settings icon
share icon
Tambaya

Ko Maryamu uwar Allah ce (Theotokos)?

Amsa


Jimlar “uwar Allah” an kirkire ta ne an kuma cigaba da amfani da ita a Ikilisiyar Katolika. Daya daga cikin darusan majalissar Afisa a A.D. 431 an amfani ne da kalmar Helinanci Theotókos, ko “wadda ta haifi Allah”, suna nufin Maryamu. Wannan majalissa musamman suna kiran maryamu a matsayin “uwar Allah”, kuma ka’idar daga baya an sa ta cikin katikizim na Katolika. Dalilin kiran Maryamu “uwar Allah” shi ne, tunda Yesu Allah ne kuma Maryamu ita ce uwar Yesu, uwar Allah ce.

Babbar matsalar wannan salon ita ce kalmar “Allah” tana Magana akan Yahweh gaba daya, kuma mun san da cewa Yahweh ba shi da farko ba shi da karshe (Zabura 90:2). Timoti ta fari 6:15-16 ta ce Allah ba mutum ba ne. kasancewarsa ba mutum ba, Ba “haihuwar” Allah aka yi ba kuma ba shi da “uwa.” Na biyun Uku cikin daya, Yesu, yana da farko na aikinsa na duniya sa’ad da Maryamu ta dauki cikinsa a ka haife shi, amma tun farko Ya kasance Dan Allah.

Filibiyawa 2:6–7 ta ba mu Karin haske akan abin da ya faru sa’ad da Yesu ya bar sama domin ya zama mutum. Sabuwar Hausa ta ce, “Wanda ko da yake a cikin surar Allah yake, bai maida daidaitakar nan tasa da Allah a bar da zai rike kan kan ce ba. Sai ma ya maida kansa baya matuka ta daukar surar bawa, da kuma kasancewa da kamannin dan adam.” Yesu tunda daya yake da Uba, amma ya ajjiye surarsa ta Allahntaka ya dauki surar jariri (Yahaya 1:1). Ya zo ya cigaba da yin rayuwa ta yaro a Yahudiya, yana yi wa iyayensa na duniya biyayya (Luka 2:51).

Uwa bisa bayani tana gaban danta kuma a wani lokaci tana da karfi fiye da dan. To, kiran Maryamu “uwar Allah” ya ba da karkataccen bayani cewa Maryamu tana gaba kuma a wani lokaci tana da iko fiye da Uba madaukaki. Duk da tsarin Katolika ya so ya karyata haka, amma ba za a iya kaucewa hakan ba.

Littafi Mai Tsarki ne yake cewa da Maryamu uwar Ubangiji Yesu Kiristi a lokacin da aka haife shi a duniya. Duk da haka, Katolika sun gaskata da cewa wannan bai wadatar ba cewa Maryamu uwar Yesu. Fafaroma John Paul II, a maganarsa a 1996, ya karfafa mutane cewa “ba ma kawai a kira budurwa mai albarka a matsayin uwar Yesu ba, amma an kira ta uwar Allah” (L'Osservatore Romano, 4 Desamba 1996, p. 11). Wannan ba bisa Littafi Mai Tsarki ba ne. Ubangiji Allah madaukaki ba shida uwa, tun da ba shi da farko ba shi da karshe (Farawa 1:1; Wahayin Yahaya 4:8).

English



Koma zuwa shafin gida na Hausa

Ko Maryamu uwar Allah ce (Theotokos)?
© Copyright Got Questions Ministries