Tambaya
Ko Yesu Dan Allah ne? Ta yaya Allah, da yake shi kadai, zai sami da?
Amsa
Musulmi suka yi tambaya, “Ta ya ya Allah, da yake shi kadai, zai sami da?” Rashin fahimtar Uku cikin daya, wasu lokutan suna kalubalantar Kirista da bautawa Allah uku. Duk da haka, Kiristoci sun gaskata da cewa Allah na gaskiya daya ne.
Yesu kansa ya goyi bayan cewa Allah daya ne. Da aka tambaye shi game da babban umarni, sai ya ce, “. . . Ubangiji Allahnmu, Ubangiji daya ne. Sai ka kaunaci ubangiji Allahnka da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka, da dukkan hankalinka, da kuma dukan karfinka” (Markus 12:29-30).
Yesu ya koyar da cewa Allah daya ne, kuma Yesu ya koyar da cewa Shi daya ne da Allah (Yahaya 10:30). Don haka, Yahudawa suka dauki duwatsu za su jejjefe Yesu saboda suna tunanin ya aikata laifin sabo. Makamancin haka, Musulmi suna cewa idan mutum ya ce shi Allah ne ya yi “Shirka.” Duk da haka, Yesu ba mutum bane da yake cewa shi Allah ne. Shi Dan Allah ne a da jikin mutum (Yahaya 10:36-38).
Sunan na “Dan Allah” ba yana nufin Allah shi ne ya haifi Yesu ba. Littafi Mai Tsarki bai koyar da mu’amula ta jiki tsakanin Allah da Maryamu ba, kamar yadda wasu lokutan Musulmi suke kalubalanta. A haihuwar Yesu, mala’ikan ya cewa budurwa Maryamu:
“. . . ‘Kada ki ji tsoro, Maryamu, kin sami tagomashi a wurin Allah. Ga shi kuwa za ki yi ciki, ki haifi da, ki kuma sa masa suna Yesu. Zai zama mai girma za a kuma kira shi dan madaukaki. . . . mulkinsa kuwa ba shi da matuka.’ Sai Maryamu ta ce wa mala’ ikan, ‘kaka wannan zai yiwu, tun da yake ba a kaini daki ba?’ Sai mala’ ikan Allah ya ce, ‘Ruhu Mai Tsarki zai sauko miki, Ikon Madaukaki zai lullube ki. Saboda haka Mai Tsarkin nan da za a haifa, za a kira shi —Dan Allah’” (Luka 1:30-35).
Pastor John MacArthur ya yi bayani akan wadannan ayayoyin: “Tunda ɗan yana da abubuwa irin na Uba, kiran shi dan wani mutum hanya ce ta nuna daidaito. Anan mala’ ikan yana gayawa Maryamu cewa Danta zai kasance daidai da Allah Madaukaki” (The MacArthur Study Bible).
Shada ta mutum ta cewa Yesu Dan Allah ne
Sa’ad da mutane suka ga al’ajaban Yesu, da koyarwarsa, da mutuwarsa, da tashinsa daga matattu, da kuma tafiyarsa zuwa sama, da yawa sukan gaskata da cewa Yesu Dan Allah ne.
• Mabiyan Yesu sun shaida bayan ya tsawatawa iska mai karfi: “Da suka shiga cikin jirgi iskar ta tsaya. Wadanda suke cikin jirgin suka yi masa sujada, suna cewa, ‘Lalle kai Dan Allah ne’” (Matiyu 14:32-33).
• Bitrus ya shaida: “To, da Yesu ya shiga kasar Kaisariya ta Filibi, sai ya tambayi almajiransa ya ce, ‘Wa mutane suke cewa, Dan mutum yake?’ Sai suka ce, ‘Wadansu suna cewa, Yahaya Maibaftisma, wadansu kuma Iliya, wadansu kuma Irmiya, ko kuwa daya daga cikin annabawa.’ Ya ce musu, ‘Amma ku fa, wa kuke cewa nake?’ Sai Bitrus ya amsa ya ce, ‘Kai ne Almasihu Dan Allah Rayayye.’ Yesu ya amsa ya ce, ‘Kai mai albarka ne Saminu, dan Yunusa! Domin ba dan adam ne ya bayyana maka wannan ba, sai dai Uba da yake a cikin sama (Matiyu 16:13-17).
• Matar da, Yesu ya tada dan’uwanta daga matattu, ta shaida: “Yesu ya ce mata, ‘Ai, Ni ne tashin matattu, ni ne kuma rai. Wanda ya gaskata da ni, ko ya mutu zai rayu. Wanda kuma yake raye, yake kuma gaskatawa da ni, ba zai mutu ba har abada, kin gaskata wannan?’ Ta ce masa, ‘I, ya Ubangiji, na gaskata kai ne Almasihu, Dan Allah, shi wannan mai zuwa duniya’” (Yahaya 11:25-27).
