Tambaya
Ko New World Translation sahihiyar fassara ce ta Littafi Mai Tsarki?
Amsa
New world translation (NWT) ya fito ne daga Jehovah's Witnesses’ parent organization (the Watchtower Society) Kamar yadda “Fassarar Litattafai Masu Tsarki ta samo asali kai tsaye daga harshen Ibranitanci, da Armaniyanci, da kuma Helinanci zuwa harshen Turanci da ake yi Yau ta wurin kwamatin Jehovah witness.” NWT Shi ne aikin “kwamatin fassarana yanzu (New World Bible Translation Committee.) Jehovah witness sun ce dalilin da yasa ba’a ambaci sunan wadanda suka yi aikin ba shi ne domin daukakar ta tafi zuwa ga Allah. Wannan yana da fa’idar kiyaye masu fassara daga duk wani abin da ya shafi kurakuran su da kuma hana manyan masanan bincikar takardunsu.
New World Translation ta sha dabam a abu daya – shi ne yunkuri na farko wajen kokarin a ga an samar da Littafi Mai Tsarki da aka bincika aka sake bincikawa domin wata manufa ta musamman don a yarda da shi. The Jehovah’s Witnesses da kuma Watchtower Society sun fahinci cewa imaninsu ya sha bamban da na Littafi Mai Tsarki. Don haka, maimakon yarda da abubuwan da suke a Littafi Mai Tsarki, sai suka juya Littafi Mai Tsarki ya yi daidai da abin da suka gaskata. Kwamatin fassarar Littafi Mai Tsarki na “New World Bible Translation” sun shiga cikin Littafi Mai Tsarki sun canza duk wani nassi da bai yarda da tauhidin Jehovah’s Witness ba. Wannan ya nuna a bayyane cewa yayin da aka yi sabbin bugu na New World Translation , an kara wasu canje canje a cikin Littafi Mai Tsarki. Yayin da Kirita masu karanta Littafi Mai Tsarki suka ci gaba da gano nassoshin da suke da mahawara da Allahntakar Kiristi (misali), Watchtower Society za su wallafa sabon bugu na New World Translation tare da nassoshin da aka canza. A nan ga wasu misalai na canje-canjen da ka yi da gangan:
New World Translation suka ba kalmar Helinanci ta staurós ("Gicciye") a matsayin "gungumen azaba" domin Jehovah’s Witnesses ba su gaskata da cewa a kan gicciye aka gicciye Yesu ba. The New World Translation ba ta fassara kalmar sheol, hades, gehenna, da tartarus a matsayin "jahannama” saboda Jehovah’s Witnesses basu gaskata da jahannama ba. The NWT sun ba da fassarar "kasancewa" maimakon “zuwa” na kalmar Helinanci parousia sabada Jehovah’s Witnesses sun gaskata da cewa Kiristi ya riga ya dawo a farkon 1900s. a Kolosiyawa 1:16, NWT sun sa ka kalmar “sauran” duk da ba ta gaba daya a cikin asalin rubutun na Helinanci. Sun yi wannan ne domin su bayyana cewa Kiristi ne ya halicci “dukan sauran abubuwa” maimakon abun da nassin ya fadi na cewa “Kiristi ne ya halicci dukan abubuwa.” Sun yi haka ne domin abun ya tafi dai-dai da abin da suka gaskata na cewa Kiristi halittar shi aka yi, sun gaskata haka ne domin sun karyata Uku cikin daya.
Abu sananne cikin dukan abubuwan da New World Translation suka canza shi ne Yahaya 1:1. Asalin kalmar ta Helinanci ita ce “kalmar nan kuwa Allah ne” NWT suka bayyan shi a matsayin “kalmar nan kuwa ta allah ce” wannan ba maganar dai-daitacciyar fassara ba ce, amma sa ka tauhidin wani a cikin nassi ne, maimakon barin nassin ya yi Magana don kansa. Ba kalma mara iyaka a harshen Helinanci (a Turanci, "a" ko "an"), don haka duk inda aka yi amfani da wannan kalma a Turanci mai fassarar ne ya kara ta. wannan shi ne abin da harshe ya amince da shi, idan dai bai canza ma’anar maganar ba.
Akwai kyakkyawan dalili da yasa theos ba ta da kalma mara iyakancewa a Yahaya 1:1 da kuma dalilin da ya sa abin da New World Translation suke bayyanawa ya zama kuskure. Akwai ka’ idoji guda uku da muke bukatar mu fahimta domin muga dalilin da yasa.
