settings icon
share icon
Tambaya

Ta yaya Yesu ya zama Allah, bayan Littafin Kidaya 23:19 ya ce Allah ba mutum ba ne ko dan mutum?

Amsa


Wasu suna cewa Tsohon Alkwari ya tabbatar da cewa Yesu ba zai zama Allah ba saboda Littafin Kidaya 23:19a, da ya ce, “Allah ba kamar mutum ba ne da zai yi karya, Ba kuwa dan mutum ba ne, da zai tuba” (KJV). Dalilin shi ne, idan Allah ba mutum ba ne, to abin da Kirista suke cewa na Yesu, mutum, Allah ne karya ne. kamar yadda masu kokarin kawo rudani suke cewa gaskiya ne Yesu ya kira kan shi “Dan Mutum” sau da yawa a cikin bisharu (misali., Markus 14:21).

Tsohon Alkawari ya koyar da cewa Allah ba mutum ba ne, ba a Littafin Kidaya 23:19 kai dai ba, amma har a 1 Sama’ila 15:29 da Yusha’u 11:9. Duk da haka, Sabon Alkawari ya nuna mana cewa Yesu ya ce shi Allah ne—kuma a lokaci guda Ya kira Kansa “Dan Mutum,” sunan da yake nuna kasancewarsa a mutum. Idan duka wadannan gaskiya ne, ta ya ya zamu ba da hujjar cewa Yesu Allah ne?

Yesu ya ce shi Dan Allah ne da kuma Dan Mutum duka. Ba wani rudani a nan. Ya ce shi Allah ne, kuma ya ce Shi (a lokaci guda) mutum ne. ba wanda ya taba fadin wani abu makamancin wannan a baya. abin mamaki ne a yanzu—abin mamaki ne ga wanda bai taba jin haka ba, kasancewar Allah da mutum a wuri daya (hypostatic union). Ba wanda zai iya cikakkar fahimtar dayantuwar Kiristi Allah da kuma zama mutum, ko da ya ya za muyi magana akan haka, ko bayani, ko kuma misalta haka. saboda haka, “hujja” ba za ta iya isa ba. Ko dai mu gaskata da Yesu, ko mu ki.

Abu mai wuya ne a gane a wannan wurin cewa Littafi Mai Tsarki gaskiya ne ciki da waje (in toto)—duka Tsohon Alkawari da Sabon Alkawari. Sa’ad da Yesu ya fara koyar da sababbin abubuwa, tsofaffin ba sun zama karya ba kenen; sun zama bayyanannu. Ku tuna abin da ya ce game da Doka: “Kada ku yi zaton na zo ne in shafe Attaura da koyarwar annabawa. Na zo ne ba domin in shafe su ba, sai dai domin in cika su” (Matiyu 5:17). Dukan sabon wahayin aikin Yesu duk iri daya ne. tsohon sanin a duhu yake, kuma, a matsayin hasken duniya, Yesu ya kori duhu (duba Kolosiyawa 2:16–17). Wannan koyarwar ba shefe tsohon sanin take ba—tana cika shi ne, kamar haduwar Filibus da mutumin Habasha (Ayyukan manzanni 8:30–35).

Dole kuma mu yi la’akari da abin da Tsohon Alkawari yake cewa game da Allah sa’ad da yake cewa shi ba mutum ba ne. maganar da aka yi a Littafin Kidaya 23:19, 1 Sama’ilal 15:29, da Yusha’u 11:9 ita ce Allah ba ya karya. Ba ya canza wa. Yanda yake ji a zuciyarsa baya canza manufofinsa na har abada. Ba kamar mutum mai kasawa ba, wan baya iya ganin babban hoto, wanda yake yawan karya alkawari, kuma wanda abin da yake ji da shi yake yanke hukunci. A wani bangaren, maganar cewa Allah ba mutum ba ne tana bambance bangare daya na halin Allah da kuma bangaren da ya da ce da mutum. Cewa, “Allah ba mutum ba ne”, ba shi da wata alaka da cewa Allah zai kasance ko ba zai kasance a cikin jiki ba.

Abin da Tsohon Alkawri yake magana kan kasancewar Allah ba kamar mutum ba, ba yana magana akan irin zama mutum din da Yesu ya yi ba. Abin da ake gaya mana kawai shi ne, Allah ba mutum ba ne kamar yadda mutuane ke tunani. Misali ne, ba kayyadewa ba ne. Ba abin da zai hana Allah zama mutum a wata hanyar da ban—a zahiri, Ceto yana bukatar haka, kuma ceto shirin Allah ne tun kafin a kafa duniya (Wahayin Yahaya 13:8). Wato, za a iya cewa Allah ya san Zai zama mutum tun kafin a shirya Littafin Kidaya 23:19!