• Ko aljanu ma sun san Yesu Dan Allah ne: “Bakaken aljanu kuwa, duk sa’ad da suka gan shi, sai su fadi gabanh sa suna kururuwa, suna cewa, ‘Kai Dan Allah ne.’” (Markus 3:11).
• Sojoji masu tsaron tsaron Yesu sa’ad da zai mutu a kan gicciye sun shaida:: “Sa’ad da jarumin da wadanda suke tare da shi suna tsaron Yesu suka ga rawar kasa da kuma abin da ya auku, sai duk tsoro ya kama su, suka ce, ‘Hakika wannan Dan Allah ne!’” (Matiyu 27:54).
• Toma ya shaida bayan tashin Yesu daga matattu: “Toma kuwa, ɗaya daga cikin goma sha biyun nan, wanda ake kira Ɗan Tagwai, ba ya nan tare da su sa'ad da Yesu ya zo. Sai sauran almajiran suka ce masa, “Mun ga Ubangiji.” Amma ya ce musu, “In ban ga gurbin ƙusoshi a hannuwansa ba, in sa yatsata a gurbin ƙusoshin, in kuma sa hannuna a kwiɓinsa ba, ba zan ba da gaskiya ba.”
Bayan kwana takwas har wa yau almajiransa na cikin gidan, Toma ma yana nan tare da su, ƙofofi suna kulle, sai ga Yesu ya zo ya tsaya a tsaka, ya ce, “Salama alaikun.” Sa'an nan ya ce wa Toma, “Sa yatsanka nan, ka ji hannuwana. Miƙo hannunka kuma ka sa a kwiɓina. Kada ka zama marar ba da gaskiya, sai dai mai ba da gaskiya.” Toma ya amsa masa ya ce, “Ya Ubangijina Allahna kuma!” Sai Yesu ya ce masa, “Wato saboda ka gan ni ka ba da gaskiya? Albarka tā tabbata ga waɗanda ba su gani ba, amma kuwa suka ba da gaskiya.” Yesu ya yi waɗansu mu'ujizai da yawa dabam dabam a gaban almajiran, waɗanda ba a rubuta a littafin nan ba. Amma an rubuta waɗannan ne, domin ku ba da gaskiya Yesu shi ne Almasihu, Ɗan Allah, ta wurin gaskatawa kuma ku sami rai a cikin sunansa.” (Yahaya 20:24-31).
Shaidar Yesu ta cewa Shi Dan Allah ne
• “Don haka, Yahudawa suka ƙara nema su kashe shi, ba don ya keta Asabar kaɗai ba, har ma domin ya ce Allah Ubansa ne, wato, yana daidaita kansa da Allah.
Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Lalle hakika, ina gaya muku, Ɗan ba ya yin kome shi kaɗai, sai abin da ya ga Uba yana yi. Domin duk abin da Uban yake yi, haka shi Ɗan ma yake yi. Domin Uban na ƙaunar Ɗan, yana kuma nuna masa duk abin da shi kansa yake yi, har ma zai nuna masa ayyukan da suka fi waɗannan, domin ku yi al'ajabi. Yadda Uba yake ta da matattu ya kuma raya su, haka Ɗan ma yake rayar da wanda ya nufa. Uba ba ya hukunta kowa, sai dai yā danƙa dukkan hukunci ga Ɗan, domin kowa yă girmama Ɗan, kamar yadda ake girmama Uban. Wanda ba ya girmama Ɗan, ba ya girmama Uban da ya aiko shi ke nan. Lalle hakika, ina gaya muku, duk mai jin maganata, yake kuma gaskata wanda ya aiko ni, yana da rai madawwami. Ba za a yi masa hukunci ba, domin ya riga ya tsere wa mutuwa, ya kai ga rai’” (Yahaya 5:18-24).
• Yesu wajen gwada shi, ya shaida: “. . . Sai babban firist ɗin ya sāke tambayarsa, “To, ashe, kai ɗin nan ne Almasihu Ɗan Maɗaukaki?” Yesu ya ce, “Ni ne. Za ku kuwa ga Ɗan Mutum zaune dama ga Mai Iko, yana kuma zuwa cikin gajimare.’” (Markus 14:61-62).
• “Mun kuma sani Ɗan Allah ya zo, ya yi mana baiwar fahimta domin mu san shi wanda yake na gaskiya. Mu kuwa muna a cikinsa, shi da yake na gaskiya, wato Ɗansa Yesu Almasihu. Shi ne Allah na gasikya da kuma rai madawwami” (1 Yahaya 5:20).
Shaidawar Allah ta cewa Yesu Dansa ne
• Allah ya yi Magana a wurin baftismar Yesu: “Wannan shi ne Dana kaunataccena, wanda nake farin ciki da shi kwarai” (Matiyu 3:17).
• “Yana faɗar haka sai wani gajimare ya zo ya rufe su. Da kuma gajimaren ya lulluɓe su suka tsorata. Sai aka ji wata murya daga cikin gajimaren, tana cewa, “Wannan shi ne Ɗana zaɓanɓɓena. Ku saurare shi!” (Luka 9:34-35).
