settings icon
share icon
Tambaya

Ko Littafi Mai Tsarki da gaske maganar Allah ne?

Amsa


Amsar mu ga wannan tambaya ba zai ƙudurta kaɗai yadda muke duban Littafi Mai Tsarki da muhimmancin ta ga rayukan mu ba, amma kuma a ƙarshe zata zama da madawwamiyar tasiri a kan mu. Idan Littafi Mai Tsarki da gaske maganar Allah ne, sa’anan zamu ƙaunace ta, nazarce ta, yi biyayya da ita, kuma a ƙarshe zamu amince da ita. Idan Littafi Mai Tsarki maganar Allah ne sa’anan da a sallame ta ya zama a sallame Allah da kansa ke nan.

Da gaske cewa Allah ya bamu Littafi Mai Tsarki ya zama shaida da ishara na ƙaunarsa gare mu. Kalmar “wahayi” a sauƙaƙe tana nufin cewa Allay ya sadar ga ƴan adam abin da kamanninsa yake da yadda zamu iya sami madaidaiciyar dangantaka da shi. Waɗannan sune abubuwan da ba zamu iya sani ba in ba don Allah cikin Allahntakar sa ya bayyana mana su a cikin Littafi Mai Tsarki. Ko da yake bayyanin Allah na kansa cikin Littafi Mai Tsarki an ci gaba da bayar da ita har kusan shekaru 1500, kullum tana ƙunshe ne da komene ne da mutum ke bukatar ya san game da Allah garin ya sami dangantaka na gaskiya tare da shi. Idan Littafi Mai Tsarki da gaske maganar Allah ne, sa’anan ita ce ke da iko na ƙarshe ga dukkan al’amuran bangaskiya aiwatawar addini da halayen kirki.

Tambayar da dole ne muyi wa kanmu shine yaya zan iya san cewa Littafi Mai Tsarki maganar Allah ne kuma kawai ba kyakkyawar littfi ba? Mene ne yake na dabam game da Littafi Mai Tsarki da ya maida ita keɓaɓɓiya daga dukkan sauran littattafan addiini da an taɓa rubutawa? Akwai wata shaida cewa Littafi Mai Tsarki da gaske maganar Allah ne? Waɗannan sune irin tambayoyin da dole a dube su idan zamu jarraba da tsananin da’awar Littafi Mai Tsarki cewa Littafi Mai Tsarki ce ainihin maganar Allah, hurarre daga wurin Allah, kuma gaba ɗaya ta isa don dukkan al’amuran bangaskiya da aikatawa.

Zai zama babu shakka game da gaskiyar cewa Littafi Mai Tsarki tana da’awa ita ce ainihin mganar Allah. Ana ganin wannan a zahiri cikin ayoyi kamar 2Timoti 3:15-17, wanda tace, “--- da kuma yadda tun kana ɗan ƙaramim ka san littattafai masu tsarki, waɗanda suke koya maka hanyar samun ceto ta dalilin bangaskiya ga Alamsihu Yesu. Kowane Nassi hurarre na Allah ne, mai amfani ne kuma wajen koyarwa, da tsawatarwa, da gyaran hali, da kuma tarbiyyar aikin adalci, domin bawan Allah ya zama cikakke, shiryayye sosai ga kowane kyakkyawan aiki.”

Garin a amsa waɗannan tambayoyi dole ne mu dube duk da shaidun ciki da na waje cewa Littafi Mai Tsarki da gaske ne maganar Allah. Shaidun ciki sune waɗancan abubuwa na cikin Littafi Mai Tsarki kanta masu shaidar tushen ta daga Allah ne. Ɗaya daga cikin na farkon shaidun ciki cewa Littafi Mai Tsarki da gaske maganar Allah ne na ganuwa cikin zamantowar ta guda ɗaya tak. Ko da yake da gaske tana da littattafai ɗai ɗai sittin da shida, da aka rubuta a manyan ɓangarorin duniya kashi uku, a cikin harsuna dabam dabam guda uku, na kusan lokaci shekaru 1500, daga fiye da marubuta 40 (waɗanda sun taho ne daga sana’o’in rayuwa da dama), Littafi Mai Tsarki ta rage littafi guda haɗaɗɗiya daga farko zuwa ƙarshe da babu baki biyu. Wannan haɗin ta zama dabam ne daga dukkan sauran littattafai kuma shaida ne kalmominta daga wurin Allah ta yadda Allah ya motsa mutane a irin hanyar da suka rubuta ainihin kalmomoinsa.

