Tambaya
Ko Yesu Allah ne a cikin jiki? Me yasa yake da mahimmanci cewa Yesu Allah ne a cikin jiki?
Amsa
Tun daga daukar cikin Yesu ta wurin Ruhu Mai Tsarki a cikin cikin budurwa Maryamu (Luka 1:26-38), ainihin asalin Yesu Kiristi an yi ta tambayoyi akansa daga masu shakka. An fara da Yusufu, saurayin Maryamu, wanda ya ji tsoron ya aure ta sa’ad da ta bayyana cewa tana da ciki (Matiyu 1:18-24). Ya dauke ta a matsayin matarsa ne sa’ad da mala’ila ya tabbatar masa da cewa yaron da take dauke da cikinsa Dan Allah ne.
Daruruwan shekaru kafin haihuwar Kiristi, annabi Ishaya ya yi fadin zuwar Dan Allah: “Ga shi an haifa mana da! Mun sami yaro! Shi zai zama Mai Mulkinmu. Za a kira shi, “Mashawarci Mai Al’ajabi,” “Allah Madaukaki,” “Uba madawwami,” “Sarkin Salama.” (Ishaya 9:6). Sa’ad da mala’ika ya yi magana da Yusufu ya sanar masa da haihuwar da za a yi ta Yesu, sai ya danganta abin da annabcin annabi Ishaya: "Ga shi budurwa za ta yi juna biyu ta haifi da, za a kuma sa masa suna Immanuwel (ma’anar Immanuwel kuwa ita ce Allah na tare da mu’)" (Matiyu 1:23). Wannan ba yana nufin a sa wa yaron suna Immanuwel ba; yana nufin cewa “Allah na tare da mu” wannan shi ne asalin Yaron. Yesu Allah ne ya zo jikin jiki ya zauna tare da mutane.
Yesu kansa ya san akwai maganganu game da ko shi wane ne. ya tambayi almajiransa, “Wa mutane suke cewa Dan mutum yake?" (Matiyu 16:13; Markus 8:27). Amsoshin sun bambanta, kamar yadda suke cewa a yau. Sai Yesu ya kara yin tambaya: "Amma ku fa, wa kuke cewa nake?" (Matiyu 16:15). Bitrus ya ba da amsa dai-dai: "Kai ne Almasihu, Dan Allah Rayayye" (Matiyu 16:16). Yesu ya tabbatar da gaskiyar amsar Bitrus ya kuma yi alkawarin cewa, akan wannan dutsen, Zai gina Ikilisiyarsa (Matiyu 16:18).
Gaskiayar yanayin Yesu da kuma ko wane ne shi yana da mahimmanci madawwami. Dole kowa ya amsa tambayar da Yesu ya yi wa almajiranSa: "Wa kuke cewa nake?"
Ya bamu daidaitattun amsoshi ta hanyoyi da yawa. a Yahaya 14:9-10, Yesu ya ce masa, "Duk wanda ya ganni, ai ya ga Uban. Yaya za ka ce ‘nuna mana Uban’? Wato baka gaskata ba cikin Uba nake, Uba kuma cikina? Maganar da nake fada muku, ba domin kaina nake fada ba, Uba ne yake zaune a cikina yake yin ayyukansa."
Littafi Mai Tsarki ya bayyana komai game da yanayi na Allahntakar Ubangiji Yesu Kiristi (duba Yahaya 1:1-14). Filibiyawa 2:6-7 ya ce, ko da yake Yesu, "a cikin surar Allah yake, bai maida daidaitakar nan tasa da Allah abar da zai rike kan kan ce ba, sai ya maida kansa baya matuka ta daukar surar bawa, da kuma kasancewa da kamannin dan adam." Kolosiyawa 2:9 ta ce, “Domin a cikinsa ne cikin jiki dukan cikar Allahntaka take tabbata.”
Yesu Allah ne cikakke mutum ne kuma cikakke, amma daukar siffar mutum da ya yi yana da matukar mahimmanci. Ya yi rayuwa ta mutum amma dauki hali na zunubi kamar yadda muke yi ba. an jarabce shi amma bai ta ba yin zunubi ba (Ibraniyawa 2:14-18; 4:15). Zunubi ya shigo ta wurin Adamu, kuma zunubin Adamu kowane mutum da aka haifa a cikin duniya an haife shi da wannan zunubi (Romawa 5:12)—banda Yesu. Domin Yesu ba shi da Uba na jiki, bai gaji wannan zunubi ba. Ya dauki kamanninsa ne ga Ubansa na Sama.
Sai da Yesu ya cika duk wani abu da ake bukata na Tsarkin Allah Kafin ya zama hadaya karbabbiya domin zunubanmu (Yahaya 8:29; Ibraniyawa 9:14). Sai da ya cika kusan annabci dari uku game da Mai Ceto, ta wurin fadar annabawa (Matiyu 4:13-14; Luka 22:37; Ishaya 53; Mika 5:2).
Tun daga faduwar mutum (Farawa 3:21-23), hanya daya ta daidaitawa da Allah shi ne hadaya ta jinin mara laifi (Littafin Firistoci 9:2; Kidaya 28:19; Maimaitawar Shari’a 15:21; Ibraniyawa 9:22). Yesu shi ne cikakkar hadaya ta karshe da ta isa ta dauke fushin Allah akan zunubi har abada (Ibraniyawa 10:14). Wannan yanayi na Allahntaka ya sa ya yi daidai da aikin Ceto; jikinsa na mutum ya bar shi ya zubar da jininsa domin ya yi Ceto, ba wani mutum da yake hali na zunubi da zai iya biyan wannan ba shi. ba wanda zai iya cika abubuwan da ake bukata na zama hadaya domin zunuban dukan duniya (Matiyu 26:28; 1 Yahaya 2:2). Da a ce Yesu mutumin kirki ne kawai kamar yadda wasu suke cewa, to yana da zunubi kuma bai cancanta ba. don haka, Mutuwarsa da tashinsa ba su da iko su ceci wani.
Saboda Yesu Allah ne a cikin jiki, shi kadai ne zai iya biyan bashin da Allah yake bin mu. Wannan nasara kan mutuwa da kabari nasara ce ga duk wanda ya ba da gaskiya gare shi (Yahaya 1:12; 1 Korantiyawa 15:3-4, 17).
English
Ko Yesu Allah ne a cikin jiki? Me yasa yake da mahimmanci cewa Yesu Allah ne a cikin jiki?