• “Tun da yake muna yarda da shaida mutane, ai, shaidar Allah ta fi ƙarfi. Wannan ita ce shaidar Allah, wato, ya shaidi Ɗansa. Kowa ya gaskata da Ɗan Allah, shaidar tana nan gare shi. Wanda bai gaskata Allah ba, ya ƙaryata shi ke nan, domin bai gaskata shaidar da Allah ya yi Ɗansa ba. Wannan kuma ita ce shaidar, cewa Allah yā ba mu rai madawwami, wannan rai kuwa yana cikin Ɗansa. Duk wanda yake da Ɗan, yana da rai. Wanda ba shi da Ɗan Allah kuwa, ba shi da rai. Na rubuto muku wannan ne, ku da kuka gaskata da sunan Ɗan Allah, domin ku tabbata kuna da rai madawwami.” (1 Yahaya 5:9-13).
• A zamanin dā, Allah ya yi wa kakannin kakanninmu magana ta hanyoyi masu yawa iri iri, ta bakin annabawa, amma a zamanin nan na ƙarshe, sai ya yi mana magana ta wurin Ɗansa, wanda ya sa magājin kome, wanda ta wurinsa ne kuma ya halicci duniya. Shi ne hasken ɗaukakar Allah, ainihin kamannin zatinsa kuma, shi kuma yana a riƙe da dukan abubuwa ta ikon faɗarsa. Bayan da ya tsarkake zunubanmu, sai ya zauna a dama da Maɗaukaki a can Sama. (Ibraniyawa 1:1-3).
Yesu shi ne “asalin bayyanar” Allah. Duk da daya yake da Ubansa a asali, Yesu ya bayyana a cikin jiki a matsayin Dan Allah. Allah ya bayyana kansa a matsayin Allah daya, da ya bayyana a matsayin uku, Uba, da Da, da Ruhu Mai Tsarki.
Tun kafin duniya farkon duniya, Yesu yana tare da Allah kuma shi Allah ne (Yahaya 1:1-2; 17:5). Allah ya halicci dukan komai a duniya ta wurin Yesu (Yahaya 1:3; Kolosiyawa 1:15-20).
Duk da har abada daya yake da Allah, Yesu ya zo duniya cikin siffar mutum (Filibiyawa 2:5-11). Budurwa Maryamu ta haife shi, Yesu Allah ne cikakke Mutum ne cikakke kuma a lokaci guda (cikin jiki: Matiyu 1:22-23; Yahaya 1:14; Romawa 1:3-4; Kolosiyawa 2:9; 1 Yahaya 4:1-3; 5:20).
Gaskatawa da Dan Allah
Dole mu gaskata da maganar Allah cewa Yesu Dan Allah ne, duk da abin yana da wuyar fahimta. Zamu mutu da tambayoyi masu wuya da ba a amsa ba. Amma kada mu sake mu mutu ba tare da ansar alkawarin Allah na shari’ a da ceto ta wurin Dansa (Yahaya 3:35-36; 5:25-29; Ayyukan Manzanni 10:38-43; 17:30-31; 1 Yahaya 4:14-15).
A matsayin Dan Allah mara aibi, Yesu bai cancanci hukuncin zunubi ba, wato mutuwa (Romawa 6:23). Amma ta wurin mutuwarsa kan gicciye da kuma tashinsa daga matattu, Yesu ya biya hukunci zunubi ya kuma karya ikon zunubi ga wadanda suke nasa (Romawa 8:1-3).
Allah yana kiran masu zunubi su juyo daga zunubansu su bi Ubangiji Yesu rayayye cikin tuba da kuma bangaskiya (Luka 24:46-47). Ba za mu iya ceton kanmu ba. wadanda suka juyo daga zunubi ne kadai suka yarda da Dan Allah aka cece su daga zunubi da kuma mutuwa ta har abada.
“Saboda kaunar da Allah ya yi wa duniya har ya ba da makadaicin Dansa, domin duk wanda ya ba da gaskiya da shi kada ya hallaka, sai dai ya sami rai madawwami. Gama Allah bai aiko Dansa duniya domin ya yanke mata hukunci ba, sai dai domin duniya ta sami ceto ta wurinsa. Duk wanda ya gaskata da shi, ba za a yi masa hukunci ba. Wanda kuwa bai gaskata ba, an riga an yi masa hukunci, domin bai gaskata da suna makadaicin Dan Allah ba.” (Yahaya 3:16-18).
Ta wurin karanta wadannan bayanai, ka yarda da Yesu a matsayin Mai Cetonka daga zunubi da kuma jagoran rayuwarka? Idan haka ne, ka danna “Na karbi Kiristi yau” a wurin dannawa na kasa.
English
Ko Yesu Dan Allah ne? Ta yaya Allah, da yake shi kadai, zai sami da?