Wani dabam na shaidun ciki mai nuna Littafi Mai Tsarki da gaske maganar Allah ne na ganuwa cikin annabtai fill-filla dake ƙunshe tsakanin shafunan ta. Littafi Mai Tsarki na ƙunshe da ɗarurrukan annabatai filla-filla dangane da lokacin gaba na al’ummai ɗai ɗai haɗe da Isra’ila, zuwa lokacin gaba na waɗansu birane, zuwa lokacin gaba na ɗan adam, da kuma zuwa wanda zai zama Mahadi, mai ceto ba na Isra’ila kaɗai ba, amma dukkan waɗanda zasu bada gaskiya cikin Sa. Ba kamar annabtai waɗanda ana samunsu a cikin sauran littattafan addini ko waɗancan da Nostradamus yayi su, annabatan Littafi Mai Tsarki suna filla-filla matuƙa kuma basu taɓa kasa da zamar gaskiya ba. Akwai fiye da annabtai ɗari uku game da Yesu Kiristi a cikin Tsohon Alkawari kaɗai. Ba kaɗai an faɗa tun da wuri inda za a haife shi kuma daga wani dangi zai taho ba, amma kuma yadda zai mutu kuma ya sake tashi a rana ta uku. A sauƙaƙƙe ba wata makama a bayyana cikakkun annabtai na Littafi Mai Tsarki ban da cewa su daga wurin Allah ne. Babu wata littafin addini da ke da iyakaci ko da irin annabtan da aka faɗe su a gaba yadda Littafi Mai Tsarki ke da su.

Na uku na shaidun ciki cewa Littafi Mai Tsarki daga wurin Allah ne na ganuwa cikin iznin kanta na dabam da kuma iko. Sa’anda wannan shaida ya zama ra’ayin wani ne fiye da shaidun ciki na farko, bata kasa ainun ƙwarai da ƙaƙƙarfar shaidar Littafi Mai Tsarki daga wurin Allah ne ba. Littafi Mai Tsarki tana da iko na dabam wanda bai zama kamar wata littafin da aka taɓa rubutawa. Wannan izni da iko ana ganinsu mafiya kyau a cikin hanyar da ɗumbun rayuka sun sami sakewa ta karatun Littafi Mai Tsarki. An warkad da ƴan kwaya ta wurin ta, an ƴantar da ƴan kushili ta wurin ta, yasassu da gajiyayyu sun sami sakewa ta wurin ta, tattauran miyagu sun sami sabuntawa ta wurin ta, masu zunubi sun sami tsawatarwa ta wurin ta, kiyayya ta juyo zuwa ƙauna ta wurin karatun ta. Littafi Mai Tsarki ta mallaki wata ƙarfi da ikon sauyawa mai yiwuwa kaɗai domin ita ce da gaske maganar Allah.

Ban da shaidun ciki cewa Littafi Mai Tsarki ce da gaske maganar Allah akwai kuma shaidun waje masu nuna Littafi Mai Tsarki da gaske maganar Allah ne. Ɗaya daga waɗancan shaidun shine tarihin Littafi Mai Tsarki. Domin Littafi Mai Tsarki ta zama abubuwan da sun faru a tarihi filla-filla gaskiyarta da daidaitaka ya zama abin haƙiƙanta kamar kowace sauran rubutun tarihi. Ta wurin duk da shaidun kayan tarihi da aka haƙo da waɗansu rubutattun shaidu, labarin tarihi na Littafi Mai Tsarki an jaraba su lokaci akan lokaci kuma sun zama daidai da kuma gaskiya. Gaskiya, dukkan shaidun kayan tarihi da aka haƙo da rubutun farko masu tallafar Littafi Mai Tsarki sun mai da ita mafi dukka na rubutattun takarda daga duniyar zamanin dă. Da cewa Littafi Mai Tsarki tana rubuce da daidai da gaskiyar tarihin abubauwan da za a tabbatar ya zama babban alama na gaskiyar ta idan ana zancen fannin addini da jigajigan koyarwa da kuma da taimakon gindaya da’awar ta cewa ita ce maganr Allah na ƙwarai.

