Tambaya
Ko Maryamu mai ceto ce / matsakanciya?
Amsa
Wasu yan Katolic din suna kallon Maryamu a matsatin Mai ceto (co-redemptrix) ko kuma matsakaiciya (mediatrix) wadda take taka rawar gani a ceton yan adam. (wadannan kalmomi na karshe -trix sunan mace ne yake karewa da haka a Latin, to redemptrix na nufin mace mai ceto, kuma mediatrix na nufin matsakaiciya mace.) A cikin Katolika, akwai kokari don bayyana sabuwar Marian dogma inda a maganar bangaskiya, Katolika za su yard aka ka’idoji uku: (1) Maryamu tana da sa hannu wajen ceto tare da Yesu Kiristi, (2) samun alheri gun Yesu sai da shiga tsakani na Maryamu, da kuma (3) dukkan addu’oin tsarkaka sai sun bi ta wurin Maryamu, wadda za ta kai su ga Danta. Aikata wannan zai canza uku cikin daya zuwa hudu.
Yarda da Maryamu a matsayin wadda za ta iya yin ceto zai zama kari a cikin koyarwar Katolika yanzu a kan Maryamu, wadanda suka ce Maryamu ta kasance da budurcinta har tsawon rayuwarta, cewa ba ta taba yin ma’amula ta jima’I da mijinta, Yusufu ba; da cewa ba ta da wasu ya’yan ban da Yesu;da kuma cewa ba ta da zunubi kuma an dauke ta zuwa sama. Wannan koyarwa ba ta Littafi Mai Tsarki ba ce; Littafi Mai Tsarki ya karya ta su a bayyane.
Maganar cewa Maryamu mai ceto ce ko kuma matsakaiciya ce ta sha bamban da 1 Timoti 2:5, wadda ta ce, “Domin Allah daya ne, matsakanci kuma daya ne, a tsakanin Allah da mutane, Almasihu Yesu mutum.” Yesu shi ne matsakanci. Ba wani matsakanci tsakanin mutum da Yesu. Yesu kansa yana cikin masu bi; ba wani da ake bukata (Kolosiyawa 1:27).
Yesu shi ne cikakke kuma matsakanci tsakanin mutum da Allah domin shi ne Dan Allah mara zunubi. Maryamu ta na da zunubi. Ba wata aya da ta goyi bayan cewa Maryamu ba ta da zunubi ko kuma daukar ta zuwa sama. Wannan dogma an amince ta shi ne sakamakon fadar papal. A cikin Littafi Mai Tsarki, an bayyana Maryamu a matsayin natsattsar mace mai biyayya da kuma mika kai, mai aminci ga Allah, tana bin hanyar abin da ke kokarin faruwa da ita, tana mika yabo da daukaka (Luka 1:46–55). Zahirin gaskiya, cikin Girmamawar ta, Maryamu ta ce, “Allah Mai Ceto na, da shi ruhu na yake ta farin ciki” (aya ta 47). Dalilin da yasa Maryamu ta kira Allah “Mai Cetonta”shi ne ta gane cewa tana bukatar Mai Ceto, Mai Yantarwa.
Yesu da kansa ya nuna cewa Maryamu ba ta da wani wuri na musamman da ya danganci Ceto ko tsayawa a tsakani. A cikin Matiyu 12:47–50, Maryamu da sauran ya’yanta suka zo suna son ganin Yesu sa’ad da yake koyarwa. “Wani ya ce masa, ‘Ga tsohuwarka da yan uwanka suna tsaye a waje, suna so su yi Magana da kai.’ Sai ya amsa wa wanda ya gaya masa, ya ce, wace tsohuwa ta, su wane ne kuma yan uwana? Sai ya mika hannuwa wajen almajiransa, ya ce, “ga tsohuwa ta da yan uwana nan! Ai kowa ya yi abin da Ubana da yake cikin sama yake so, shi ne dan uwana, shi ne yar uwata, shi ne kuma tsohuwata.”
Daga baya, a wurin gicciye, Maryamu uwa ce da ta yi bakin ciki. Ba ta sha wahala domin dukan yan adam ba; ta dai sha wahalarta ta yin bakin ciki. Tana daya daga cikin mutanen da za su sami Ceto daga Yesu, ba mai taimakawa aikinsa ba. Ta yi bakin ciki da dole ma sai da manzo Yahaya ya kula da ita.
Bayan mutuwar Yesu da tashinsa, Maryamu tana daga cikin al’ummar masu bi da suka cigaba da yin addu’a da roko kafin ranar fentikos (Ayyukan manzanni 1:14). Maryamu “mafi albarka ce a cikin mata” (Luka 1:42) domin ita ce uwar Mai Ceto. Amma ba ta da Allahntaka kuma ba za a dube ta a matsayin wani sashi na Uku cikin daya ba.
Ba ta cece mu daga zunubi ba kuma ba za ta kasance cikin hanya ta cetonmu ba.
English
Ko Maryamu mai ceto ce / matsakanciya?