settings icon
share icon
Tambaya

Mene ne baiwar magana cikin harsuna?

Amsa


Farkon magana cikin harsuna ta faru ne a Ranar Fentikos cikin Ayyukan Manzanni 2:1-4. Manzanni sun fita waje kuma suka yaɗa bishara tare da su jama’a, suna magana da su cikin yarurrukansu, “duk muna ji suna maganar manyan al’amuran Allah da bakunan garuruwanmu!” (Ayyukan Manzanni 2:11). Kalmar Hellananci da aka juya “harsuna” a zahiri na nuna “yaruruka.” Don haka, baiwar harsuna shine magana cikin yaren da mutum bai sani ba garin ya hidimta ga wani wanda ke magana da yaren. A cikin 1Korantiyawa Surori 12-14, inda Bulus yayi zance baye-bayen al’ajabi, ya bayyana cewa, “To, ƴan’uwa, in nazo muku ina magana da waɗansu harsuna, amfanin me zai yi muku in ban zo muku da wani bayyani, ko ilimi, ko annabci, ko koyar da Maganar Allah ba?” (1Korantiyawa 14:6). Bisa ga manzo Bulus, kuma cikin yarda da harsunan da aka kwatanta cikin Ayyukan Mmanzanni, magana cikin harsuna na da amfani ga mai sauraron saƙon Allah cikin yaren kansa/ta, amma ta zama da rashin amfani ga kowane dabam- sai dai ko an fassarta/juya.

Mutum mai baiwar fassarta harsuna (1Koarantiyawa 12:30) zai iya gane abin da mai magana da harsuna ke faɗi ko da yake shi/ita bai san yaren da ake magana ba. Mai fassarta harsuna zai sadar da saƙo na mai magana da harsuna ga kowane kuma, don duk su iya ganewa. “Saboda haka duk mai magana da wani harshe, sai yayi addu’a a yi masa baiwar fassara” (1Korantiyawa 14:13). Taƙaitawar Bulus game da harsuna da ba fassarta ba na da ƙarfi, “Duk da haka dai a taron ikilisiya na gwammace in faɗi kalmomi biyar game da tunanina, domin in karantar da waɗansu, da in faɗi kalmomi dubu goma da wani harshe” (1Korantiyawa 14:19).

Ko baiwar harsuna sun zama na yau? 1Korantiyawa 13:8 ta ambaci tsayawar baiwar harsuna, ko da yake ta haɗa tsayawar da kuma isowar “cikakken” cikin 1Korantiyawa 13:10. Waɗansu na nuna da bambanci cikin tsayawar harshen annabci da kuma sani kuma da “tsayawar” harsuna ta shaidar tsayawar harsuna kafin isowar ‘cikakken.” Yayin da yana yiwuwa, wannan baya a bayyane sarai daga nassin ba. Waɗansu ma na nuna nassoshi irin su Ishaya 28:11 da Yowel 2:28-29 kamar shaida cewa magana cikin harsuna ta zama alamar zuwan shari’ar Allah. 1Korantiyawa 14:22 ta kwatanta harsuna kamar wata “alama ga marasa bada gaskiya.” Bisa ga wannan gardama, baiwar harsuna sun zama gargaɗi ne ga Yahudawa cewa Allah zai shari’anta Isra’ila don ƙin Yesu Kiristi a matsayin Almasihu. Don haka, sa’anda Allah da gaske ya shari’anta Isra’ila (da hallakar Urushalima ta Romawa cikin A.D. 700, baiwar harsuna bai zama kuma da manufar da aka nufa ba. Yayin da wannan ra’ayi zai zama da yiwuwa, manufa ta farko na harsuna mai cikawa bai bukaci lalle da tsayawar ta ba. Littafi Mai Tsarki bai faɗi a taƙaitawa cewa baiwar magana cikin harsuna ta tsaya ba.

A lokaci guda, idan da baiwar magana cikin harsuna ana yin ta cikin ikilisiya a yau, za a yi ta ne cikin yarda da Littafi Mai Tsarki. Da ya zama ainihin da yare mai fasaha (1Korantiyawa 14:10). Da ya zama don manufar sadar da Maganar Allah da mutumin da ke na wata yare (Ayyukan Manzanni 2:6-12). Da ya zama cikin yarda da umarnin da Allah ya bayar ta wurin Manzo Bulus, “In kuwa waɗansu zasu yi magana da wani harshe, kada su fi mutum biyu, matuƙa uku, suna kuwa bi da bi, wani kuma yayi fassara. In kuwa ba mai fassara, sai kowannensu yayi shiru cikin taron ikilisiya, yayi wa Allah magana a zuci” (1Korantiyawa 12:27-28). Da ya zama kuma cikin miƙa wuya ga 1korantiyawa 14:33, “ Domin Allah ba Allahn ruɗu ba ne, na salama ne. Haka yake kuwa a duk ikilisiyoyin tsarkaka.”

Allah ta tabbaci mafiya zai iya ba mutum baiwar magana cikin harsuna don shi/ita ta iya sadarwa tare da wani mutum wanda ke magana da wata harshe. Ruhu Mai Tsarki ne mai iko dukka cikin rarrabawar baye-bayen ruhaniya (1Korantiyawa 12:11). Kayi zato kawai da yaya masu yaɗa bishara zasu iya nasara idan da basu sami tafiyar makarantar koyon yare, da kuma a ce kawai haka sun iya magana da mutane cikin yarensu. Duk da haka, da alama dai Allah baya yin haka. Harsuna basa faruwa a yau da kamannin da anyi ta cikin Sabon Alƙawari duk da zance cewa da zata yi amfani mai yawa. Yawanci masu bada gaskiyar da suna da’awa ta yin aiki da baiwar magana cikin harsuna basa yin haka cikin yarda da Littattafan da aka ambata a sama ba. Waɗannan dalilai masu kaiwa ga taƙaitawa cewa baiwar harsuna ta tsaya, ko kuma aƙalla ba safai ba cikin shirin Allah ga ikiklisiya a yau.

Waɗanda sun gaskata da baiwar harsuna kamar wata “yaren addu’a” don inganta kai, na samun ra’ayinsu daga 1Korantiyawa 14:4 da /ko 14:28, “Duk wanda ke magana da wani harshe, kansa yake ingantawa. Mai yin annabci kuma, ikilisiya yake ingantawa.” Koina a sura 14, Bulus na ƙarfafa muhimmancin samun fassarar harsuna (juyawa) dubi 14:5-12. Abin da Bulus ke faɗi cikin aya 4 shine, “Idan kana magana da harsuna banda mai fassara, kana yin rashin kome, amma inganta kanka, kana nuna kanka kafi saura ruhaniya. Idan kayi magana da harsuna kuma an fassarta ta, kana inganta kowa da kowa.” Babu inda Sabon Alƙawari ta ba takamaiman umarni kan “addu’a cikin harsuna.” Babu inda Sabon Alƙawari ta bada manufar “addu’ar cikin harsuna”, ko na bayyana takamaimai wani mutum mai “addu’a cikin harsuna.” Gaba kuma, idan “addu’a cikin harsuna” ya zama inganta kai, ba zai zama da rashin kyau ga waɗanda ba su sami baiwar harsuna da kuma waɗanda don haka basu iya inganta kansu ba? 1korantiyawa 12:29-30 tana nuna sarai cewa ba kowane mutum ba ne ke da baiwar magana cikin harsuna ba.

English



Koma zuwa shafin gida na Hausa

Mene ne baiwar magana cikin harsuna? Ko baiwar harsuna ta zama na yau? Mene ne game da yin addu’a cikin harsuna?
© Copyright Got Questions Ministries