Tambaya
Idan Allah ya san cewa Shaidan zai yi tawaye, me yasa ya halicce shi?
Amsa
Wannan tambaya ce da ta kasu biyu. Sashi na farko “ko Allah ya san cewa shaidan zai yi tawaye?” A cikin Littafi Mai Tsarki mun sani cewa Allah yana da riga sani, wanda ke nufin cewa “ya san komai.” Ayuba 37:16; Zabura 139:2–4, 147:5; Karin magana 5:21; Ishaya 46:9-10; da kuma 1 Yahaya 3:19–20 basu bar wata shakka akan cewa sanin Allah ba shi da matuka ba da kuma cewa ya san dukkan abin da ya faru a baya, da abin da yake faruwa yanzu, da kuma abin da zai faru a gaba.
Idan muka dubi wadansu manya manyan abubuwa a ayoyin—“cikakken sani”; “fahimtarsa ba ta da iyaka”; “ya san dukkan komai”—a bayyane yake cewa sanin Allah bawai ya fi namu nesa ba, amma ba shi da iyaka. Ya san dukkan komai. Idan da Allah ba shi da cikakken sani, to akwai kasawa a cikinsa. Idan Allah na da kasawa ko ya take ba zai zama Allah ba, domin Allah yana bukatar ya zama cikakke a cikin dukan komai. Saboda haka, amsar ita ce “I, Allah ya san Shaidan zai yi tawaye.”
Idan muka gangara zuwa sashin tambayar ta biyu, “Me yasa Allah ya halicci Shaidan kafin lokacin ya san da cewa Shaidan zai yi tawaye?” Wanna tambayar tana fda yar sarkakiya domin tambayarmu aka yi “me yasa” Tambaya ce da Littafi Mai Tsarki bai tabbatar da cikakkun amsoshi ba. duk da haka, dole zamu fahimta. Mun riga dai munga cewa Allah masanin komai ne. to, idan Allah ya san da cewa Shaidan zai yi tawaye ya fado daga sama, kuma Ya halicce shi, wannan na nuna cewa Shaidan yana cikin shirin Allah tun daga farko. Ba wata amsa da tafi dacewa da ta wuce abubuwan da muka riga muka gani.
Da farko, mu fahimci cewa sanin Shaidan zai yi tawaye ba daya yake da sa Shaidan ya yi tawaye ba. Mala’ika Lucifer yana da yancin yin zabinsa. Allah bai halicci Lucifer a matsayin Iblis ba; Allah ya halicce shi nagari (Farawa 1:31).
Wajen kokarin fahimtar dalilin da yasa Allah ya halicci Shaidan, ya kuma san zai yi tawaye, bari mu duba wadannan abubuwa:
1) Lucifer yana da kyakkyawar manufa kafin faduwarsa. Tawayen Lucifer bai canza asalin shirin Allah daga wani abu mai kyau zuwa mara kyau ba.
2) Umarni na Allah ya kai ga shaidan, ko da ya fadi. Allah ya yi amfani da ayyukan mugunta na shaidan domin aiwatar da shirin Allah mai tsarki (duba 1 Timoti 1:20 da 1 Korantiyawa 5:5).
3) Shirin Allah na ceto ya yi shi ne tun farkon duniya (Wahayin Yahaya 13:8); ceto yana bukatar wani abu da za a yantar da kai daga shi, don haka Allah ya kyale shaidan ya yi tawaye ya kuma yada zuubi.
4) Wahalar da Shaidan ya kawo duniya ta zama hanya wadda ta wurin ta Yesu, a cikin jiki, ya zama cikakken Mai Ceton duniya: “Saboda haka, ya dace da Allah, shi da duk abubuwa suka kasance dominsa, ta gare shi ne kuma dukkan abubuwa suka samu, ya kamala shugaban cetonsu ta wurin shan wuya, a wajen kawo ya’ya masu yawa ga samun daukaka” (Ibraniyawa 2:10).
5) Tun daga farko, shirin Allah ga Kiristi ya hada da rushe aikin Shaidan (duba 1 Yahaya 3:8).
Daga karshe, ba za mu iya tabbatar da dalilin da yasa Allah ya halicci shaidan ba, ya san cewa zai yi tawaye. Zai zama gwaji idan za ka yi tuanin cewa da abubuwa sunfi tafiya “dai-dai” da ba a halicci Shaidan ba ko kuma ka ce da Allah ya yi wani abu da ban. Wannan tunanin na rashin hikima ne. A zahiri, idan muka ce mun fi Allah sanin yadda zai gudanar da yadda duniya za ta kasance fadawa ne cikin zunubin Iblis na daukaka kansa fiye da Madaukaki (Ishaya 14:13–14).
English
Idan Allah ya san cewa Shaidan zai yi tawaye, me yasa ya halicce shi?