settings icon
share icon
Tambaya

An ceta gaba ɗaya, an ceta koyaushe?

Amsa


Muddar an cece mutum an cece shi ke nan koyaushe? Sa’anda mutane sun zo ga sanin Kiristi a matsayin mai ceton su, an kawo su cikin dangantaka tare da Allah mai bada tabbaci ceton su amana ce madawwamiya. Nassoshin Littafi Mai Tsarki da yawa sun furta wannan gaskiya. (a) Romawa 8:30 tayi shela, “Waɗanda ya ƙaddara nan kuwa, sune ya kira. Waɗanda ya kira kuwa, su ne ya kuɓutar, waɗanda ya kuɓutar ɗin kuwa, sune ya ɗaukaka.” Wannan ayar na gaya mana cewa daga lokacin da Allah ya zaɓe mu, ya zama kamar an ɗaukaka mu a gaban sa cikin sama. Babu wani abin da zai hana mai bada gaskiya daga wata rana a ɗaukaka shi don Allah ya riga yayi nufin haka cikin sama. Muddar an kubutar da mutum, an tabbatas da ceton sa – ya zama an tsare shi kamar ya riga samun ɗaukaka cikin sama.

(b) Bulus yayi tambayoyi biyu manya cikin Romawa 8:33-34 “Wa zai ɗora wa zaɓaɓɓun Allah laifi? Allah ne ke kuɓutar da su! Wa zai hukunta su? Almasihu Yesu wanda ya mutu, ko kuwa a ce wanda ya tashi daga matattu, shine wanda ke dama ga Allah, shine kuwa wanda ke roƙo saboda mu!” Wane ne zai ɗora laifi akan zaɓaɓɓun Allah? Babu waninsa, domin Kiristi shine lauya namu. Wa zai iya yin tir da mu? Babu waninsa, domin Kiristi shine, shine wanda ya mutu domin mu, Shine wanda ke iya yin tir. Muna da duk da lauya da alƙali a matsayin mai ceton mu.

(c) Masu bada gaskiya an sake haifuwar su (sake halitta) sa’anda suka gaskata (Yahaya 3:3; Titus 3:5). Ga Kirista ya rasa ceton sa, shi sai ya sake zama ba a maya haifuwarsa ba. Littafi Mai Tsarki bata bada wani shaida cewa sabuwar haifuwa za a iya kawar da ita ba. (d) Ruhu Mai Tsarki yana zama da dukkan masu bada gaskiya (Yahaya 14:17; Romawa 8:9) kuma yana wa masu bada gaskiya baftisma cikin Jikin Kiristi (1Korantiyawa 12:13). Ga mai bada gaskiya ya zama ba a cece shi ba, sai ya zama Ruhu Mai Tsarki “ba ya zama” a cikinsa kuma a ɓamɓare shi daga Jikin Kiristi.

(e) Yahaya 3:15 tana cewa kowane da ya gaskata da Yesu Kiristi zai “sami rai madawwami.” Idan ka gaskata da Yesu a yau kuma ka sami rai madawwami, amma ka rasa shi gobe, sa’anan ba ta taɓa zama “madawwami” ba fau fau. Har yanzu idan ka rasa ceton ka, alƙawaran rai madawwami cikin Littafi Mai Tsarki sun zama da kuskure. (f) Ga gardama mafi kawo ƙarshen magana, Ina tunani Littafi Mai Tsarki ta faɗe ta da mafi kyau da kanta, “Domin na tabbata, ko mutuwa ce, ko rai, ko mala’iku, ko manyan mala’iku, ko al’amuran yanzu, ko al’amura masu zuwa, ko masu iko, ko tsawo, ko zurfi, kai ko kowace irin halitta ma, ba zasu iya raba mu da ƙaunar da Allah ke yi mana ta wurin Almasihu Yesu Ubangijinmu ba” (Romawa 8:38-39). Ka tuna Shi Allah wanda ya cece ka shine wanda zai riƙe ka. An cece mu gaba ɗaya, an cece mu koyaushe. Ceton mu tabbatacce tana tsare har abada.

English



Koma zuwa shafin gida na Hausa

An ceta gaba ɗaya, an ceta koyaushe?
© Copyright Got Questions Ministries