Idan muka yi la’akari da Tsohon Alkawari shi kadai (wanda fanni ne na Yahudanci), ba lallai mu iya ba da “ hujja” cewa Kiristi mutum ne, Allah ne, Almasihu ne, kuma Mai Ceto—duk da wadanda suka bayyana suna nan (duba Ishaya 53, misali). Kirista suna ganin misalin na Allah-mutum a cikin Tsohon Alkawari saboda wahayin Sabon Alkawari ya taimaka ya fassara abin da Tsohon Alkawari yake nufi (miasali., Matiyu 2:15; cf. Yusha’u 11:1). Wannan ya nuna mana gaskiyar mahimmanci game fassara Littafi Mai Tsarki: Allah yana cigaba da bayyana gaskiya, haryanzu. Yana cika manufarsa daki da daki kuma kamar yadda ake bukata a cikin shekaru masu yawa.

Misali, Adamu da Hauwa’u sa’ad da basu da zunubi ba su da bukatar sani game da Mai Ceto, amm bayan sun yi zunubi, daga nan lokacin ya yi, kuma Allah ya bayyana masu a Farawa 3:15 wannan wahayin an ba da shi a daidaitaccen lokaci, kuma Allah ya bayyana shi bayan Kiristi ya zo a cikin jiki—kuma sa’ad da marubutan Sabon Alkawari suke rubutawa karkashin izawar ruhu Mai Tsarki. Yanzu Sai muka gane cewa Farawa 3:15 tana Magana ne kai tsaye akan mutuwar Yesu domin kaffara—kuma wannan wahayin ya zama wajibi gare mu a yau. Amma wannan sakon ba domin Adamu da Hauwa’u ba ne. rashin saninsu kafin su fadi. Zamansu a cikin rashin sani, ya fi ye masu da di.

Kamar haka, Allah yana cigaba da bayyana nufinsa ga mutanensa a Tsohon Alkawari, kuma wadannan mutane aikinsu ne su yi rayuwa ta biyayya bisa ga iya lokacin wahayin da aka ba su. A yau, duka maganar Allah ta wajaba ne a kan Kirista saboda mu muna rayuwa a lokacin da take cikakka. Kari akan haka, masu bi suna da Ruhu mai Tsarki da yake a cikinsu, to ba wata hujja ta kin yarda da Yesu Kiristi a matsayin Allah.

Tun da wahayi cigaba yake yi, amincewar mutum game da Allah ta danganta ga lokacin da yake. Bayahude na Tsohon Alkawari ba zai san bayanin Allah mutum ba, duk da akwai alamu (irin su Zabura 110:1) sun kasance. Amma Annabce annabcen Yahaya Maibaftisma, a ka zo kan mu’ujizan Yesu, da sauran wahayi. A zahiri, mu’ujizan Yesu shaidu ne na tabbatar da ko shi wane ne: “Yesu ya yi wadansu mu’ujizai da yawa dabam dabam a gaban almajiransa, wadanda ba a rubuta a Littafin nan ba. Amma an rubuta wadannan ne, domin ku ba da gaskiya Yesu shi ne Almasihu, Dan Allah, ta wurin gaskatawa kuma ku sami rai a cikin sunansa” (Yahaya 20:30–31). Mutane a yau har yanzu suna bukatar su amince cikin bangaskiya ga mu’ujizan Yesu. wadanda ba su amince ba makafi ne a bangaskiya.

A karshe, Allah ya ce Shi ba mutum ba ne kuma Yesu ya ce Shi Dan Allah ne da ya kasance gaskiya; ba rikici suke ba. wahayi yana ci gaba, kuma abubuwan Tsohon Alkawari an fadada su a Sabon Alkawari. A karshe, Allah ya sani a zuciyarsa cewa Dan zai zama jiki ya kuma zauna cikin mutane, Allah bai ta ba “canza zuciyarsa” ba game da zama mutum.

English



Koma zuwa shafin gida na Hausa

Ta yaya Yesu ya zama Allah, bayan Littafin Kidaya 23:19 ya ce Allah ba mutum ba ne ko dan mutum?
© Copyright Got Questions Ministries