settings icon
share icon
Tambaya

Mece ce Turban Ceto na Romawa?

Amsa


Turban Ceto na Romawa hanya ce na gutsura Bisharar Ceto ana amfani da ayoyin Littafi Mai Tsarki na Romawa. Tana da sauƙi duk da haka ƙaƙƙarfar hanyar bayyana dalilin da yasa muna bukatar ceto, da mene ne ceto ke haifarwa.

Ayar farko kan Turban Ceto na Romawa shine Romawa 3:23,”Gama ƴan adam duka sun yi zunubi, sun kasa kuma ga ɗaukakar Allah.” Dukan mu mun yi zunubi. Dukan mu mun yi abubuwan da zasu sa ɓacin zuciya ga Allah. Babu wani ɗaya wanda ya zama marar laifi. Romawa 3:10-18 tana bamu hoto filla-filla na abin da zunubi yake a cikin rayuwarmu. Aya na biyu akan Turban Ceto na Romawa, Romawa 6:23, tana koyar mana game da abubuwan da zunubi yakan haifar –” Gama sakamakon zunubi mutuwa ne, amma baiwar Allah ita ce rai madawwami cikin Almasihu Yesu Ubangiji mu.” Hukuncin da ya zama ladan aiki zunubanmu shine mutuwa. Ba kawai mutuwar jiki ba, amma mutuwa ta har abada!

Aya ta uku akan Turban Ceto na Romawa ta ɗauki inda Romawa 6:23 ta bari,” amma baiwar Allah ita ce rai madawwami cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu.” Romawa 5:8 tayi shela,” Amma kuwa Allah na tabbatar mana da ƙaunar da yake mana, wato tun muna masu zunubi, Almasihu ya mutu domin mu.” Yesu Kiristi ya mutu dominmu! Mutuwar Yesu ta biya don farashin zunubanmu. Tashin Yesu daga matattu ta gwada cewa Allah ya amshi mutuwar Yesu a matsayin biyarwa don zunubanmu.

Wurin tsayawa na hudu kan Turban Ceto na Romawa shine Romawa 10:9,”Wato in kai da bakin ka ka bayyana yarda, cewa Yesu Ubangiji ne, ka kuma gaskata a zuciyarka Allah ya tashe shi daga matattu, zaka sami ceto.” Saboda mutuwar Yesu a madadinmu, duk abin da ya kamata muyi shine bangaskiya cikinsa, muna amincewa da mutuwarsa a matsayin biya don zunubanmu – kuma zamu sami ceto!

Romawa 10:13 kuma tana cewa,” Duk wanda kuwa yayi addu’a da sunan Ubangiji zai sami ceto.” Yesu ya mutu da ya biya hukunci don zunubanmu kuma ya tserad da mu daga mutuwar har abada. Ceto, gafarar zunubanmu, suna samuwa ga kowane wanda zai amince cikin Yesu Kiristi a matsayin Ubangijinsu da mai ceto.

Wajen ƙarshe na Turban Ceto na Romawa shine sakamakon ceto. Romawa 5:1 tana da wannan saƙo mai ban mamaki,”To, da yake mu kuɓutattu ne ta wurin bangaskiya, muna da salama ke nan a gun Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Almasihu.” Ta wurin Yesu Kiristi zamu iya sami dangatakar salama da Allah. Romawa 8:1 tana koyar mana,”Saboda haka yanzu ba sauran kayarwa ga waɗanda ke na Almasihu Yesu.” Saboda mutuwar Yesu a madadinmu, ba za a taɓa kayar da mu don zunubanmu ba. A ƙarshe muna da wannan alƙawari mai daraja na Allah daga Romawa 8:38-39,” Domin na tabbata, ko mutuwa ce, ko rai, ko mala’ika, ko manyan mala’iku, ko al’amuran yanzu, ko al’amura masu zuwa, ko masu iko, ko tsawo, ko zurfi, kai ko kowace irin halitta ma, ba zasu iya raba mu da ƙaunar da Allah ke yi mana ta wurin Almasihu Yesu Ubangijinmu ba.”

Ko zaka so ka bi Turban Ceto na Romawa zuwa ceto? Idan haka ne, ga wata addu’a anan mai sauƙi da zaka yi ga Allah. Faɗin wannan addu’a wata hanya ce na furta wa Allah cewa kai kana dogara kan Yesu Kiristi don ceton ka. Kalmomin kansu ba zasu cece ka ba. Bangaskiya kadai cikin Yesu Kiristi ne zai iya tanada ceto!”Allah, na sani cewa nayi zunubi gare ka kuma na cancanci hukunci. Amma Yesu Kiristi ya ɗauki hukuncin da ya cancance ni, don ta wurin bangaskiya a cikinsa in sami gafartawa. Na juyo daga zunubaina kuma na sa amincewa tawa a cikinka don ceto. Na gode maka don alherinka mai ban mamaki da kuma gafara – kyautar rai madawwami! Amin!”

Ko ka yanke shawara domin Kiristi saboda abin da ka karanta anan? Idan haka ne, don Allah danna kan “Na riga na karɓi Kiristi yau” botin na ƙasa.

English



Koma zuwa shafin gida na Hausa

Mece ce Turban Ceto na Romawa?
© Copyright Got Questions Ministries