu ƙagaggen labari ne cikin yaudara suna amfani da wannan kalma, “baftisma”, domin su bayyana dukan ayyukan da ƙoƙarin danganta biyun.
Wannan shi ya kawo mu ga maganar gaskiyar Sabon Alkwari. Ba wani aiki da aka taɓa yi da yake da shaida ta tabbacin tarihinsa fiye da Sabon Alkawari. Sabon Alkwari yana da yawan marubuta (tara), mafi kyawun marubuta, da kuma marubuta na wuri fiye da duk wani rubutu da ya kasance a zamanin. Bugu da ƙari, tarihi ya ba da shaidar cewa waɗannan marubuta sun mutu suna faɗar cewa Yesu ya tashi daga matattu. Wasu za su iya mutuwa akan ƙaryar da suke tunanin cewa gaskiya ce, amma ba mutumin da zai mutu akan ƙaryar da yasan cewa ƙarya ce. Ka yi tunani akan haka—an yi maka barazanar gicciyewa, kamar yadda al’ada ta ce idan da kai ne manzo Bitrus, kuma abin da za ka yi ka ceci kanka shi ne ka ƙaryata ƙaryar da ka faɗi kuma dama ka san ƙarya ka faɗi, me za ka yi?
Ƙari akan haka, tarihi ya nuna cewa a ƙalla sai zuriya biyu ta wuce kafin ƙagaggen labari ya shiga tarihi. Saboda indai akwai shaidu na gani da ido na abin da ya faru, ana iya ƙaryata kurakurai a kuma fallasa duk wata ƙarya da take cikin labarin. Dukan bisharu na Sabon Alkawari an rubuta su ne a lokacin rayuwar shaidu na gani da ido, tare da wasu wasiƙun Bulus da aka rubuta tun farkon A.D. 50. Bulus ya yi kira kai tsaye ga waɗanda suke nan kuma shaidu na gani da ido domin su bada shaidar maganarsa (1 Korantiyawa 15:6).
Sabon Alkawari ya tabbatar da gaskiyar cewa a ƙarni na farko, ba a yi kuskuren ɗaukar Yesu da wani allah ba. Lokacin da Bulus yake wa’azi a Atina, masu ilimi na wannan gari suka ce, “‘Ga alama, mai yin wa’azin baƙin alloli ne”—domin kawai yana yin bisharar Yesu, da kuma tashinsa daga matattu. Sai suka riƙe shi suka kai shi Tudun Arasa, suka ce, “ko ka faɗa mana wace irin baƙuwar koyarwa ce wannan kake yi? Domin ka kawo mana abin da yake baƙo a gare mu, muna kuwa so mu san ma’anarsa.”’ (Ayyukan manzanni 17:18–20, NASB). A zahiri, idan da Bulus yana maimaita labaran sauran alloli ne, da Arasawan ba su bayyana koyarwarsa a matsayin “sabuwa” da kuma “baƙuwa” ba. Idan da mutuwa da tashin alloli ya yawaita a ƙarni na farko, me ya sa, lokacin da manzo Bulus ya yi wa’azin Yesu ya ta shi daga matattu, ko Abikuriyawa da Sitokiyawa ba su yi Magana sun ce, “Ah, kamar Horus da Mithras ba”?
A ƙarshe, Maganar cewa Yesu kwaikwayo ne na ƙagaggun alloli ta samo asali ne daga marubuta waɗanda masu ilimi kuma sun ƙaryata ayyukansu, domin yana ɗauke da yaudara, kuma ba za a iya kwatanta shi da Bisharu na Sabon Alkawari ba wanda ya jure kusan shekaru 2,000 na bincike mai zurfi. Kwatancin da yake tsakanin Yesu da wasu alloli ya ɓace sa’ad da aka bincika asalin ƙagaggun labaran. Ruwayar cewa Yesu ƙagaggen labari ne ta danganta ga zaɓaɓɓun kwatance-kwatance da aka bayyana, da sake fasalin kalmomin, da kuma zace-zace na ƙarya.
Yesu Kiristi na musamman ne a tarihi, muryarsa ta fi ƙarfin dukan muryoyin alloli na ƙarya yayin da ya yi tambayar da ta iyakance makomar mutum ta har abada: “Wa kuke cewa nake?” (Matiyu 16:15).
English
Ko Yesu ƙagaggen labari ne kawai? Ko Yesu kwafin allolin al’ummai ne na sauran addinan dā?