1. A Helinanci, abin da kalma take ba da umarni ba shi ke ba da amfanin kalmar ba kamar yadda yake yi a Turanci, A Turanci, ana tsara jimla ne bisa ga umarnin kalma: Abin da ake Magana akai – Aiki – kaya. "Harry ya kira kare" ba daya yake da "Kare ya kira Harry ba." Amma a Helinaci, amfanin kalma ya dangana ne da karshen abin ya yi dai-dai da farkon kalmar. Akwai abu biyu da yake karewa ga tushen kalmar theo: daya shi ne -s (theos), dayan kuma shi ne -n (theon). Karewa da -s yana bayyana suna a matsayin abin da ake Magana akai a cikin jimla, yayin da kuma karewa da –n yake bayyana kan suna a matsayin kayan kai tsaye.
2. Sa’ad da suna ya yi aiki a matsayin bayyanau (a Turanci, sunan da ya biyo baya ko aikatau kamar "is"), abin da ta kare da shi dole ya yi dai-dai da sunan da aka sake fadi, domin mai karatu yasan wane suna yake Magana akai. Don haka, theo dole ta dauki -s a karshe saboda tana sake fadar sunan logos. Don haka, Yahaya 1:1 muka fassara ta zuwa "kai theos en ho logos." ko theos shi ne abin da ake maga akai, , ko logos? Dukkansu suna da -s a karshe. Amsar za a same ta a ka’ida ta gaba.
3. A cikin al’amarin da suna biyu ya fito, kuma dukka suka kare da abu guda, marubucin zai kara da bayyanau ga kalmar wato abin da ake Magana akai domin gujewa rudani. Yahaya ya sa bayyanau a logos (“Kalmar”) maimakon a theos. Don haka, logos shi ne abin da ake Magana akai, kuma theos yake kara bayyana suna. A Turanci, wannan shi ne ya sa a cikin Yahaya 1:1 aka karanta ta a matsayin "kalman nan kuwa Allah ne" (maimakon "Allah shi ne kalmar").
Babbar shaida da ta bayyana ta Watchtower's bias ita ce gurbataccen tsarin fassararsu. Cikin duka Bishara ta hannun Yahaya, kalmar Helinanci theon ta bayyana ba tare da bayyanau ba. The New World Translation ba su bayyana ko daya daga ciki ba a matsayin “allah.” Ayoyi uku bayan wannan Yahaya 1:1, the New World Translation sun fassara wani al’amarin na theos ba tare da kalma mara iyaka a matsayin "Allah." Karin rashin dai-daito, a Yahaya 1:18, NWT sun fassara abu iri daya duka a matsayin "Allah" da kuma "allah" a jimla daya.
Don haka Watchtower, ba shi da wani abu mai wuya wajen fassara shi—abin da tauhidinsu ya yarda da shi ne kawai. Masu kare New World Translation za su iya yin nasara wajen nuna cewa Yahaya 1:1 an fassara ta yanda suka yi, amma ba za su iya nuna cewa daidaitacciyar fassara ba ce. Ba kuma za su iya yin gaskiyar bayanin cewa NWT bata fassara wata jimla ta Helinanci a wani wuri a cikin Bishara ta hannun Yahaya ta hanya iri daya ba. Kin yarda da Allahntakar Kiristi ce kadai ta tunzura Watchtower Society su yi gurbatacciyar fassara ta harshen Helinaci, suna sa kurakurensu su yi kama da na gaskiya a cikin zukatan wadan da basu san gaskiyar ba.
Abin da Watchtower's suka gada na abin da suka gaskata shi ne ya kawo wannan gurbatacciyar fassara ta kin gaskiya wadda ita ce New World Translation. The New World Translation ba sahihiyar fassarar Maganar Allah ba ce.
Akwai yan kananan bambance bambance tsakanin dukan fassarar Turanci ta Littafi Mai Tsarki. Ba wata fassara ta Turanci da take cikakka. Duk da haka, sauran masu fassarar Littafi Mai Tsarki sun yi yan kananun kurakurai wajen juya Helinanci da Ibraniyanci zuwa Turanci, su NWT cikin sani suka canza bayan nassi domin su yi daidai da tauhidin Jehovah’s Witness. The New World Translation rudarwa ce, ba fassara Littafi Mai Tsarki ba ce.
We highly recommend Witnesses for Jesus for more information.
English
Ko New World Translation sahihiyar fassara ce ta Littafi Mai Tsarki?