Tambaya
Ko Yesu ya mutu?
Amsa
Shugabannin duniya da yawa sun bar abin da suka yi a litattafan tarihi. Manya manya a addinai sunyi kokari wajen gyara al’adu da tunani. Amma duk da abin da suka koyar, nasarar da suka yi, ko abin da suka yi imani, akwai abu daya da dukan su suka yi—dukansu sun mutu. Akwai lokacin da manyan mutane, da sarakuna, da kuma masana suka zo duniya akwai kuma lokacin da suka bar duniya. Za mu iya ziyartar kabarin su ko wurin tuna wa da su, kuma har yanzu gawawwakinsu ko kasusuwansu suna nan. Kowane shugaba, ko annabi, ko kuma sarki sun mutu ko kuma za su mutu, idan suka mutu, shikenan, sai su fuskanci shari’ar Allah kamar sauran mutane (Ibraniyawa 9:27; 2 Korantiyawa 5:10)—ban da guda daya. Yesu Kiristi, wanda a gare shi ne dukan tsarin mutuwa na duniya yake, bai mutu ba.
Domin shi ba mutum ba ne kamar kowa, Yesu bai kasance na wani lokaci ba ne. yana nan da ma a matsayin dan Allah (Yahaya 1:1–5; 8:58). Ya zabi ya bar sama ya shigo wannan d uniya a cikin siffar jariri (Luka 1:35; Filibiyawa 2:5–8). Kuma, koda yake uwarsa mutum ce, Ubansa Allah ne. Yesu Allah ne cikakke kuma mutum ne cikakke ya bar wannan rayuwar ta duniya domin ya zama matsakaici tsakanin mutum mai zunubi da mahalicci Mai Tsarki (1 Timoti 2:5). An jarabce shi kamar yanda aka yi mana, amma bai yi zunubi ba (Ibraniyawa 4:15). A kowane lokaci yana yin abin da Uba yake so (Yahaya 8:29; 14:31). Kuma sa’ad da lokaci ya yi, ya ba da kansa a matsayin hadaya ta karshe domin zunubanmu (Yahaya 10:18; 2 Korantiyawa 5:21).
An kama Yesu an gwada shi domin ya ce shi Allah ne (Yahaya 5:18; 10:33). Sun gicciye Shi kamar yadda aka yi annabci a Zabura 22 da Ishaya 53 (Luka 22:37). Aka gicciye shi a kan gicciye, Yesu ya zama kowane zunubi da yan adam suka yi (2 Korantiyawa 5:21; 1 Yahaya 2:2). Ya biya cikakken hukunci da Allah zai mana domin mu zama adalai a kuma gafarta mana. Sa’ad da ya ce, “An gama!” (Yahaya 19:30), ba yana Magana akan rayuwarsa ta duniya ba ne, saboda ya riga ya gayawa mabiyansa cewa Allah zai tashe Shi daga matattu a rana ta uku (Markus 9:31; 10:33–34). Yana nufin shirin ceto mutum kasasshe, wanda Shi da Uba suka sani tun farko, an gama shi yanzu (1 Bitrus 1:18–20; Ayyukan manzanni 2:23; Afisawa 1:4). Hakika Yesu ya mutu a jiki ya tsaya a matacce na tsahon kwana uku.
An binne Yesu a kabari na aro, domin ba zai buka ce shi na tsawon lokaci ba (Matiyu 27:59–60). Shugabannin Romawa sun rufe kabarin da hatimi da kuma babban dutse, suka sa ya zama kusan ba zai budu ba. An kuma sa matsara su tsare don tsoron ka da almajiransa su zo su sace jikinsa su ce ya ta shi kamar yadda ya alkawarta (Matiyu 27:62–66). Kowa ya san da abin da Yesu ya fada, duk da ba wanda ya fahimci asalin abin da yake nufi (Markus 9:31–32). Matsaran, Karin tsaro ne da shugabannin Yahudawa suka bukata domin kokarin kawo karshen sabuwar koyarwar da Yesu Banazaret ya gabatar a cikin al’adarsu. Sun gano cewa, idan shugaban ya mutu kuma bai tashi ba, zuciyar mabiyansa za ta mutu kuma abubuwa za su koma yadda suke a da.
Da abubuwa sun masu daidai idan da Yesu ya tsaya a kabari. Idan da Yesu bai ta shi daga matattu ba, da bai zama da bam daga sauran manyan malamai ba. Bulus ya rubuta a 1 Korantiyawa 15:14 cewa, “in kuwa ba a ta da Almasihu ba, to, ashe, wa’azinmu a banza ne, bangaskiyarku kuma banza ce.” Sai a aya ta 17–19 ya rubuta, “In kuwa ba a ta da Almasihu ba, ashe, bangaskiyarku banza ce, har yanzu kuma kuna tare da zunubanku. Ashe, wadanda suka yi barci akan su na Almasihu, sun hallaka kenan. Da begenmu ga Almasihu domin wannan rai ne kadai, ai, da munfi kowa zama abin tausai.”
Amma Yesu bai tsaya a matacce ba. A rana ta uku, kamar yadda ya ce, ya fito daga kabarin (Matiyu 28:2–10; Markus 16:4–7; Luka 24:1–8; Yahaya 20:1–8, 19). Sai mala’ika ya kawar da matsaran, ya mirgine dutsen daga kabarin ya zauna kai, yana jiran abokan Yesu su zo (Matiyu 28:2; Yahay 20:1, 11–12). Cikin kwana arba’in Yesu ya bayyana ga fiye da mutum dari biyar (1 Korantiyawa 15:3–7), yana bayyana cewa shi ne, kuma a raye cikin jiki (Luka 24:36–42). Sai aka dauke shi zuwa sama akan idon almajiransa (Luka 24:51; Ayyukan manzanni 1:9–11).
Yesu yana raye kuma yanzu yana zaune a hannun dama na Uba (Ibraniyawa 1:3). Tun da yake “kullum a raye yake” saboda yi wa mutanensa addu’a (Ibraniyawa 7:25) kuma ya yi alkawarin cewa zai sake dawowa (Yahaya 14:3; Wahayin Yahaya 22:2). Ya jure rabuwa da Allah (Matiyu 27:46) to ba ma bukatar mu yi nasara da mutuwa kuma (1 Korantiyawa 15:55). Ya bambanta kansa daga sauran shugabanin addinai saboda ba wani kabari da sunansa ne akai. Dan Allah ne kadai zai iya mutuwa domin zunuban duniya ya kuma tashi daga matattu. Saboda tashinsa daga matattu, duk wanda ya gaskata da shi zai sami bege makamancin na tashi daga matattu. Yesu bai mutu ba, kuma saboda yana raye, za mu iya yin madawwamiyar rayuwa tare da Shi (Yahaya 3:16–18; 14:19).
English
Ko Yesu ya mutu?