Tambaya
Me ake nufi da Salama alaikum ya Maryamu da Katolika suke yawan fadi?
Amsa
Kalmar “Salama alaikum ya Maryamu,” Ave Maria a Latin, addu’a ce ta Katolika zuwa ga budurwa Maryamu da ta kunshi gaisuwa da kuma roko domin shiga tsakani. Akwai kuma jimlar "Hail Mary pass" wadda masu sharhi suka yi amfani da ita su bayyana wani fasin daga Dallas Cowboys quarterback Roger Staubach a 1975 wurin wasan share fage wanda ya zama sananne a kwallon kafa tare da wani dogon fasin da ya kai su ga nasara. Nassin a kan addu’a ta salama alaikum ya maryamu ya hada nassoshi guda biyu: “Salama alaikum yake zababbiya, Ubangiji yana tare da ke!”. (Luka 1:28) da kuma “Ke mai albarka ce a cikin mata, dan cikinki kuma mai albarka ne!” (Luka 1:42). Nassi na farko mala’ika Jibra’ilu ne yake gaishe da Maryamu sa’ad da ya zo ya gaya mata cewa an za be ta ta haifi mai Ceto. Na biyu yar uwarta ce Alisabatu take gaishe da Maryamu sa’ad da Maryamu ta ziyarci yar uawar ta ta, wadda ita ma take da cikin Yahaya Maibaftisma. Fanni na uku na addu’a r ta sallama ga Maryamu ba ta a Littafi Mai Tsarki, kuma tana sabani da gaskiyar Littafi Mai Tsarki: Ya Mai Tsarki, Maryamu uwar Allah, roka mana mu masu zunubi, daga yanzu da lokacin mutuwarmu. Amin.”
Wannan fannin na karshe na addu’a ga Maryamu yana da abubuwa uku da ba na Littafi Mai Tsarki ba ne. Na farko, Maryamu ba “Mai Tsarki” ba ce ba kuma ta taba zama ba. Maryamu mutum ce wadda aka haifa, kamar yadda kowane mutum yake, da gado na zunubi kuma wadda ta gane cewa tana bukatar Mai Ceto. A zahirin gaskiya ma, wannan nassin da aka yi amfani da shi a salama alaikum ya Maryamu, wanda aka sani da suna bangirma ga Maryamu (Luka 1:46-55), yana dauke da cewa “Allah Mai Cetona, da shi ruhuna yake farin ciki”, wannan ya bayyana cewa ta gane bukatar ta ta Mai Ceto daga zunubi. Littafi Mai Tsarki bai ce Maryamu wata ba ce amma mutum ce wadda Allah ya zaba ya yi amfani da ita ta hanya mai ban mamaki. I, Maryamu mace ce mai aminci kuma wadda ta sami tagoma shi (alheri) gun Allah (Luka 1:27-28). A lokaci guda kuma, Maryamu mutum ce mai zunubi wadda take da bukatar Yesu Kiristi a matsayin Mai cetonta, kamar kowa (Mai Hadishi 7:20; Romawa 3:23; 6:23; 1 Yahaya 1:8).
Fanni na biyu wanda ba na Littafi Mai Tsarki ba, a cikin salama alaikum ya Maryamu shi ne bayyana Maryamu a matsayin “Uwar Allah”. Maryamu uwar Yesu Kiristi ce ta jiki, wadda hakika Allah ya kasance cikinta. Amma ba Uwar Allah ba ce, kuma ba “sarauniyar sama ba ce”, wani sunan da aka bata daga Ikilisiyar Katolika wanda ba shi da dangantaka da Littafi Mai Tsarki. Allah ba shi da uwa, ba shi da sarauniya, ba shi da farko, ba halittar shi aka yi ba ba kuma haihuwarsa aka yi ba, mai dogara da kansa wanda kuma ya isarwa kansa.
Magana ta uku wadda bata a Littafi Mai Tsarki a cikin Salama alaikum ya Maryamu ita ce rokon ta ta yi mana “addu’a mu masu zunubi”. A nan, munga yin wani abu da ba shi a Littafi Mai Tsarki na addu’a ga Maryamu ta roka mana a zurin Allah. Na farko, ba ma bukatar wani tsakaicin tsakanin mu da Allah kuma. Kiristi shi kadai ne matsakancin da muke bukata. Ta wurin Yesu ta wurinsa kadai, muke da hanya zuwa zurin Uba. Kiristi kadai ne matsakaici tsakanin mutum da Allah. “Domin Allah daya ne, matsakaici kuma daya ne, tsakanin Allah da mutune, Almasihu Yesu, mutum.” (1 Timoti 2:5). Addu’a ga wani ban da Allah kin yarda da Littafi Mai Tsarki ne. addu’a ga Maryamu ko kuma rokonta ta yi mana yi mana addu’a sabanin Littafi Mai Tsarki ne. addu’a nau’I ne na sujada. Sa’ad da muka yi addu’a ga Allah, muna cewa muna bukatar taimakonsa ne. Yin addu’a ga wani ban da Allah kamar satar daukakar Allah ce wadda take tasa shi kadai, wani abu da Allah ba ya so kuma ba zai yarda da shi ba (Ishaya 42:8).
Saboda haka Maryamu budurwa ce mai aminci ga Allah wadda aka albarkace ta da cewa an zabe ta ta zama wadda za ta haifi Mai Ceton duniya, bata da Allahntaka ta kowace hanya, kada a ce bata da zunubi, ko a ce za a yi mata sujada daukaka, ko bangirma, ko kuma addu’a zuwa gare ta.
English
Me ake nufi da Salama alaikum ya Maryamu da Katolika suke yawan fadi?