Wani shaidar waje na Littafi Mai Tsarki da gaske ne maganar Allah shine mutuncin mutane marubuta . Yadda aka faɗa da farko, Allah ya mori mutane daga sana’o’in rayuwa masu yawa su rubuta maganar sa gare mu.A cikin nazarin rayuwar waɗannan mutane, babu wata kyakkyawar dalili a gaskata cewa ba su basu zama salihai da salihan mutane ba. Da jaraba rayukan su da kuma cewa suna da yarda su mutu (sau tari mutuwar azaba) ga abin da sun gaskata a ciki, ya zama maza-maza sarai cewa waɗannan talakawa duk da haka salihan mutane da gaske ne sun gaskata cewa Allah yayi magana da su. Mutanen da sun rubuta Sabon Alkawari da yawan ɗarurrukan sauran masu bada gaskiya (1Korantiyawa 15;6) sun san da gaskiya saƙon su domin sun ga da kuma an kashe lokaci da Yesu Kiristi bayan da ya tashi daga matattu. Sauyawa na ganin Kiristi da ya tashi daga matattu na da gaggarumar shafa a kan waɗannan mutane. Sun tafi daga ɓuya cikin tsoro, zuwa ga bada yarda a mutu don saƙon da Allah ya bayyana masu. Rayukan su da mace-macen su sun shaida gaskiya cewa Littafi Mai Tsarki ne da gaske maganar Allah.

Shaidar waje na ƙarshe cewa Littafi Mai Tsarki ne da gaske maganar Allah shine mai sa rashin rusawa na Littafi Mai Tsarki. Domin muhimmancin ta da kuma da’awar ta da zama maganr Allah ne ƙwarai, Littafi Mai Tsarki ta wahala fiye da muguwar faɗawa kuma da ƙoƙarin a lalata ta fiye da kowace littafi cikin tarihi. Daga farkon sarakunan Romawa kamar Diocletian, zuwa mulki kama karya na Kwaminisanci da kuma kan kafirai na zamani ta yau, da masu shakkar kasancewar Allah, Littafi Mai Tsarki tayi tsayin daka kuma tana a raye bayan dukkan masu farmakin ta sun mutu da kuma ita ce mafi yaɗuwa na littafin da aka buga cikin duniya yau.

A dukkan lokaci, masu shakka sun ɗauki Littafi Mai Tsarki kamar hikayar mafari amma kayan tarihin da aka haƙo ta ƙarfafa tarihin ta. Abokan gaba sun far ma koyarwar ta kamar na duhun kai da kuma na wanda ba na yau ba, amma tunanin ta na halin kirki da na halal, da koyarwa suna da tabbataccen tasiri akan zaman jama’a da al’adu zuwa cikin duniya koina. Kimiyya ta ci gaba da far mata, da ilimin hankalin mutane, da kungiyoyin jam’iyyun siyasa kuma har ila dai ta saura kawai da gaskiya kuma tana da shafa a yau kamar yadda take da farko da aka rubuta ta. Ta zama littafi ce ta sake rayuka da al’adu marar lissaftawa har na shekaru 2000 yau. Ko da yaya ne abokan gaban ta sun kai mata farmaki, rusawa, nuna rashin gaskiyar ta, Littafi Mai Tsarki ta saura daidai da ƙarfi, daidai a gaskiya, da kuma daidai da shafa bayan faɗawa da kamar yadda yake dă ma. Daidaitakar da an kiyaye duk da kowace gwaji a ‘ɓata, faɗa wa, ko a rusar da ita,ta zama shaida sarai na gaskiyar cewa Littafi Mai Tsarki ne da gaske maganar Allah. Kada ya zama mana da mamaki cewa ko da yaya ne za a far ma Littafi Mai Tsarki, kullum zata fito ne babu sakewa da mara taɓo. Bayan dukka, Yesu ya ce, “Sararin sama da ƙasa za su shude, amma magana ta ba zata shuɗe ba” (Markus 13:31). Bayan an dubi shaidar wani zai iya ce ban da shakka cewa “I, Littafi mai Tsarki ne da gaske Maganar Allah.”

English



Koma zuwa shafin gida na Hausa

Ko Littafi Mai Tsarki da gaske maganar Allah ne?
© Copyright Got Questions Ministries