Tambaya
Idan Allah kauna ne, me yasa ya hana luwadi?
Amsa
Muhawarar da a ka fi yi game da amincewa da luwadi da kuma auren jinsi ita ce, idan Allah kauna ne, ba zai hana kaunar wasu ba. Asalin matsalar a nan ita ce wa ce irin “kauna” muke Magana.
Yahaya ta fari 4:8 ta ce, “Wanda baya kauna, bai san Allah ba sam, domin Allah shi ne kauna.” “Kaunar” da a ke nufi a nan ita ce wadda a ke kira da harshen Helinaci agape. Irin wannan kaunar ita ce ta sadukar da abin da ka ke so, da jin dadinka, dama zaman lafiyarka domin wani. Ita ce kaunar da ta kai Yesu ya mutu a kan gicciye domin zunubanmu (Romawa 5:8). Da kuma kaunar da ta sa Allah ya aiko Shi (Yahaya 3:16). Ba kaunar da tafi haka ga mutane, wato mutum ya ba da ransa saboda aminansa (Yahaya 15:13).
Sai kuma tambayar ta koma, mene ne zaman lafiyar wani ta kunsa? Duniya da tunaninmu ma zai iya cewa barin wani ya kasance cikin ludu da madigo ma domin son zaman lafiyarsa ne. Littafi Mai Tsarki ya fadi akasin haka. Romawa 1:26 ta ce abin kunya ne da abin kyama. Korantiywa ta fari 6:9 ta ce zai hana mutum shiga mulkin Allah. Korantiyawa ta fari 6:18 ta ce mai yin fasikanci yana daukar alhakin kansa ne.
Idan gaskiya ne halin luwadi abin kyama ne, rabuwa ce da albarkar Allah, kuma cutar da kai ne, to yin kaunar shi ne ka guje ma shi. Karfafa mutane su kasance cikin zunubi karfafa sune su ki albarkun Allah a rayuwarsu. Wannan kuwa kishiyar kauna ce.
Wannan ya nuna cewa, wadanda suke da sha’awar luwadi suna cikin muguwar sha’awace ta kauna. Ko da a ce sun amince da Littafi Mai Tsarki cewa luwadi zunubi ne suka kuma yanke cewa ba za su nemi gamsarwa daga sha’awoyinsu na jima’I ba, za su sami kauna ta wata dangantakar—kauna ta sadaukarwa ta agape da kuma ta abokantaka ta phileo. Sa’ad da aka biya bukatar zuciyarmu da kuma na zamantakewa, za mu sami karancin neman gamsarwa wadda ba ta hanyar Littafi Mai Tsarki ba. Ba wani bambanci da sha’awar wadanda basu yi aure ba masu sha’awar jinsin da ba na su ba da kuma sha’awar wadanda suke luwadi.
Ko wandan yake da sha’awar jima’I da jinsinsa zai iya warkewa ya koma yana tunani, da marmari da kuma aikata abin da masu jima’i da jinsin da ba na su ba suke yi? Abu mai yiwuwa ne, amma ba tabbas. Ceton ka da kuma gafarta maka baya cire ka daga gwaji. Ga masu bi, idan dai sha’awa ta jinsi guda ta zo, kamewa tana da matukar mahimmanci—kamar yadda yake ga duk wanda yake cikin aure na jinsin da ba na shi ba, ko da suna nuna kauna ta agape da kauna ta phileo.
Karya ne cewa dukkan mutane suna bukatar gamsarwa ta jima’I (Matiyu 19:12). Karya ne cewa jima’i daya yake da kauna. Allahn da ya halicce mu ya ce jima’I bayyana kauna ce tsakanin mace da namiji wadanda suka aure junansu. In ba cikin haka ba kuwa, jima’I yana da illa kuma rashin kauna ne. idan muna kaunar wasu, ba za mu karfafasu su yi zunubi ba, su illatar da kansu. Maimakon haka, za mu bi babban umarni mu kuma tabbatar ma su asalin kaunar da suke bukata daga garemu.
English
Idan Allah kauna ne, me yasa ya hana luwadi?